AUREN JINYA Complete Hausa NovelHAUSA NOVEL

AUREN JINYA Complete Hausa Novel

*_BISMILLAHIR~RAHMANIR~RAHIM_*

Page:01

 

 

Auren jinya, auren jinya ubangiji ya tsarini da yin auren jinya, duk wanna kyawo nawa da komi nawa, na taso gidan talauci sannan na Kare kan yin auren jinya,

Ihu da sowa dukan yan matan da samarin sunka duka, wani saurayi Dan baki ya dura da cewa shigiya nana.

Samari ne da yam mata ke zaune cikin wata inuwa , a cikin wata makaranta, waton sokoto poly. Babu abinda sukeyi sai firar duniya.

 

Wadda akan kira da Suna Nana, kallo daya zaka yimata kasan cewa kyakyawa ce a cikin kyawawa, Sannan ga tsantsan wayewa ta yan Matan zamani, ko a fanni suturarta zaka san cewa tana cikin zamani kuma duniya ta aure ta.

 

Haba haba AI yanzu mata sunyi wayo Sun daina auren jinya, ina laifi ka samu wanda ya kama karatunsa ya fara aiki ko kasuwanci kudi na shigowa ta ko ina sai kuyi auren babu wata wahala, shan dadi kawai zaku rigayi.’

 

Kisa duk kalar supar da kikeson, ki Saka kalar less dinda ke ke so, ki hau babba mota, ki zagi duk ubanda kike so ba Mai Yimiki magana.

 

amma inah ni , ina wani auren jiya kullum cikin fargabar abin yin lalura da abinda mutum zai ci, Kai auren jinya baiyiba.

 

Dariya dukansu suka saka, sunka ci gaba da saurarin hadisan nana na yam mata su daina yin auren jinya, wanda zuwa yanzu duk wata kawa ko aboki yasan karatun nana.

Wani saurayi Na gani zaune kusa da majalisar su nana tun farkon Zamansu , Sai dai ga dukan alama saurayin bako ne kuma baya cikin yan zaman majalisar.

 

Amma dukan firarsu bisa kunninsa suke, iya tunaninsa ya rasa wani irin aure ne, ake kira da auren jinya, haka kawai zurciyarsa ta kwadaita masa son kullah wata alaka da nana domin jin maanar auren jinya.

Sai dai yana ganin ba karamar wahala zai sha kafin yama nana ta saurareshi saboda ya riga da ya hango inba ‘yayan banki ga rika ba to bakada wani mutumci a idon nana, kuma shikam baida ko asi.

 

Can yaji nana ta ci gaba da biyan karatun ta, kee sani zainab nifa ko tsoho na samu indai ba auren jinya zanyi ba to banda matsala, sake bugewa sunkayi da dariya Wanda akan kira zainab ta ce to aiki yaro ba kudi shine tsoho, tsoho da kudi ai yaro ne, shegiya zainab dadina da ke kinsan kan abin, cewar nana.

 

 

nifa iya kata da saurayi indai naga yanada dan wani abu in yazo yana sona zan ce ina sonsa amma fa cikin zurciyata ba da Gaskiya nakeyi ba, kawai zan wanki gara, amma aure kam sai mai kudi, cewar zainab.

 

Kokam Allah ya shiyarku cewar wata budurwa kyaukyawa ta karshe mai kalar indiyawa amma kallo daya Zaka yimata kasan bafillatana ce, saboda Tsananin kyawonta idan ka kallah sau daya gabanka ya fade domin zaka yi tunanin gamu kayi.’

 

Don Allah rufamuna baki cewar nana, ta katse budurwar mai suna meenatu , Ai gara mu da muna fadi raayinmu amma ke saboda tsabar munafucci Duk wanda Yazo korarsa kikeyi sannan in anyi magana kice muji Tsoron Allah da ke muke jin tsoro.

 

Meenatu murmushi tayi saida fararin hakoranta sunka baiyana ta ce kome dai zaki ce ke ce, banga Wanda yayimin ba ne IN nasamu zanyi Auren insha Allahu.

 

Nifa nana nafi son saurayi bisa ga babban mutum, koda ko baida ko sisi muddin dai yanada ilmi da yar Sana’a yadda cikin rufin asiri zai duke dawainiyar iyalinsa, shifa arziki da samu duka suna wajin Allah kuma sai ya so zai baiwa wanda ya ga dama alokacinda ya so.

Nidai tashi Muje gida cewar meenatu ko dai yanzu mun dan huta.

 

Hakane kawata wlh yau garin ana balain zafi cewar nana, sallama sunkawa sauran abokanin karatunsu da kuma firarsu…
[07/10/2018, 00:28] 80k: ????‍❤‍????AUREN JINYA????

 

ZAMANI WRITERS ASSOCITION

RUBUTAWA????????

AMA ALHAJI KABIR

DA

HUSSAINI 80k

 

LABARI:
AMA ALHAJI KABIR

SADAUKARWA ZUWA GA SAMARI DA ‘YAM MATA.

 

KIRKIRARREN LABARI NE.

 

Allahumma laa sahala illamaja’altahu sahala wa’anta Taj’anil haxna ixa shi’ita sahala.

Page :02

Sunatafe nana sai faman zuba taketayi tana wani rawarkai sukatare mai adaidata sahu inazakuje malama sai meenatu tace malam arkillah zaka kaimu.

Ita ko nana sai wani shan kamshi takeyi wai ita yam mata sai meenatu tace ki nedai mutafi dan allah kinata yin abu kamar wata zautarciya.

Suka kama hanya sunatafe suna fira amma fa ita nana hankalinta nawani gun harsuka isa batamasan Sun iso gidaba sai da meenatu ta dukita ki malama fita munzufa amma kina can kina wani tunaninki na banza.

Nana ta Kalli meenatu tace Allah kincika zakiwa dayawa amma da sannu zakigane me nake nufi hmmm inji meenatu tace ke nidai jeki Allah ya shiryeki yasa ki gane.

Tasauka daga adaidaitar tanufi kofar gida tace to sai mun hadu gobe meenatu tace toh Allah yakaimu tanufi cikin gida tashiga tana wani rangaji wai ta gaji salamu alaikum mama nadawu.

Toh nana ya naganki haka wallah mama nagaji dayawa wallahi mama tai murmushi taci nanan mama to ai karatu dama wahalane dashi amma idan ka dagi sai kaji dadi nana dai shuru tayi kawai .

Mama yau mi akayi agidannan mama ta kalli nana tace shin kafa dawaki kai mama kullon shinkafa dawaki kamar wasu bayi nifa sai mama tace kifa mi to to haba dai.

Mama tace to nidai ita mukasamu inzakici kici samuma ki kayi wallahi wasu nacan suna bida basu samu koda fara damaine ki kinsamu harda waki kin raina.

Nana tace hmmm ta tunzire baki ta nufi daki tana tafe tana gunguni wai kai baranar dazaka samu irin abinda kakisoba.

Ahaka aki kirama kayi auren jinya hm bani ba auren jinya wallahi sai inda zanje nahuta wani nawa yahuta amma nazauna naci maida yaji agidanmu kuma naci agidan miji kai ina wallahi dasaki.

Mama tace waiki nana kidawa ki magana tun dazu ashi mama najina to bakowa karatu nakiyi mama tace to dama wanki wankinnanne nakiso kiyimun nana tace kajiba.

Wai wani wanki wanki Zanyi badai zaabarka kahutaba to indai nayi nanne idan ma banyiba nanne saboda dule in aure mai gari ahannu kumai ma sai dai ayimin .

Tafito daga daki mama gani mama tace ga su acan tana tafiya sai ga kira yashigo wayarta taduba sai tace waki kirana tana shirin dagawa sai waya ta dauki .

Tayi wani irin tuma har saida mama taji tsoru tace nana lafiya miyasameki budar bakin nana wai wayatace tamutu haba akuda yaushe haka wayarnan kimun nace mama ki gayawa abba ya canzamin kinki nifa nagaji da rukon wannan wayar.

Haba duk abukainena suna da wayarsu mai dama amma saini ni nagaji mama tace kingaji toh wai ki nana mi kika dau duniyane duniya da ki kigani wallahi batada tabbas.

kibi duniya ahankali kibandama rashin tunani irin naki kuwannan rufin asirin da Allah yaimana bakiganinsa sai Sun kidai ki burge.

bama neman kumi agonwani amma ki kuda yaushi baki gani to nidai adduace atsakanina daki allah yasa kigane.

Nasan Mai karatu zai so Sanin waye meenatu da Nana?

Meenatu yarinyar ce budurwa yar kemanin shikara goma sha takwas da haihuwa , tana zaune ne tare da mamanta wadda iya tashinta so kadai tasan suna rayuwa, cikin gidansu.

Baza a kira mahaifiyar meenatu da mai kudi ba haka kuma baza’a kirata da talakka ba gargadon mahaifiyar meenatu nada rufin asiri dai dai gar gado.

Kuma babu abinda sunka nema sunka rasa , meenatu ta dadi da sanin matsalar da ke tsakanin mahaifiyar ta da mahaifinta Wanda matsalar tasa meenatu tsanar maza.

Meenatu yarinya ce mara son yawan magana sannan ta cika sanya wani lokaci, amma fa tana da zafi so sai in ka kaita karshe.

1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button