AUREN GADO 1-END

AUREN GADO Page 1 to 10

Hour guda ta kaisu gidan na kawun nasu Alhaji modu mai gwal wanda D’an kasuwa ne sosai a harkar gwalagwalai, mutum ne a tsaye akan zumuncin shi domin baida wasa yanada mata biyu da yara sunkai goma, shikadai Hajiya balkisu ke shakka domin yafita fitina kuma shima yanada kudi shiyasa take ragamishi domin sau tari yakan yimata Abu tace yaci Arzikin Aljihun shi. 

Sunada kanni biyu mata bayan mahaifin su khaleel  shine babba sai Alhaji modu din, su Y’an Asalin garin maiduguri ne iyayen su ne suka kawosu babban birnin na kano, sunginu suma duka domin ba talaka a cikin su har matan ma domin suna gidajen kusoshin kasar mu, 

  

Y’an mata ne birjik a gidan wainda kowaccen su nada burin samun daya daga cikin wa’innan zaratan mazan saidai sam su Hankalin su baya kan kannin nasu infact basa burin Auren zumunci ma, itama Hajiya balkisu bata ra’ayi domin batason ya’yan ta suyi Aure inda bazata iya juya Suruka ba,, 

Domin tasan Y’an Uwan mijinta duk ba wai mutunci sukeda shiba wanketa zasuyi akan ya’yan su, 

Sun samu tar bar bangirma daga uwar gidan Kawu modun kafin ya dawo, 

Sundauki lokaci a gidan har kawun nasu yazo, wanda yayi farin ciki sosai ya musu nasiha tareda basu shawarori, “yanzu tunda kadawo khaleel saika tallafawa D’an Uwan ka domin yayi matukar kokari wajen tafiya da campanoni da kuma masana’antun ku, sai kuci gaba da tafiyar da kasuwancin ku cikin tsari, Sannan naje munyi magana da uban Naziya, Auren naku nan da sati biyu aka tsayar don haka ka je ka karasa shirin ka  “na kammala komai kawu ni ta wajena. “Toh masha Allah, sai mu jira lokaci Allah ya tabbatar da Alkhairi, Amma dattijon nata mutumin Arziki ne baidamu da Abin duniya ba gaskiya karka damu da shirmen mata wannan gidan irin shi ya kamaci namiji ya nemi Aure. Wani irin dad’i yaji tareda sauke Ajiyar zuciya, saida suka yi magrib kafin su bar gidan, suna hanya yana bashi labarin Naziya,…….. ????

*watch out, domin salon zai tafiyar daku masoya muje zuwa*

*Matar Soja*

???????? *AUREN GADO* ????????

                           

*Matar soja ce*

Daga marubuciyar 

KUSKURE NA

BARIKI AUREN SOJA 

MUK’ADDARI 

WANAKE AURE 

ZANYI BIYAYYA 

And now AUREN GADO, 

 ???? page

3⃣&4⃣

………….. D’an karamin gidane mai zaure a cikin tsohuwar unguwar ta jakara, almajirai ne birjik a zauren da Alama malami ne a gidan  mai Y’ar Karamar tsangayar Almajirai,  ko tsakar gidan ma akwai wasu dakuna dake dauke da Almajirai, rayuwar gidan sun dauki Almajiran kamar Yaran gida ba kyama ba wulakanci, matar gidan inna kulu mace mai hakuri, tanada ya’ya  mata guda hudu manya biyu sunyi Aure sai Naziya da kanwar ta Shukrah, Yanzu Naziya nada shekara goma shatakwas sai shukrah mai shabiyar, ta kammala secondary dinta Bana a makarantar gwamnati, a tsugune take tana wanke kwanonin da suka bata Y’ar Karamar wayarta ce a kunne a gefen ta tana sauraron karatun Al’qur’ani mai  girma tana bi a hankali cikin kwarewa, 

Kare mata kallo nayi domin yarinyar batayi Kama da kalar talaka ba  domin dai dai da duddugen kafarta farare ne tas kyakkywa ce sosai kamar wata Y’ar larabawa tana sanye da guntun hijabi akan al adar ta da kuma koyarwar inna kulu domin gidan su akwai mazajen Almajirai akoda yaushe,   fitowa dattijuwar tsohuwar tayi tareda cewa “inkin kammala ki dora mana Abincin rana Naziya, shukrah ta kai mana markade tunda duk babu  Almijirai yau, “toh Inna. Tafada tana wanke wurin data bata, she is really cool and beautiful ga tarbiya dake tattare da ita jikinta ba rama kuma bakiba duk da tana cikin hijabin ta nagano hakan jikinta D’an dai dai bazaka taba yimata kallon talauci ba duk da Abinci baifi karfin tukunyar suba, mahaifin su yana koyarwa yana sana’oin shi wanda yake daukar gidanshi da kuma hidimomin iyalin shi, 

Haduwar  ta da Ahmed wata rana ce tadawo makaranta a gajiye shikuma yazo unguwar su gidan wani yaron shi dabaida lafiya, tafiya takeyi cikin gajiya a kuma natse ta gefen titi, y’anda ya kwaso motar tashi yasa ya watsa mata ruwan datti kasancewar gari ne na damuna ga kuma yanayin unguwar da yatara guraben ruwa ta ko Ina,  saurin jatayi ta tsaya domin gaba daya uniform d’inta ya baci Har fuskar ta ma ruwan ya fallatso mata, saurin fakawa yayi ya fito da sauri yana so yabata hakuri, 

Dago kyawawan idanun ta tayi tareda goge fuskar ta da gefen hijabin ta inda jan ruwan bai bata ba, ta kuma kallon y’anda ya saki baki yana kare mata kallo batareda ya iya cewa komai ba, yarinyar ta gama tafiya dashi, juyawa tayi ganin baida niyyar cewa komai tayi gaba, saurin shan gaban ta yayi “Am sorry please ki tsaya muyi magana, ya zaki wuce batareda kince komai ba bayan nayi miki laifi? 

Saurin Tsayawa tayi tareda dago idanun ta masu narkar da zuciya tace “nice zanbaka hakuri domin hanyar bata Y’ar talaka bace Nazo kuma na tsaya, sannan don Allah ka matsa in wuce kafin ayi wani tunani akaina a cikin unguwa ba mutuncin gidan mu bane tsayuwa da bako a kan titi. Tafada tana rabewa tayi gaba. 

“Wow wow wow what a magic voice, yafada yana binta a hankali tana sauri har ta fada gidan su da gudu domin tana jin takun shi a bayan ta   a mugun tsorace take dashi domin yayi Kama da Aljani a wurinta domin he is very handsome kana ganin shi kaga D’an hutu,. 

Gefen Ahmed tunda yasa Naziya a ido yakasa sukuni saida yabi ta gefen yaron shi yaji komai akanta, tuni yagano Y’ar babban gidace wato gidan dattijan kwarai,  baiyi kasa a guiwa ba ya dawo yasamu mahaifinta tareda neman izinin neman ta, Malam garba yaso ya hana domin ganin D’an gidan wani ne Bayason ya saka Y’ar shi cikin matsala, ya nuna mai mahaifin shi ya rasu kuma shike rikeda kanshi ba wata matsala, bai Amince ba saida ya turo kawun shi yazo suka tattauna ya Amince yabada izinin neman ta,. 

Allah yagani bawai Ahmed baiyi mata bane, ita batada burin shiga gidan da yafi karfin ta wanda bata ma riga taga dukiyar ba tukun kawai shitake gani   kudin su na bata tsoro, ganin irin k’a’i dar mahaifin ta,  baya ko sake mata kudi infact tuni ya daina zuwa da shigar da zata hanata sakewa dashi domin ya lura da yanayin ta dana gidan su tsab, yasamu kanta ta hanyar nuna mata akarkashin wani yake shima yana hustling ne,. Shiyasa yasamu kanta har ta Amince suka Gina soyayya mai karfi a tsakanin su she really loves him domin he is very simple baida fushi baida girman kai saurayi ne mai natsuwa wanda ko yatsanta bai taba kokarin kamawa ba soyayya yake mata mai tsafta, har kawo yanzu da Al amarin yakai ga zancen Aure, zaman ta dashi tagano Abu biyu sune masu matukar muhimmanci a rayuwar shi, mommy and khaleel wanda basa hira sutashi bai kira sunan shi ba tagano irin tsantsar soyayyar da yakewa kanin nashi ta hanyar bata labarin shi a kullum zaice “in munyi Aure zaki rika dafa mai Abincin da yakeso baya son irin namu na nija zansa akoya miki irin dishes din da yakeso.  Abun na bata mamaki ace mutum Abincin mu na nija mai shegen test baya burgeshi sai mara magi? she almost know everything about him by now saboda labarin shi, tasan yana karatu a waje kamar yadda Ahmed yafada mata kawun su ya kaishi waje karatu, Ita kanta so take taga wannan khaleel din da labarin shi baya karewa a bakin Ahmed,. Tana son Ahmed sosai halin shi, yanayin natsuwar shi ya banbanta da na samarin zamani masu burin cakumar mace da sunfara soyayya……..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button