AUREN GADO 1-END

AUREN GADO Page 1 to 10

Wani irin dadi mommy taji ganin khaleel bazai juyuba a wurin mace tunda ita keso shi bayaso ai irinta takeso, “wow Auta na wacece wannan yarinyar? “Mommy Y’ar gidan minister kudin Nigeria ce, “what?  Tafada tana dafe kirji, “Y’ar gidan mai nasara kake fada? Oh my god khaleel, ta rungume shi, that’s my son, ka kawomin ita kaji kace tazo inganta Amma ka gama wanke min zuciya d’an nan. Tafada tana mikewa bari inkira Auntyn ku infada mata tafara shirya mana babbar harka ta Fita tana danna kiran kanwar tata mai ra’ayi irin nata. Binta sukayi da kallo suna mugun mamakin halin na mommy, sai kace wadda bata jiku da kudi ba, kullum she is hungry for more, kallon Ahmed yayi da fuskar tausayi yace “why zaka fada mata Yaya kasan am not ready, kuma yanzu tunda taji bazata taba bari insha ruwa in Ajiye cup ba. “Is OK fauzy love you a lot kuma meye laifinta nasan tun lokacin da kuke tare, ya isa haka ka Amince bayan nawa kawai a daure min kai, do you know, Ina mafarkin ganin Auren ka?  Ina so inyi witnessing Auren ka inga jinin ka. “Hhh oh come on Yaya kamar wani tsoho na barin wasiyya please tare zamu cika gidan nan da yara, “who know Khaleel? Allah kadai yasan me zai faru gobe, kasan cewa nan gaba kaine zaka rike gidan nan?  “Why Yaya?  Indai har kana nan bazan taba daukar girma ba saidai in tafiya zakayi dole in rike kana dawowa zanbaka komai domin ka shagwaba ni tuntasowa ta Abu daya nasani shine in saka master card dina inciri duk Abunda nake so ba tareda antanbaye ni me nayi dasu ba, Yaya nasan kudin da daddy yabari bawai haihuwa sukeyi da kansu ba kaine kakara habaka su har suka kai haka kaine jigon gidan nan bazan taba iya Abinda kakeyi ba…… “Shhhhhh zakayi Idan bana nan fiye ma da Wanda zanyi saboda I believe kai jarumi ne kafini iya tafiyar da Rayuwa. “Enough of this discussion kana sani a damuwa. “OK now kakira fauzy kafara bata kulawa domin tunda zancen yaje kunnen mommy ba fashi, yafada Yana dariya,. 

  

Fita yayi daga dakin yayan nashi yanajin wani iri “Aure?  Gaskiya bai shirya ba infact zaiyi ne saboda yayanshi ya insisting kuma koda baison Abu Idan yayan shi na sonshi dole shima ya soshi, Allah kadai yasan iyakar soyayyar da yake wa d’an uwan nashi, kwanciya yayi a kujera a dakin nashi Yana mai runtse idanun shi, so yake ya tuna komai na fauzy da quality’s dinta just for Ahmed, Amma first thing da yafado mai a rai yasa ya zabura  tareda  girgiza kai, “no no no why her? 

 Cikin Sauri ya dauki wayar shi domin ya k’aryata  tunanin shi, fauzy ya Kira, kamar mai gadin wayar ta ta dauka jikin ta na rawa “oh my goodness darling you call me?  Tafada tareda Sanya kukan farin ciki, tundazu take kiranshi yaki dagawa har wani zazzabi takeji saboda damuwa tana yimai wani irin so mara misali. Tun isowar ta ake tarairayar ta Amma duk natsuwar ta bata tare da ita, 

“Yes I call. Yafada Yana gyara zaman shi domin baisan ma mai zaice ba kuma. “Tank you darling for calling, please Ina so inganka kasan is hard for me kwana daya bansaka a idoba  I can’t. “Is OK zaki iya zuwa gidan mu gobe yanzu dare yayi. “OK am coming tomorrow tank you darling. Tafada tana buga tsalle tareda rungume filo, tasan yafara damuwa da ita tunda har yake so taje gidan su yanzu, hakurin ta ya fara aiki yanzu. Kwanciya tayi tareda Addu’ar gari yawaye ta ganta agidan su. 

Gefen Naziya ta shiga gida da takaicin khaleel, domin yaron mugun d’an wulakanci ne, inba wai gizo idanun ta ke mata ba kamar kallon kyama yake mata, bayan duk unguwar su an shaida tsabtar su, duk da suna fama da Almajirai Inna kulu nada kokarin ganin ta tsabtace gidanta sosai,. Kwance take tana juyi shukrah ta matso gefen ta akan Y’ar madai daiciyar katifar tasu, tace “Aunty lafiya? “Hmm bakomai. “Aa Ina kallon yanda kike ta juyi tundazu kinkasa bacci, meke faruwa ne? “Kawai Ina tunanin yanda zan zauna da Ahmed ne tareda kanin shi shukrah dazu sunzo, baida k’irki irin Ahmed ya cika girman kai  da nuna shiyayi karatu a kasar waje. “Ni kuwa Aunty kallon Arziki sosai nakeyiwa Yaya Ahmed fa. “No yafada min Yana da ubangida mai kirkine watarana motocin yake zuwa dasu, “nidai Aunty Ina tantama domin ko tsarin jikinshi ya isa ya nuna Yana cikin hutu. “Ni kuma me zakice dani?  Tunda kowa kallon Y’ar masu kudi yakemin a school ko in munfita, halitta ce kawai. “Hmm tom kiyi bacci Ki kyale wani kanin shi Bashi zaki Aura ba. 

Washe gari Karfe goma tayi mata a gidan su khaleel cikin tangamemiyar motar ta ta yayi, da kanta ta tuko kanta, da taimakon shi ta zo gidan domin unguwar su ba boyayya bace,  momy ta zage sai rawar kafa takeyi an shirya mata tarba Kala Kala, cikin adon jan material doguwar Riga dinkin yayi na yayan masu daula,  taci gwala gwalai wuya da hannayen ta tana zabga sheki da kamshi. Ta hadu ba sauki domin ta iya caba ado. Tasamu tarba gefen momy, Wanda koda tazo gidan bai tashi baccin safe ba, 

Momy sai Ina ta saka Ina ta Ajiye takeyi da ita, sai zare idanun ta takeyi taga inda zai bullo. “Huh khaleel na bacci haryanzu bai tashi ba,   kinsan da gajiya a jikin shi.   

Shigowar Ahmed ne yasa Momy tace “ka duba d’an uwan ka ko ya tashi ga bakuwar ta iso. Gaisawa sukayi Yana Kara ganin wayewar ta da kudi Wanda yasan ba yanda za ayi Naziya tazo gidan nan saboda shi, banbancin yayan talaka kuma y’an gidan mutunci kenan da kuma ya’yan masu kudi. Yanzu meye Abun burgewa a nan mace ta nuna rawar kafa akan namiji, idanun fauzy ya gama budewa gaskiya and zasuyi kusan sa’a da Khaleel like he said, wucewa yayi Yana daya sanin bashi goyon baya akanta,. 

A kwance ya sameshi Yana kallon saman pop, “oh you wake up? So kazo fauzy is here. “You see tunda Asuba mayyar ta tanbayeni address nafada mata don uwar ta a gidan mu zata karya?  Dariya Ahmed yayi, “Auzubillahi yada zagi?  “That’s why Yaya bana sonta wallahi batada kamun kai  Sam ace Karfe goma ta zo wurin saurayi saikace ba iyayen ta a gidan. “Yanzu dai katashi kayi fresh up kafito tana jira mother in law dinta ta bata big welcome. Tashi yayi ya shige bathroom, like Always Saida ya kwashe hour guda kafin ya fito Wanda shirin nashi ma Saida ya kwashi rabin hour cikin guntayen kayan nashi kamar yanda ya saba. 

Cikin takun kasaita da shan kamshi ya fito falon,   fuskar shi Sam ba fara’a, “ga shinan yaron kirki ya fito. Mommy Tafada tana mikewa tareda taroshi kamar wani kwai jitake kamar ta goyashi saboda so, jikin fauzy na rawa tace “hy darling kamar ta ruga ta rungume shi takeji. “Tashi kuje dakin shi zakufi sakewa bari insa a hado muku breakfast akawo ciki. Cikin sakewa tace “Saidai baby ni ai mommy kin cika min ciki tun zuwana kike duramin ciye ciye, Tafada tana Dariya, “Allah Y’ar nan, to bakomai ai gidan kune nan.  

Zama yayi a falon fuskar shi a cakude yace “ke iyayen Ki basa gidane kika fito early morning? Kallon fuskar shi tayi tareda yin murmushi duk da tasan maganar banza yafada mata ranta bai baci ba, “mommy na nan dady na nan kuma sun san inda naje. “Really?  Kuma basuyi kokarin hanaki ba? “Why zasu Hanani?  Bayan su masu goyon baya na ne akan duk Abinda nakeso kasan cewa sun san komai akan ka dady na a shirye yake da katuro neman Aure na, please khaleel ka cika mun burina I promise zaka sameni yanda kakeso zan share maka damuwar ka duka zanbaka gatan da mata basa iya bawa mazajen su just give me chance. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button