AUREN GADO Page 1 to 10

Tana dauka tasaki kuka mai ciwo. “Aunty wallahi nagaji ni zankoma gida nagaji bazan iya ba, zan mutu a rasa dalilin mutuwa ta Aunty please kizo ki tafi dani.
Saida tayi ma ishinta ta yi shiru tana jinta, “Naziya’, ta kirata, bata iya amsawa ba sai sheshsheka tace ” kin taba ganin ko kwana muntaba yi agida tunda mukayi Aure, bare kuma yaji? Dagani har Aisha ba wadda ta taba kai Karar mijin ta cikin gida ko gaban malam, muna hakuri tareda bawa junan mu shawara in Matsala ta taso, infada miki gaskiya? Ba macen da batada kalar tata Matsalar Aure, please Naziya ki dauki halin Inna, kina gani kullum malam yabon ta yakeyi domin yasan mace ce tagari, nasan duk Abinda yake faruwa a gidan Auren ki, ba kanki farau ba, ki jajirce kici gaba da hakuri, yanzu fa aka fara Naziya, ni nafada miki tun farko kibi mijin ki tunda shi an hanashi binki, biyayyar Aure kikeyi bauta kikeyi, ki rungumi taki kaddarar Allah zai kawo miki mafita.
“Aunty banki ta taki ba, Amma inayin iya bakin kokari na, kinaji fa wai Aure zai karayi. “Toh sai me? Baki yarda da kanki bane? Ke ba mace bace? Look ki nuna musu Auren ba komai bane idan bakida hakki zakiga saka mako, nasan kinada hakuri ki Kara akai kar taurin kanki ya motsa Wanda bakya juyuwa.
“Hmmm nagode Aunty, insha Allahu zanyi hakuri. “That’s my sister, kuma insha Allahu zamuzo karshen satin nan nida Aisha. Dadi taji sosai domin Y’ar uwarta ta bata shawara mai kyau, tareda sanyaya mata zuciya.
Sharewa tayi da komai cikin ikon Allah, ta Kara rungumar hakuri tareda daura damarar share komai, tana ganin yanda aketa shirin biki kamar da gayya itama Amarya anyo mata kayan fitar kunya, Aljihu tasa Ahmed ya bude yana bata kudi ta zabgi kaya, ciwo yakeyi a tsaye batareda ya fadawa kowa ba shikadai yasan damuwar shi, Naziya tuni ya nesanta kanshi da ita domin ya rage mata damuwa, itama ta Ajiyeshi a kwandon shara, badon bata damuwa ba, biki nata matsowa shikuma yana shirin tafiyar shi.
Khaleel yayi yayi yabarshi ya tafi yace no shi zaije Ana gama biki Washe gari zai wuce. Mommy ma basu fada mata shirin su ba.
Khaleel ma tuni ya kiyayi Naziya domin ya lura tsanar tashi ta Kara yawa fiyeda da, yana ganin yanda take hada girar sama data kasa in sun hadu, shi yasan halinta Wanda Ahmed bai san shiba ma yanzu, daga gani macece kaifi daya inbata yinka shikenan, ga taurin kai.
Tana lura da Al amarin shi yanzu sama sama in sun hadu ta lura yanzu baya fitowa da kana nan kaya ko falo, tun ranar da tayi mai gori.
Biki fa yazo Amare nata rawar kafa, angwaye kuwa ko motsi basayi, ko Khaleel Yafada mata karta sake ta sakashi cikin shirmen party d’in su. Momy ta tattara su duka ta watsar tana hidimar ta, itadai tasan burin ta zai cika ya’yan ta zasu Auri irin zabin ranta, don haka ta zage ta bude bakin Jakarta.
Lafiyayyan mothers day suka shirya a tafkeken hall da yaji kudi, ta gayyaci manyan mata masu kudi da Aji, da kanta tayowa Naziya dunkuna Kala goma wai na dannar kirji tasa na fitar biki.
Lokacin da malam yaji labari, waya yasa aka hadashi da ita ya mata nasiha tareda Sanya mata Albarka, Wanda ta Kara mata kwarin guiwa, bawai Abun baya taba ta bane a’a “ya za’ayi bazai zafeta ba, kawai dai ta rungumi hakuri da kuma waraka, Wato Alqur’ani mai girma. Wanda shine maganin duk wata damuwa da yayewar bakin ciki.
Ana Saura kwana uku biki tasa Shukrah tazo domin ta yi mata lalle, Wanda saida tayi da gaske Malam yabari, tazo suka baje a dakin suna hira tana yimata lalle, “Aunty Kinga magana ta ko, nafada miki Yaya Ahmed mai kudi ne, gaskiya kin more irin wannan katon gidan. “Hmmm. Kawai tace, “Amma Aunty kin d’an rame kadan sai haske kawai da kika Kara, Ina Yaya Ahmed din? “Yana nan, kuma ki rage surutu kiyi sauri kafin lokacin da Malam yabamu yayi, Amma Aunty da gaske Aure zai Kara wai? “Eh. “Auren ku wata daya da y’an satika shine zai Kara? “Ya isa maganar shukrah, tafada domin batason zancen,
Maid ta kawo musu kayan ciye ciye a dakin, domin mommy tafita, har suka gama ta rakota tareda bata kyautar kayan shafa, domin batada kudi a hannun ta, suna fitowa su Ahmed sukayi Sallama, tayi Saurin dauke kanta. Shukrah baki har kunne domin tayi mugun sabo dashi tace “lah Yaya Ashe zangan ka kafin intafi? “A a shukrah kece a gidan namu? “Eh Yaya Ahmed har nagama wa Amaryar taka lalle zantafi, Saurin kallon hannun nata sukayi dukan su, khaleel yayi Saurin dauke kanshi, “kai Amma mungode shukrah da wannan zuwan Yafada yana matsawa kusa da Naziya ya riko hannun ta, shukrah tayi Saurin rufe idanun ta saboda kunya ta ruga hanyar waje tana ni na gudu gida Aunty bye, Dariya Ahmed yayi yace “please Brother ka kaita gida. Amsawa yayi kawai ya fita, motar shi ya fada dalleliya yabi bayan ta, tareda yimata horn, ta tsaya don har tafita wajen gate d’in, “muje ko’ Yafada ba wani walwala, “nagode zansamu adai daita ma. “Come on ki shigo Yaya Ahmed yace inkai ki.
Budewa tayi kawai saboda batason musu, gashi ya cika mata ido, maganar gaskiya zaiyi wulakanci domin fuskar tashi Sam ba fara’a ko walwala, don haka batayi yunkurin cemai komai ba har ya Kama hanya yana driving slowly, sai kamshin shi da kwarjini da ya cika motar, “me yasa bakya zuwa kina ganin Y’ar uwar ki? Yafada batareda yako kalli gefen taba, itama Abun yazo mata a bazata duk ta diririce, saida ya mai maita, tace “ba a barin mu fita zuwa yawo. Tabe bakin shi yayi kawai bai kuma cewa komai ba har ya kaita kofar gidan tace ta gode, ya ciro kudi a gaban motar shi ya mika mata masu yawa, Saurin kallon hannun shi tayi ta koma gefe tana girgiza kai, domin kudin zai kai dubu Ashirin, “nagode bama karbar kudi a waje. Mayar wa yayi kawai yaja motar shi tareda bade ta da kura yayi gaba, “tab Aunty Naziya wannan ai yafi Yaya Ahmed girma da cika ido ga girman kai kamar d’an gidan Sarki,. Tafada tana bin bayan motar shi da kallo har ya bace.
Su khaleel na fita ta fisgi hannun ta tayi dakin ta da gudu, yanzu ne wani irin bakin ciki yake rufe mata zuciya, bin bayan ta yayi batareda ya shirya ba, zubewa tayi agadon ta kife tareda sakin kuka mai taba zuciya, dafata yayi tayi Saurin zabura fuskar ta shabe shabe da hawaye “don’t touch me. Tafada kai tsaye tana mai kallon kai ne sanadi, “Ina dana sani, nayi hakuri tunda ga ranar farko da Nazo gidanku, bawai nace mommy bata isa tayi min fada bane, a’a kaine Matsala ta, kai kakawo ni gidan nan, Amma sai dai in hadu dakai a hanya, duk na daure nayi hakuri, yanzu kishiya…… Takarasa tana kife kanta a cinyar ta, shiru yayi tareda dafe kanshi yazame gefen gadon ya Rungumo ta baki daya zuwa jikin shi tana kokarin Sauka. “Nasani Naziya, ki yafemin don Allah, nasan sai Allah ya tanbayeni hakkin ki, domin banyi miki Adalci ba, yazanyi Naziya Ina gudun bakin uwa, yanzu ma na kaucewa tsarin ta da dokar ta, don Allah kiyi shiru ki yafemin kar Kisa ni a cikin damuwa, kinsan cewa ganin kwanciyar hankalin ki ke kwantar min da nawa, Amma yanzu idan kina wannan kukan zuciya ta zata iya bugawa kowa yarasa ni. Saurin yin shiru tayi tareda share hawaye da bayan hannun ta “meye laifi na? Saboda Ina Y’ar talaka? Meye illar talauci tunda bamu nema a wurin wani ba, Alhamdulillah da gidan da na fito bama raina Abin da Allah ya bamu. “I know” Naziya please forgive me, kuma Kisa a ranki wata rana komai zai wuce, zakiyi farin ciki insha Allahu, ni nasan banda wata kalma da zanyi Amfani da ita domin baki hakuri Amma nasani na zalunce ki, ki yafemin. Naziya na gaza akanki ban sauke nauyin ki dake wuyana ba. Yafada yana dora fuskar shi akan wuyan ta, wasu irin hawayen shi taji suna bin wuyan nata, da sauri ta dora hannun ta saman kanshi tareda cewa “don Allah kayi shiru nima kaga na hakura nayi shiru, kaga bakyau babba na kuka. Tashi yayi tareda ita ya zauna gefen gadon, tareda fuskantar ta yana share idanun nashi yana mai murmushi kadan, “wayace miki ni babba ne a wurin ki? “Kai babba ne ai ka girme ni sosai. “No ni jaririne a wurinki domin wata rana shayar dani zakiyi,,, wani irin saurin rufe fuskar ta tayi saboda kunya, “Hhhhhh ko za a bani ne yanzu, Yafada yana riko west dinta cikin tsokana, ta zame cike da kunya, dadin moment din sukeji sosai, ta kalle shi cikeda tausayin shi tace, “bakada lafiya ne? Murmurshi yayi, “yes. “Meke damun ka? “Soyayyar matata, you know banason in rasaki Naziya idan nayi tunanin zaki iya gajiya ki gujeni hankalina natashi, bazan iya ganin ki kina Rayuwa ba agidana ba, banason inganki tareda wani Naziya saboda Ina sonki Ina kishin ki, ganin ki a inuwar Aurena yana sani inji farin ciki, yana rage min damuwa, please stay with me, my wife komai zaizo karshe wata rana zamu kasance a cikin inuwa daya zanganki da jini na atare dake a wannan shafaffen marar. Yafada yana shafo cikin ta, d’an zamewa tayi kadan domin yanasa ta jin wani iri a jikin ta. A wannan lokacin ya bata farin ciki mai yawa Wanda zata sakashi a tarihin Rayuwar ta domin yamata Alkawura da yawa akan yanda zaman su zai kasance, anan yake fada mata bayan bikin Khaleel da kwana biyu zaiyi tafiya, Kinga da momy zata Amince tare zamu tafi dake, muje musha soyayyar mu a can har in zagaya dake kasashe da dama.