AUREN GADO 1-END

AUREN GADO Page 1 to 10

Dariya Fauzy tayi tace “may be akwai inda keda illah Mommy, Tafada tana tafawa da Aunty zarah dake biyeda ita, “kwarai kuwa a Cire kar a cuci dana,. 

Cikin sauri ta Cire hijabin kanta bako d’an kwali sumarta mai tsananin tsawo da kyau kamar buzuwa na nade cikin sabon ribbon, gashine kwance har gaban goshin ta Wanda ke sanarda kai akwai sumar. Kayan jikinta kuwa atamface dai dai talaka wadda malam ya dunka mata tafitar biki akalla zatakai dubu goma, domin kawai ya fitarda Y’ar tashi ranar Aure ya dunka mata su kusan guda uku, 

Atamfar mai golden ce blue, dinkin nata nazamani mai kyau na Amare Riga da sket ya mata cif mai d’an shoki ta baya perfect figure dinta ya fito fiyeda tunanin masu sa idon dake wurin, duk sun gama yarda cewa Naziya mace ce kuma  kyakkyawa ajin farko ba kamar na Y’ar talaka ba. D’askarewa Ahmed yayi domin yau ne yasan ya tsinci dami akala, yau yake ganin wacece Naziya, wani irin yanayi yakeji, burin shi bai wuce ya ganshi daga shi sai itaba a kebe ya samu ya rage damuwa da wahalar da yasha kafin yasameta. 

Gefen Khaleel kuwa bazaka taba gano komai ba sai tsantsar bacin rai da bakin ciki Wanda yarasa dalilin shi, cikin zafin zuciya ya kalli fauzy ” you come and get lost from my house, angama biki ki koma gidan ubanki right now. Yafada cikin karaji da fitinar da ba Wanda yataba jin yayi irin ta. “Aunty zarah I thought Aure kikeyi kema kije gidanki mungode da zumunci we need privacy that’s enough. 

Fadan da yakeyi ba Wanda za a iya tsaya wa ayi musu dashi bane, mommy ma mamaki takeyi tareda kallon shi saida ya kuma cewa “I said get lost. Tace “khaleel ” cikin tsawa, “ka kiyaye ni ba inda zasuje, kuma don iskanci ka manta Zarah kanwa tace uwa daya uba daya, don’t forget your manners and Fauzy, karka manta she is your bride to be. “Momy tell them to stay within their limit, ita Aunty zarah ba girman mu tayi ba I can talk to her any how, and   Fauzy Auren ta kikeso inyi zan iya fasawa anytime idan naso, don haka before I change my mind leave”.  Yafada yana nuna mata hanya. 

“Innalillahi, ni Balkisu daga zuwan ki kinfara hada mana gida” Tafada tana nuna Naziya, lallai kuwa yarinya kintabo tsuliyar dodo, Ahmed kaga Abun da ka debo, yarinya mai farar kafa bad luck to our family. Wani irin zafi yakeji tareda kallon momy yana girgiza kai, “no mommy me tayi, Ina bin duk Abinda kikeso momy saboda ingama lafiya please na rokeki kibarmu mu koma gefen mu zamufi samun kwanciyar hankali. 

“Naga takaina ni Balkisu kaga ni ko yarinya ta shigo da mugun Asiri, toh wallahi kunyi kadan keda iyayen ki zan nu na muku ni Balkisu in kun kwana akan buzu ni akan dadduma nake kwana mu zuba, daga shigowar ki Dana yafara musu dani. “Momy please stop” this drama is enough. Khaleel yafada yana matsawa kusa da ita tareda riko Hannun ta Alamar lallashi domin yaga Alamar nuna fushin su b’ata Al amarin zai karayi, domin kwanciyar hankalin d’an uwan nashi yace “Fauzy kuzo muyi breakfast Aunty zarah please komai ya wuce OK. “Dama Ibrahim kai raini ne dakai tun kana yaro shiyasa Ahmed yafika Abun kirki. 

 “Oh am sorry my Aunty yafada yana Dariya kadan, zama sukayi, ita kuma ta wuce dakin da ta kwana tana share hawaye masu ciwo da dumi, domin all her life bata taba tsayawa gaban mutane ba hijabi ba, yau gashi an wulakanta ta saboda me?  Saboda tana Y’ar talaka, shiyasa batason tasa Rayuwar ta inda tafi karfin ta. 

Ahmed kokarin bin ta yakeyi mommy tace “zonan d’an anace shiryawa zatayi tafito kuma kiyi sauri don bazamu tsaya jiranki ba hamshakiya. Komawa yayi ya zauna tareda zubawa bayanta ido har ta shige, ga koshi ga kwanan yunwa shine wannan. 

Gudun fada yasa tayi wanka cikin sauri bayan ta gano inda zata Tara ruwan, domin ko bakomai tanajin labarai tareda gani a TV  sometimes duk da ita ba ma’abociyar kallo bace, bisaga Al’adar gidansu na riko da Addini tareda kaucewa duk wata Rayuwa ta nasara, sai gata a yau tana Rayuwa cikin nasara baki daya domin a ganin ta gidan baki daya ma  Rayuwar nasara sukeyi. 

Ganin bataga kayan taba yasa ta mayarda na jikin ta, tareda daura d’an kwalinta ko mai bata shafa ba ta fito cikin sauri. Suna zaune yanda ta barsu,  sai Ahmed da ya rike Haba yana kallon ta inda zata bullo, Ajiyar zuciya yayi ganin fitowar ta, yanzu ya samu damar karewa gabanta kallo da take tahowa toward him, Ajiyar zuciya ya jera tafi goma, domin shidai yana ganin samu da rashi ga mace Allah ya Bashi ta huce takaici Amma mommy taja layi,  “bazamuga tsiya ba mudai ki kwana da Kaya ki tashi dasu ki shiga kitchen kifito yanzu kuma kizo ki zauna cikin mu kina tsami, maza ki koma ki canja Kaya, Ahmed kaga illar Auren irin wannan yaran ko? yanzu da akwai bakon ido da munsha kunya. Shiru tayi takasa cewa komai. Cikin sauri Ahmed yace “mommy kayanta na part din mu ne shiyasa duk can aka kaisu, “oh kace kagama planing din tarewa acan to kaje ka kwaso mata kayan zuwa nan ban Amince maka zama da wannan ignorant din ba a cikin wannan gidan ba sai in kashirya yin wani Aure kwa tare da Amaryar Arziki ba wannan ba, Tafada tana nunata sama da kasa, da Alama kalaman mommy nayiwa khaleel zafi fiyema da Ahmed domin yasan d’an uwan nashi hakuri ne kawai yasa yakasa cewa komai shikuwa hakurin shi yafara karewa. “Mommy please am hungry ko intafi ne waje inci yau bazamuci breakfast din ba? “Kizo ki zubawa kowa yarona najin yunwa kinja kin tokare. Matsowa tayi jikin ta NA rawa,  ” gefen da Khaleel yake ta fara nufowa kanta akasa bata ma iya kallon idanun mutanen, infact haryanzu bazata iya tantance kamannin fuskokin su ba. Wani irin kamshin turaren wuta d’an mai duguri mai sanyin kamshi, Wanda ya Kama jikinta ya daki hancin shi, Hmmm yana matukar son kamshi a Rayuwar shi, ga wannan da yake shaka mai wani sirri na daban. 

Plate ta dauka ta fara zuba musu chips din dankali da source, Ahmed so yake ta kalleshi, just once ko zaiji sauki domin Allah kadai yasan Abinda ke cikin zukiyar shi, damuwar da yake ciki bata faduwa. 

 Saida ta zubawa kowa tazo kan Khaleel, ya daga mata hannu tareda janyo tarkacen shi gabsnshi domin shi cimar shi daban take a gidan, zuba mai ido tayi tana kallon shi zaici wannan Abun? “Naziya “. Ahmed ya Kira sunan ta cikin wani irin kashe murya tareda tsareta da idanu, batada choice dole tadaga idanun ta takalle shi, nuna mata kujerar gefen shi yayi tareda mata Alamar tazo ta zauna. Ba musu ta nufi gefen shi, mommy nata hararar ta kasa kasa, Su fauzy kuwa kallon village girl suke mata, zama tayi a takure da kanshi ya zuba mata Abincin tareda hada mata tea very thick, “toh shanyayye ita batada hannu ko?  Inji mommy shidai shiru yayi, saboda jin ta a zaune kawai a kusa dashi yaji ya d’an natsu kadan. 

Tsit kakeji  sai karan cokula, ganin hankalin kowa nakan plate ya sauke left hand dinshi tareda dafe Hannun ta daya dake Kan laps d’in ta, gam gam, wani irin zabura tayi, Wanda khaleel ne kawai idanun shi yagani, idanun ta a gefe take kallon Ahmed din tareda kokarin kwace wa ta kasa , wani irin bakon Al amari takeji domin zata iya cewa wannan ne karon farko da namiji ya rike mata hannu, gashi ba rikewar  kawai yayiba wani irin murzawa yakewa Hannun kamar kwadayin shi akan Hannun yake, 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button