AUREN GADO 1-END

AUREN GADO Page 1 to 10

Wannan shine D’an takaitaccen labarin Naziya da Ahmed. 

A hanyar su ta dawo wa daga sabon titi yake bashi labarin komai na su Naziya tareda fadamai boye mata kudin da yayi saboda batason mai kudi y’anda ta nuna mai. Khaleel yasamu kanshi da yin dariya, ” she is funny wace mace ce  batason hutu da kudi in this era? ” my Naziya wants a simple life ba a ginata akan greedness ba, all this kyale kyalen duniya basa burgeta do you know nasha siya mata gifts in ajiye domin gudun matsala ko fushin ta, do you know tun zaman mu bata taba demanding tana bukatar wani Abu a wurina ba, “she is such a diamond in the rocks, she is different khaleel my Naziya is perfect I told you. “Hmmm Allah yasa tana sonka like you love her? “She do Insha Allahu, koda baikai wanda nake mata ba nasan tana sona,

Karar wayar khaleel yasa yace “my God this witch. Yafada yana cutting call din. “Fauzy right?  “Yes yaya ta cika naci bana son mace mai naci. “Hhhhh you are lucky khaleel fauzy batada laifi and secondly irinta mommy keso Y’ar gidan wasu kaga babanta ne minister na kudi, don haka bakada matsalar mommy kabada kai musha biki bayan nawa.   “Yaya why ake Aure? “Hhhh khaleel saboda Aure sunnah ce mai karfi, sannan ba Abinda ke karawa namiji mutunci irin Aure, ga kuma samun natsuwa da soyayya idan kayi dace. “Yaya I don’t need any natsuwa a wurin mace ni. “Ah bakada lafiya ne?  “Kalau nake kawai bana jin akwai macen da zatasa inji ni a namiji sai kawai in lafiyata ta motsa,. “You are wrong khaleel, kana samun macen da kakeso manhood dinka yadaina  kwanciya cikin sauki, domin the moment you fall in love, zaka ji duk duniya ba Abinda kakeso sai kasamu kwanciyar hankali da farin cikin zuciyar ka, you are my younger brother but bazan boye maka ba na matsu ba a daura min Aure da Naziya ba am eager to have her ban taba jin lafiya ta tana aiki ba saida na hadu da ita, don haka kaima duk ranarda ka afka soyayyar wata zaka gano komai. Dariya kawai yayi domin shi yasan lokacin da kawai yake samun erection sai inya tashi a bacci yake sanin he is healthy ba wata Y’ar macen dake daga mai hankali   domin bai sawa ranshi ba ma bare Abun duniya ya dame shi. 

  

Cikin unguwar suka nufa wadda tuni yaji wani iri musamman irin kofar gidan dayaga sun tsaya  Almajirai birjik sunata karatu ga hasken farin wata daya dallare KO Ina fiyeda hasken lantarkin dake wurin,   wayar shi ya daga tareda danna number ta, ba bata lokaci ta daga hade da yin sallama, “Gimbiya kifito ku gaisa da heartbeat tare muke dashi. 

Cikin murna ta mike tace “gani nan zuwa yanzu inga wannan kanin namu. 

Yana kishingide ko motsi baiyi ba impact bayajin zai iya fitoda takalmin shi wajen wannan unguwar, dole momy tayi spark ai, don ma batazo tagani ba ma da in sama da kasa zata hade ba Yarda zatayi ba  yasani. 

Fitowa tayi cikin natsuwar ta sanye da hijabin ta, ta karaso jikin motar dayake tsaye nad’e da hannu, ya zubawa kofar gidan idanu har ta karaso kusa ta d’an tsaya nesa kadan kanta akasa ta gaida shi, “Ina wuni. “Lafiya kalau gimbiya ya kike? “Alhamdulillah, cikin  muryar ta mai cikeda natsuwa, kwankwasa glass din motar yayi, ya sauke a natse tareda gyara zaman da yayi kamar wani sarki,  kamshin shi mai matukar tsada ya huro tareda muryar shi mai cikeda wasu irin sirrika suka sakata dago kai cikin  sauri, 

A cikin kyawawan idanun shi nata yasauka domin hasken motar na haskashi dakyau, wani irin sanyi jikin ta yayi Mata domin Sam baiyi Kama da sunan kanin Ahmed ba a wurin ta saidai Yaya, irin cika motar da yayi da kwarjinin shi tareda kamshi da cikar haibar shi, kallo daya ta sauke idanun ta akanshi Wanda tsab da ita gwanace ya isa ta Zane hoton shi, daga ganin shi bazaiyi yawan magana ba, kuma zaiyi miskilanci sosai. Tunanin ta ya katse ne lokacin da taji saukar muryar shi a cikin kunnen ta “Yayana naga Auntyn zamu iya tafiya ko?  Shine kalmar data fito kawai batareda gaisuwa ko wani dogon zance ba. Ta shirya sakewa dashi domin karo dankon soyayyar ta a zuciyar Ahmed,  amma is impossible yanzu don taki jinin girman kai da nuna isa just because yaje waje karatu, tuni taji yafita a ranta takuma daura damarar Kama kanta da Al amarin shi koda ta shiga gidan nasu,.  Saida Ahmed ya leka kanshi tareda zuba mai ido “come on brother kafito mana ku gaisa da kyau, “no mungaisa daga nan ka sallameta mutafi nagaji kasan bangama hutawa ba, yafada a mugun kagare yake subar wurin yanajin warin Almajirai daga inda yake Idan yakara more minutes a wurin he will surely vomit,. Ya lura da yanayin shi don haka a gurguje ya sallameta ta tafi tana mai jin takaicin wannan khaleel din,. 

Yana tada motar yace “Yaya wannan Y’ar yarinyar zaka Aura?  Why?? she is too young for you please, fuskar shi a kwabe, “hhhhh she is perfect banason Auren katuwar mace ko over twenty nafison irinta mutum ya mori kuruciyar ta yafi Amma Idan ka Auri wayayyun mata bazaka mori komai ba, nafison innocent girl da zankoya wa komai,. “Hmmm zakasha aiki wallahi ai wahala zakayi kafin wannan ta iya daukar ka, kuma Yaya iyayen ta suka yarda suyi mata Aure? “Yes saboda mu anan takai Aure tunda ta kammala secondary,. 

“What?  Yaya this is too much, da Ina nan bazan bari kafara sonta sosai ba gaskiya. “You are too late now, domin inaji a jikina Idan ban Auri Naziya ba zaku iya rasani  so ku tayani Addu’a kawai Ina son ta fiyeda tunanin ka nasan you will always support my back. “Of cos brother Insha Allah. 

Karfe goma suka isa unguwar su, Wanda mommy Saida taci gaba da fada “kunje ghetto Area ko nasani saiya jamun kai, ka wuce kayi wanka kazo kuci Abinci kaima wuce ka watsa wainnan kayan dustbin kafin ka dawo falon nan kajini ko?  Wucewa yayi cikin sanyin jiki ya tafi dakin shi Yana mai jin bakin cikin halin na momyn shi, kasa fitowa yayi saboda rashin jin dadin Abun, shima khaleel kasa cin komai yayi ya kalli momyn dake kan korafi “mommy why please?  Ki yi hakuri Ki daina fada akan abunda dole za ayi. “Yes za ayi Amma ni Balkisu bazan bari ya cakuda min iri da na talakawa ba mu zuba tunda dangin ubanku sun nuna sunfini iko akan shi  ni kuma zan nuna musu sai naso komai ketafiya mu zuba nida su. 

“Momy ji nake kamar in koma bangkok kawai domin bazan iya tsayawa inga d’an uwa na a damuwa ba, please Ki barshi ya samu natsuwa mana. “Khaleel, kana ganin uwa zataki d’an tane?  Ina son Ahmed kamar yanda nake sonka saidai bazan iya  kawar da idona akan kwashi kwaram din da zai debo min ba. 

Mikewa yayi kawai cikin fushi yabar mata Abincin yayi dakin yayan nashi,  a kwance yake Yana tunani, dafashi yayi, dagowa yayi tareda rungume Khaleel din, “brother am worried, bansan irin zaman da zamuyi da Naziya a gidan nan ba, bana so injefa Y’ar mutane a damuwa bayan an bani amanar ta. Bubbuga bayan shi yayi “karka damu Ina nan zan taimaka maka ba Abunda zai samu baby doll dinka. Yafada cikeda dariyar tsokana domin ya kwantar da hankalin d’an uwan nashi, 

Shigowa tayi dauke da tray tana fara’a domin taga Alamar Idan tayi sake yaran  nata zasu juya mata baya akan zancen Auren nan, Wanda bazata taba Yarda da hakan ba, 

“Toh yaran momy ga Abincin nakawo muku ni na damu kuci, kashin awaki, ta ajiye a tsakiyar gadon tareda jansu da hira kamar zata mayarda su ciki, tuni suka ware suka kwashi deshes din, tana cewa “bayan rasuwar mahaifin ku nayi iya bakin kokari na ganin bakuyi maraici ba, Alhamdulillahi yau dukan ku kunkai matasa Abun Alfahari a wurina,  forgive your mother Ahmed na dauki buri mai girma akan ku naso nice zanyi maku zabin matan da suka dace daku Amma ka watsa mun duk shirina Ahmed. “Am sorry momy, kuma nayi miki Alkwarin zaki samu Naziya a duk yanda kikeso bazakiyi dakin sani ba yarinyace mai tarbiya da kin Amince da tuni nakawo miki ita ma kingan ta. “Aa tunda ansa rana ai lokacin zaizo don haka basai ka kawo taba, bakomai zan cika burina akan khaleel. “No mommy khaleel ma yanada tashi zabin ai, yafada Yana kashe mai ido, “no no no bana sonta Yaya please meye haka she is my mate fa tare muka kammala karatu why zaka ce Ina sonta ita keso na ni banga Y’ar da zanso ba har yanzu’

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button