AUREN GADO 1-END

AUREN GADO Page 41 to 50

Gaba daya ya manta da duk mutanen dake dakin likita kuwa Abun ya matukar burgeshi, don haka bai tafi ba, Saida momy tace “doctor ka sallame ni zanje gida inkarasa warkewa idan akwai Abinda za arika yimin zan rika zuwa checkup. 

“Tab bansan Wanda yafi wani doki ba keda khaleel Aunty. “Zarah gwara inkoma gidan tunda kinsan halin d’an naki kar yaje ya hana min ita sakewa yajamun Asara. “Tofa kaji likita. “Eh ba wani damuwa sai medication dinta kawai dama ba Abinda muke yimata shi irin wannan ciwon warkewar shi gaba daya dama sai a hankali. Amma Hajiya kiyi hakuri har zuwa karshen satin nan. “No likita discharge me. Juyowa khaleel yayi “no momy please kibari ki Kara samun sauki zan kula da ita karki damu. 

Shiru Tayi na d’an lokaci Saida likita ya fita tace “khaleel kana ganin zan kuma shiga Rayuwar ku ne domin inkara hanaku zaman lafiya? So nakeyi inkasance tareda Naziya nasan wahalar laulayi tunda tafara da Amai ga gida bakowa at least ina kusa hankalina zai kwanta. 

Gwanin tausayi Naziya ta sakko duk da batajin karfin jikin ta ta matso kusa da MOMY, ” momy ina nan tareda ke Sai kinji sauki ba inda zanje. “Aa Naziya gida Zaki koma ki kula da kanki kinji” nidai tare zamu tafi. Tafada tana marai raice wa kamar zatayi kuka. Fita kawai yayi yabi likitan yace ” doctor you have to discharge my momy kafin matata ta jamun Asara please, zaku iya hadamu da nurse da zata kulamin da ita kafin ta karasa warwarewa,and inaso ayi mana Ultrasound insan watan cikina da kwanakin shi da kuma lafiyar shi. ” that’s not a problem dama yakamata hakan, maganar nurse munada kwararru,madam ko yanzu zaka iya kawota muyi ultrasound din. 

Godiya yayi ya koma tareda cewa ” get ready Aunty Zarah zamu tafi gida baki daya bari muga doctor da Naziya, let go. Yafada tareda dagata suka fito yana makale da ita kamar gold takun ma ji yake kamar yayi mata shi, nan take akayi mata, cikinta kimanin sati bakwai zuwa takwas. 

Abu daya ke takura ta shine kamshin perfumes dinshi, is killing her dauriya kawai takeyi, koda suka shiga mota juyawa tayi gefen window ta danna domin iska ya rika shigowa, kokafin su isa gida duk ta bata jikinta da Amai, da kuma motar shi, sai sannu suke yimata duk ta galabaita, don haka suna isa daukar ta yayi MOMY kuwa wheel chair sabuwa Aunty Zarah ta taimaka mata ta turata zuwa gefen ta, da mai aikinta ta gyare fess, taji dadin ganin masu aikin su duk sundawo, gidanta yadawo dai dai, mai aikin tafara tanbaya ko Salifa na gidan? Tace koda tadawo basa nan batasan me yafaru ba. “Ai Aunty kinsan halin khaleel kila yayi musu Abinda ya dace, what ever dai tunda basa gidan Alhamdulillahi. 

Gefen Naziya kuwa daukar ta yayi ya kaita bathroom ya mata wanka tsab yana hadiyar yawu domin Allah yagani ya mugun yin kewar ta, dan komai yakara Masha Allah…. Yana mata wanka yana murzar ta duk ya rikice yana mata sannu, “please ka kaini dakin momy banason wannan pefurmse din naka, gaba daya gidan nan kamshin ka yakeyi zuciya ta na tashi I can’t stay here please kafitar dani kafin in Amayar da y’an hanji na….. ????

“Wnn Abu dai bamai sauki bane wurin khaleel akwai rigima kuwa, baruwana, but I understand ur situation Naziya ????

*Matar Soja*

6⃣3⃣&6⃣4⃣

……………. Tagumi yayi yana kallon y’an da take saurin zura kayan ta, kafin ma yayi wani Abu ta dauki hijabin ta da wayar ta tayi waje, “what is that? Yafada yana mikewa, ko kafin ya zura jallabiya ya bita harta kai sashin momy so take tayi nisa da kamshin jikin shi inba haka ba ta fara Amai kenan. Suna zaune a falon Aunty Zarah ta kawo matsa tea a cup tana bata Naziya ta shigo, kanta akasa ta koma gefen su akan doguwar kujera ta kwanta batareda tace komai ba, tsayawa sukayi suna kallon ta kafin zarah tace ” lafiya dai ko akwai matsala ne Naziya? ” Bakomai aunty kawai zan kwanta ne anan. “Keda nakeso ki huta shine kika fara yawo bazamu shirya ba inba zaki natsu wuri daya ba. Juyowa tayi kamar tayi kuka idanun ta rau rau tace ” momy bana son can ne wani irin kamshi yakeyi dake tadamun zuciya. “Ki fada musu kawai bakyason kamshin perfumes dina ne shiyasa kika gudo nan, ko kuma kinayi ne kawai saboda ki wahalar dani?  

Dariya Aunty Zarah tasa tareda cewa “eh akwai Kallo da bana komai da nan zan tare ba ruwana da tv, kai baby bakason kamshin dady tab. 

Dukar da kai momy tayi tana murmushi cikin wani irin farin ciki, kafin tace toh ka canja ka kumayi kokarin korar na cikin gidan da wani kamshin tunda bataso karta cutu. Kallon y’an da ta juya musu baya yayi ya kama baki yarasa me zaiyi, kafin ya mike ya fita gidan. 

Momy tace “Zarah Kira mai aiki ta bata Abinci, me zakici Naziya? Tace shrimps takeso soyayye da miyar source. 

Aunty Zarah ta kyalkyale da dariya ” barewa tayi gudu d’an ta yayi rarrafe? Lallai wannan d’an tun baizo duniya ba ya gado tsoho. ” inkin gama yiwa surukar taki iya shege ki wuce ki hada mata kinsan mai aiki bazata iya yin yanda zaiyi mata dadi ba, da kafafun na motsi da da kaina zanyi mata. “Bari inje tom. Tafada tana dariya, abun ita kanta ya mugun burgeta y’an da Y’ar uwarta ta dawo kan hanya, dama ita tuni ta tuba bata taba Y’ar da taje wurin wani malami kota aiketa dafe kudin takeyi don tasan intace bazata jeba zasu samu matsala kamar sauran y’an uwan dake fada mata gaskiya. 

Don haka ta natsu ta hado mata Abinda takeso, lokacin bacci yafara daukar ta. Momy tace “tashi kici Abinci ina kula dake ba wani Abinci kikeci ba ko a Asibiti. Tashi tayi ta zauna akasa, har wani irin tsinkewa miyanta yakeyi saboda ganin abun da take marmarin ci. 

Tafara ci kenan ya shigo da kwali kato, suka zuba mai ido har ya Ajiye tareda kallon y’an da take cin Abincin ta ko dago kai batayi tana wani irin lumshe idanun ta, ya jingina jikin kujera, Abun na matukar burgeshi, Saida ta cinye tas tasha ruwa kafin ta mike ta kai plate din kitchen. Dawowa tayi tana Ajiyar zuciya domin taji ta dam yanzu. “Momy ga shi na sayo Kala Kala ta zaba Wanda takeso inrika Amfani dashi. Yafada yana baje tirarukan masu shegen kamshi da tsada Sunkai kwalba Ashirin,

Ai kuwa da gudu ta tashi tunbai bude ba tayi dakin Ahmed dake part din tana fitar da numfashi dakyar ta samu zuciyar ta ta kwanta. 

Binta sukayi da Kallo shima ya ce ” what again momy? Aunty Zarah ta ce “kagane kamshin ne kawai bataso saika daga mata kafa har zuwa lokacin da komai zai dawo dai dai. “Till when please, nidai gaskiya da sake haba. Ya mike zai bita momy tace “dawo nan karka sata Asarar Abincin da taci yanzu yarinyar nan Ina lura da ita ba wani Abun kirki takeci ba, Amma baka damu ba, duk damuwar ka kawai ka takurata ka hanata sakat, idan ka shiga wurinta ranka zai baci.

Fita gidan yayi cikin fushi, ita kuwa samun gado tayi taci baccin ta hankali kwance. 

 haka y’an dubiya keta zuwa gidan suna duba momy y’an uwan ta kusan kullum suna gidan, yanzu ba wani hayaniya ko fada tsakanin ta dasu sai zumunci, haka kawu modu yanzu shima da iyalin shi suna yawan zuwa gidan domin kowa yasan Hajiya balkisu ta canja sosai, zumunci takeyi da gidan malam da Inna, sometimes in suna zaune da Naziya zatace “idan naji sauki kafafuna suka samu zan je har gidan inyi godiya inajin dadin Addu’oin da yake aiko min a jikina, Allah dai yasa agama lafiya. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button