AUREN GADO 1-END

AUREN GADO Page 1 to 10

Maganar mommy ce tasa ya mike tareda cewa mommy is here bari inje. Ya fita da sauri, tana tsaye tareda Khaleel Wanda shigowar shi kenan, tare suka zuba mai ido suna kallon shi, Wani irin mugun kallo ta watsa mai, “uban me kakeyi a ciki?  Shiru yayi ya kasa Amsata, “Ahmed idan ka ketare iyakar da nayi maka banyafe maka nono na da kasha ba. Tafada tana nuna shi da yatsa, saurin daga kanshi yayi tareda girgiza kai kawai ya wuce domin bazai iya magana ba, 

Khaleel ne yakalleta “why mommy? d’an  ubanka, wallahi kaima kaji ko a mafarki naji ka fada soyayyar Y’ar talaka bazamu kare lafiya dakai ba. “Saboda me?  Talaka ba mutum bane mommy?  “Me ake da sunan talauci ma?  Ni wuce bani wuri kuma kaji Abinda nace maka ko ku nemi Amaren ku sallame su banason harkar tsiya tunda dai Allah ya Azurta mu, idan bazaka iya cirewa a jikin ka ba kazo inbaka kabasu. “Wallahi mommy ba shegiyar da zanbawa kudina saboda tayi taron banza ai sunada kudi kowacce Aljihun ta yayi kuka, yafada yanayi gaba batareda ya tsaya saurarar taba, “kaga d’an banza, ai da Ahmed ne yanzu zaiyi Abinda nace Amma wannan mai taurin kan tsiyan sai mun sha fama. 

Biki fa yazo, Amare nata shan even, momy yau ne take nata taron gidan makil da mutane ta gama cika gida da manyan mata y’an karya unguwar kawai daka shigo zakasan biki akeyi na kece raini, Naziya tun da gari ya Waye take jinta wani iri, mugun sanyi da zazzabi ke rufeta ma saboda damuwa, yau dai ba aiki domin komai odar momy tayo har Abinci, 

Don haka tana kwance tana lazumi da carbinta na yatsa,  Shigowa tayi cikin fada, “ke banason bakin ciki da kishi ki tashi ki shirya ki fito, kinzo kin kunshe a cikin daki kamar tsohuwar munafuka, Aure dai gobe insha Allahu sai an daura shi ko zaki mutu, in banda Abunki keda ko dadin Auren baki sani ba meye na kishi, don haka fito maza yanzu mutane natanbaya Ina uwar gidan Ahmed. 

Tashi tayi cikin Sauri, tace “toh mommy, ta wuce bathroom ta sheko wanka, cikin kayan da momy ta bata ta ciro wani lafiyayyen leshi riga da sket kamar dinkin Amare ta saka, tana taje sumar ta taji Sallamar y’an uwan ta, Aunty Raliya da Aisha harma da Shukrah, wani irin tsallen dadi tayi domin Wannan ne karon su na farko a gidan nata, ta karbi d’an karamin goyon Aisha tace “Aunty my kalefa ya Kara wayau. Kallon ta sukeyi kawai domin sunga Alamar rama atareda ita ga kuma damuwa, basuce komai ba saida suka natsu shukrah ta tayata kwalliya ta murza dauri,  sukace muje ki rakamu mugaida uwar mijin ki. “Toh tace suka fita, tana can kuryar dakinta da kawaye sai shewa sukeyi ita tafara Sallama  wasu suka Amsa wasu suka zuba mata ido,  suga Ina wannan kyakkywar ta fito, “mommy ga yayyina sunzo su gaisheki. “Toh sannun ku da zuwa, tafada tana gyatsina, kije dasu can dakin ki kisa Abasu komai domin akwai wadatar shi anan kuje. Tafada batareda tajira ko gaisawa suyi ba. Aisha dayake tanada fushi, har ta juya, Raliya ce ta tsaya tace “Allah yasa ayi a sa’a yakuma kade fitina, wasu sukace Amin. Ta juya Naziya tabi bayan ta, 

Suna shiga dakin Aisha tafara sababi “wallahi Aunty Raliya wannan Matar batada mutunci yanzu dama Abunda ake fada gaskiya ne, gaskiya ni da malam zaiji magana ya raba Auren nan kawai. “Kinsan me zakiyi?  Dakin bar nan saikije ki same shi kuyi magana kinji Aisha. Raliya tafada cikin haushi, wane irin Abu ne zaki  tadawa yarinya hankali da mugayen kalaman ki, to sai me akanta farau da irin wannan uwar mijin?  Don Allah kirika tausasa zuciyar ki. “Kiyi hakuri Aunty Abun ne yabata mun zuciya kalli yanda yarinya ta koma saboda fitinar wannan Matar, yanzu yarinya ko wata biyu kwarara batayi ba za azabgo mata kishiya wallahi ba adalci.  “Ya isa bashi yakawo muba munzo ne mu debe mata kewa  don haka don Allah ki daina mitar haka. Shigo musu da Abubuwan ciye ciye tayi ta baje musu tareda daukar kaleefa tana mai wasa, 

Domin su dauke mata damuwa suka saki jikin su sosai tareda yimata hira tareda shawar wari, ta saki jiki a ranar, lokacin da aka fara taron ma tare suka shirya suka fito wanda tun shigowar ta gidan wannan ne karon farko data tako kofar gidan a yanzu ne take sanin Aljannar duniyar da take ciki,  Suna fitowa khaleel na shigowa  rikeda key cikin manyan kayan da ta lura yanzu yana kokarin sakawa, kallon ta yayi ya dauke kai tareda matsowa ya gaida su Aunty cikin girma yace kuzo muje inkai ku. Taso tace bazata shiga motar tashi ba Amma ba hali domin sun Ansa har suna godiya, Aunty Raliya tace munko gode domin bamu san wurin ba, shukrah ce agaba ita dasu Aunty a baya fuskar ta turbune domin Allah dai yagani tamafi kaunar mommy akan khaleel, a harabar wurin ya Ajiyesu dai dai ana kawo Amaryar tashi fauzy wadda tasha ado kamar zataje gasa cikin tsaddun bridal dress, Washe baki tayi tayi saurin nufoshi “baby “kazo. “No banzo ba mutane nakawo am going back, yafada yana shigewa cikin motar ya datse, su Aunty sukayi mai godiya  yace bakomai batareda ya ko kalli gefen Naziya ba, gaba daya kawayen ta sukayo mata cah, “angon kenan Fauxy gaskiya gayen nan yaje, Amma akwai wulakanci. “Ba ruwanku I love him like that. Tafada tana juyi tareda cewa suje, suka take mata baya tana yiwa su Naziya kallon banza, 

An barar da kudi a wannan taron na gagaruman mata da hamshakai, to suma dai ba laifi domin sunyi kwalliyar su cikin mutunci ba wadda tasaka gyale dukan su hijabine, Wanda ya janyo suke musu kallon rashin wayewa da tsantsar kauyanci,  su momy an barar da rawa da kudi itada sauran iyayen Amaren, su Naziya na gefe itada y’an uwan ta har akaci aka sude, fitar tata tasata cikin farin ciki at least  tafito a cikin wannan gidan dayake kamar kurkuku a wurin ta. 

aka yi komai suka yi gidajen su, tayi farin cikin kasancewa tare dasu domin sun Cire mata kadaici da damuwa,  Wanda sukayi mata Alkawarin dawowa Washe gari yinin bikin, throughout ranar har dare batasa Ahmed a idoba, an zubawa Amaren kayan su a sababbin ginin nasu dake gidan, kowacce an narka mata dukiya fiyeda tunani, dama haka Hajiya bilkisu takeso. 

Kayan Naziya da ko a ido bata taba ganin suba tuni antattare an zuba su a store an zuba na Amarya…….. ????

*Matar Soja*

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button