AUREN GADO 1-END

AUREN GADO Page 1 to 10

Daya cikin gwaggon nin nata tace “kawo Abar nan inrike da ita zankoma Y’ar nan domin ko takarda bazaki shara ba a gidan nan, “Toh ai gidan da waje ma babu ko Alamar d’aud’a  bare ciki, ai wajen ma ni yafi dakina tsafta, haka suketa sambatu tsakanin su. Ita kuwa jitakeyi kamar ta ruga da gudu saboda tsoro, wasu irin zafafan hawaye ne ke zubowa akan kyakkyawar innocent face dinta. She is regretting today, wayace ta Amince mai? wayace ta yarda da Auren shi? gashi yayi mata karya yakawo ta gidan da bata taba zuwa kusa da irin shiba. 

A falon mommy ce hakimce itada y’an uwan ta, Zarah ce ke gefen ta da kuma uwar y’an kanzagi fauzy, sunayin Sallama mommy tace Zarah kusa katuwar tabar mar nan akan carpet din Idan sun tafi a fita a Y’ar da ita a waje kar k’uma ta  shigo mana gida. 

Sunji komai a kunnen su jikin su na rawa suka karaso akan tabarmar suka zauna tareda gaida su cikin girma mawa, cikin su daya tayi karfin hali tace “Hajiya toh ga Amanar Y’ar ki nan Allah ya tayaki riko. 

“Ni Amanar me zaku bani saikace wata kishiya ta, to kuji infada muku tun mijina nada rai ko zance bai taba zuwa ba bare ayi zancen yimin kishiya, don haka karma ku fara ku jira Wanda ya Auro ta yazo kubashi…… Yauwa ga shi nan ma, Tafada tana nuna shi domin yana fitowa yaji zancen momyn wani irin zafi tareda damuwa zuciyar shi ta shiga. Khaleel ma yaji komai kuma he is not happy da irin yanda mommy takeyi ga su fauzy dake musu wata irin Dariya kamar sunga kashi  itada zarah, wani irin baci ran khaleel yayi da Sauri ya matso tareda kallon Fauzy, ” ke wace iri ce uban me  kikeyi a gidan mu haryanzu baki tafi ba? 

“Aa banson shirme Ibrahim, ya yarinya tazo maka k’ara zaka hauta da fada? “Mommy angama Bikin tazo ta wuce gidan ubanta tom. Jikin ta na rawa ta zabura ta nufoshi kamar zata fada jikin shi “no please na dauki permission wurin mommy na ta yarda inyi kwana biyu baby just for you….. “Oh come on, ke meyasa bakisan….. Saurin dafashi Ahmed yayi domin bayason more humiliation agaban y’an uwan Matar shi Dama  ita kanta, yanzu yana tunanin how he is going to face her ne ma. 

Shiru yayi tareda juyawa da Sauri ya yi cikin dakin shi dake part din momy,  ranshi yayi mugun baci dole ya koyawa wannan fauziyar hankali gobe. 

Fadin zuciyar Naziya da tunanin ta bata lokacine ma, daya daga cikin y’an uwan mommy ne tace “ku muje in nuna muku part d’in ta, Tafada tana mikewa kafin ya yar ta ta kuma kwab’a, sanyi Ahmed yaji domin yama d’askare yakasa ko motsi. 

Suna shiga suka ware idanu domin basuga ko tsinken da sukasa aka kawoba, wadda ta rakosu ce tace  “wannan dakin mijinta ne gidan su na waje a can akasa da kayan ta, kamar tasan me suke tunani, 

Domin sunga gadajene na kasar waje ba irin nasu d’an wambai ba. 

Cikin sauri sukace “tunda munrako ki Naziya mu zamu koma dare nayi, Allah yabada zaman lafiya da hakuri kinji ki rike tarbiya da mutuncin malam Dana kulu domin kinsamu tarbiya dai dai gwargwado kinsha nonon hakuri da kuma mutunci, Allah ya kade fitina. Suka juya cikeda sanyin jiki, riko daya daga cikin su tayi tasa kuka “Don Allah gwaggo karku tafi kubarni ni kumayar dani gida wurin Inna bana son nan gidan. Tafada tana kuka mai cikeda tausayin kanta da Rayuwar ta, daga shigowar ta harta karanto irin Rayuwar da zatayi a cikin wannan gidan. 

Shigowar Ahmed ne yasa takara rike ta gam tana gunji.  “Ahmed ka rike Amana ga Matar ka mu zamu tafi kaji. Babbar Tafada cikeda tausayin Y’ar tasu, hannu yasa zai rikota tayi tsalle ta koma gefe tareda sakin su tana gyara hijabin ta dogo.  

Fita sukayi ta koma gefen dakin ta zauna tareda saka kuka mai zafi da kuma k’ara, 

Rakasu yayi a gurguje yadawo domin kukan da takeyi bakaramin daga mai hankali yakeyi ba. 

A zaune take ta hada kai da guiwa tana kuka mai ciwo. Zama yayi dabas a gaban ta cikin sanyin jiki, tanajin kamshin jikinshi daya cika ko Ina, takasa dagowa. Hannun shi ya dora saman kanta, da yasa tayi Saurin dagowa tareda ja baya tana Kara hade jikinta wuri daya, 

“Am sorry bazan kuma tabaki ba tunda bakyaso, Amma please kiyi shiru haka kukan ki na tabamin zuciya sosai. 

Yafada yana kallon yatsun Hannun ta farare tas da sukasha jan lalle Hannun ya mugun burgeshi, ji yake kamar ya riko ya tsotsa, bai taba ganin lalle ya burgeshi ba sai a Hannun ta. Jin shirun shi yasa ta dago tareda zubamai lashes d’in ta masu kyau da kuma fararen idanun ta da suka cabe da ruwan  hawaye, taga Inda yake kallo da ya shagalar dashi sosai. Saurin cusa Hannun ta tati cikin hijabin ta da yabashi damar kallon na fararen kafafun ta, wani irin gauron numfashi yaja tareda d’an matsawa kusa da ita, ta kuma ja baya again. “Why Naziya? Please karki horani a haka zuciya ta zata buga, ki horani ta kowacce hanya but karkiyi min iyaka da zuwa gareki, am dreaming about it always, nasan ni mai laifine a wurinki, Amma kisani ni mai sonki ne shiyasa na boye miki gaskiyar rayuwata Naziya banason in rasaki I love you so much my wife. Yafada yanajin  wani irin shauk’i da yanayi mara misali, kallon shi takeyi wani iri kamar zataga wani Abu daban, batajin zata iya Rayuwa a cikin wannan gidan tareda kuma mahaifiyar shi da itace farkon matsalar data Kara girgiza ta. 

“Am sorry Naziya, nasan i’m wrong domin bakiyi planing zama a irin gidan nan ba, yafada yana murmurshi, domin itace mace ta farko dayaga wai batason daula. How silly? Maganar mommy tasa yayi Saurin ja baya tareda tashi tsaye ya kalleta “kazo ka zauna gaban jaririyar yarinya a daren farko to kazo ka wuce dakin d’an uwan ka kowa yasan ango baya shiga dakin Amarya sai anyi budar kai don haka wuce kabani wuri tun ban sab’amaka ba.  

Daukar babbar rigarshi yayi yafita jikinshi a sanyaye. “Ke kuma ki tashi kidaina wannan kukan munafuncin kije kisha Ac anzo inda yafi gidan tsoho  ga katifa mai numfashi aje a more, kin  zo kina kukan munafurci. Tafada tana fita dakin cikin fada.  Zubewa tayi nan kasan dakin tasa kuka, “Ahmed yasa ankawo ta inda bazata taba yin mutunci ba,har wani irin ciwo taji gefen kanta nayi saboda kukan da takeyi.  

A kwance ya samu khaleel idanun shi a bude yana kallon saman dakin wani irin zazzabi yakeji har yanzu Wanda yarasa dalilin faruwar shi,  jin takun d’an uwan nashi yasa yayi Saurin juyawa ya kalle shi, “Yaya ango me kakeyi a nan yau? Yanda yaga hawaye tareda ganin damuwa kwance a fuskar d’an uwan nashi yasa yaji tuni zazzabin shi ya tafi, tashi yayi cikeda damuwa yace “Yaya taki kulaka ne?  Zan bata mata rai Idan ta nemi jefamin kai cikin cikin damuwa. Yafada jikinshi na rawa domin yaune karo na farko dayaga hawaye a idanun jarumin yayan nashi mai hakuri. 

“Mommy. Yafada yana Rungume d’an kanin nashi domin yasamu sauki. “Me tayi kuma?  Fadamai yayi yana jan numfashi, “oh Mommy, Bari inje inyi mata magana. Yafada yana kokarin tashi tsaye, rikeshi yayi tareda girgiza kai, “karkaje tace Al Ada ce sai gobe zan shiga wurin Matata.       

“What kind of Al Ada? “Budar kai. Zabura yayi cikin haushi “let me talk to her. “No leave it, just do one thing please go and check on  her please she was  crying.  

“No kabarta zatayi shiru ka kwanta yau ne kawai tunda ka hanani inyi mata magana. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button