AUREN GADO 1-END

AUREN GADO Page 1 to 10

“Please go Ina so inji ko tadaina kuka, inaji a jikina tana can tana kuka. 

Bayason musu, especially da yayan nashi don haka mikewa yayi kawai ya fita. 

Ba kowa a falon yanzu duk Suna cikin part din mommy Suna hira da shewa, girgiza kai yayi yana tunanin Abinda zai aikata gobe a gidan halin shi dasuka sani bai canja ba bayason rubbish.  Tundaga falon yakejin kukan ta kasa kasa. Wani irin zafi yaji a zuciyar shi, da sauri ya shiga dakin, a kwance take a kasan kamar yanda take tundazu saidai yanzu Ana iya ganin kayan jikinta domin duk hijabin ya tattare ya koma wurin cikinta, zaka iya ganin perfect figure dinta, Wanda ko Ahmed bai taba samun damar ganin ta haka ba, kullum tana cikin hijabi,  akan kafarta idanun shi yafara sauka. 

Wanda wani irin attraction ya rika jansa ya kasa Cire idanun shi, “first time da henna designs ya Bashi sha’awa, ga kafafun ta kamar na turawa a mulmule farare tas dasu, “Wow she is Unique, zuciyar shi ta furta. Domin tsarin jikinta da yake gani,  bai taba ganin small body with a perfect shape ba like her. 

Motsinta yasa yadawo hayyacin shi cikin Saurin tareda tsorata ta zuba mai ido, tana zarewa, domin ita bata taba ganin katon namiji irin shi da guntun wando da singlet a gaban ta hakaba, wane irin gida Ahmed ya kawota, da Sam ba tsari ba wani sanin ya kamata.  Saurin jan hijabin ta tayi kasa tana mikewa kukan nata ya dauke dif,  fuskar shi mai natsar da yaro mai kukan banza, tuni ta hadiyi wani irin miyau, she knows he’s khaleel domin ganin farkon da tayimai bazai taba bacewa a idanun taba. Gaba daya jitakeyi ya cika mata dakin da girman shi, ga fuskar shi mara walwala, idanun shi masu dauke da wani irin sinadari Wanda batasan ma ma’anar shiba.  Juyawa tayi ta Bashi baya ganin ya dauke kanshi batareda ya iya cewa komai ba. Saida ya dauki lokaci kafin yagama tunanin yanda zaifara yimata magana, cikin karfin hali yace “good tunda ba kuka kikeyi ba, Yaya na is worried sosai shiyace inzo in dubaki, tunda kinyi shiru shikenan, yafada yana tafiya batareda ya kuma kallon gefen taba,  a falon yaci karo da ledar da yayan shi ya Ajiye Wanda kowane ango ke shigarwa Amarya da ita, dauka yayi ya koma, dai dai  ta kuma juyowa, idanun ta suka kuma cin karo dashi, wani irin Saurin juyawa ta kumayi   ledar ya Ajiye “you have to eat karki kwanta da yunwa Yaya na zai damu.  Yafada yana fita Hannun shi cikin pocket din guntun wandon nashi. 

Cikin sauri bayan ya fita ta dannawa kofar key domin Allah yagani batason ganin shi again,…………. ????

*Matar Soja*

????????AUREN GADO????????

                           

*Matar soja ce*

Daga marubuciyar 

KUSKURE NA

BARIKI AUREN SOJA 

MUK’ADDARI 

WANAKE AURE 

ZANYI BIYAYYA 

And now AUREN GADO, 

 

Ga masu son su biya ga account details dina, *NAFISA HASSAN SANI 7304736012 @ FCMB* Sai Ku min magana ta wannan number *09069200154*

???? page

7⃣&8⃣

…………… A tsaye ya samu  Ahmed yanata sintiri, yana ganin shi ya rikoshi “kuka takeyi ko brother? Yatanbaya cikeda damuwa. “No Yaya tayi shiru nabata ledar da ka Ajiye a falon relax am sure zataci ta kwanta. Yana gama fada ya haye gadon ya kwanta tareda juyawa yayan nashi baya. “Tank God, and tanks to you brother. Yafada yana d’an samun natsuwa, bathroom ya shige yabarshi idanun shi kur, baya kojin bacci, saida yaji fitowar Ahmed ya rufe idanun shi kamar maiyin bacci.  Saida ya shimfida dadduma ya fara jero sallolin nafila tareda Addu’oi masu zafin akan Rayuwar shi data Matar shi, ba Abinda yake nema sai farin cikin Naziya a wurin Ubangiji tareda neman zaman lafiya a tsakanin su. 

Ganin har Karfe biyu shima yakasa baccin ya diro tareda dauro Alwalar ya tada sallah shima, haka gefen Naziya bayan ta kulle bathroom tafara nema saida tayi da gaske ta gano inda zata latsa ruwan yafito kafin tayi Alwala tafito, dadduma tagani a gefe da Qur’ani ta tada sallah, saida tayi raka’a biyu ta zauna tana jan k’ira’a a zuciyar ta. Domin fadar manzon mune aduk halin da mutum ya shiga to ya koma ga Allah, 

:(Fadhkuroonee adhkurkum washkuroo lee wa laa 

takfuroon 

“So remember Me; I will remember you. And be 

grateful to Me and do not deny Me.) :

Wanda duk ya tuna da ubangiji shima bazai manta da shiba a duk halin da yashiga. 

Sai  Asuba ta tada sallah saida tayi nafila raka’a biyu kafin farillah, taci gaba da karatun ta,  sai Karfe shida ta kwanta a kan daddumar, wani irin bacci mai cikeda salama ya dauke ta domin Qur’ani maganin damuwa ne Idan har kayi Imani da Allah. 

 

Haka gefen Ahmed da Khaleel basu runtsaba saida sukaje Mosque suka dawo, saida Ahmed ya duba kofar dakin nashi yajita a rufe,  bai bugaba domin kar momy taji, dakin khaleel suka koma, kwanciya yayi yana murmurshi “daga yau bazan kuma kwana nikadai ba, ko tareda kai “am going to sleep on my wife shoulder, yafada with so much excitement, Runtse idanun shi yayi tareda yin shiru yarasa abunda yakeji a Ranshi,  a haka dai sukayi bacci har zuwa Karfe Tara na safe, Wanda Ahmed din ne yafara tashi domin ya matsu ya fita yaga halin da Naziya ke ciki. 

Saida yayi wanka ya tashi Khaleel “get up sleeping beauty muje muga momy inaso in duba Naziya Yafada yana goge fuskar shi da towel, tashi yayi yana salati tareda wucewa batareda ya furta komai ba, 

Saida yayi wanka ya fito, yasamu har Ahmed ya shirya sai kyalkyale jikin shi yakeyi domin so yake ya burgeta, Idan ta ganshi tasan bata zabi mijin banza ba. Shiryawa yayi shima khaleel cikin shigar tashi ta fama, kallon shi Ahmed yayi “yakamata kasa manyan Kaya zamuje gidan malam later gaisuwa tareda godiya inaso muje tare dakai. “no please banason zuwa wannan unguwar Yaya.”For me please. “OK for you. Amma bazan sa kayan zafi ba sai zamu tafi. “No problem muje”. 

Naziya saida mai aiki ta tasheta ta tashi cikin sauri ta bude kofar tace “Hajiya tace kifito kitayamu aikin breakfast. Tace tom tareda gyara zaman hijabin ta ta fito, tareda taimakon mai aikin suka shirya irin Abincin da sukeci wainda idan aka barta bazata iya ko kunna gas din ba bare sauran kayan wutar. Wurin gasa crabs din khaleel ne tasha mamaki,  domin ita tsawon Rayuwar ta bata taba ganin ta ido da idoba sai a text book, da kuma manyan d’anyun crayfish da Sam basuda kyan gani a idonta tana kallo aka gasa su a oven aka yanka mai salad da kuma tumatur manya aka jera su crayfish din da crabs din akan ganyen, so takeyi taga wazaici wannan Abun, sai kwai da ko kadashi ba ayiba ansaka mishi kayan kashe k’arni, kawai fasashi akayi a frying pan aka d’an barbada chilli powder asama kadan. 

Tana gefe tana kallon ikon Allah sai d’an abinda zata iya yi kawai take tabawa kamar fere dankali da yanka kayan miyan da za’ayi source dasu,  Karfe Tara da Rabi suka shirya komai a dining table, dai dai lokacin momy ta fito cikin shigar Alfarma da gwala gwalai, ta kalleta cikin fada, ” Ina fatan bada wainna kayan kika shiga kitchen ba?  Kanta tayi Saurin dukarwa tareda gaida momyn Ina kwana. Tace “mu nan wanka akeyi sau goma in antashi domin akwai ruwa basai anje tuka tuka ba ko rijiya ba don haka karki kuma shigar min kitchen da datti, yanzu ma Allah yasa khaleel ya iya cin abincin nan kin shiga kina yimai kakkabi da wannan katon hijabi kamar wadda keda nakasa, ke Kodai wannan kyan naki a fuska ne rufa rufa akayiwa Dana a cikin hijabi?  Oya Cire shi yanzu ingani wallahi inkinada ko kuna guda dayane yau sai kunbiya mu sadakin mu. Tafada dai dai y’an kanzagin ta na fitowa tareda kuma su khaleel da suka sawo kai cikin falon. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button