AUREN JINYA Complete Hausa Novel

Kai tsayi zamu iya kiranta miskila sannan meenatu nada tsananin jin tausai da dukar abin duniya ba bakin komi ba.
Hausawa na cewa in kaga ana kawance sai in hali ya xo daya, to a wajin meenatu da nana ba haka bane.
Nana yarinya ce warin meenatu tanada balain son kudi da dogun buri sannan tanada zafi so sai dumin bata dukar raini a wajin kowa.
Sannan bata iya boye abinda ke ranta shiyasa mutane da yawa ke ganin rashin tarbiyar Nana.
Gidansu baida nisa ita da meenatu sannan amintaka ce mai karfi tsakanin meenatu da nana, Sun cika saurin yin fada sannan basu minti biyu basu shiryaba.
Nana mahaifinta ma’aikacin gwamnati ne yanada rufin asirinsa so sai kuma yana iya kokarinsa wajin sauke dauyin iyalinsa, sai dai nana bata ganin wannan tarin baiwa da ubangiji yayimusu, kullum ganin takeyi mahaifinta talakka ne.
Ta duke dogon buri tasama ranta ita a dole sai mai kudi zata aura dumin debi takaicin talauci.
Ama Alhaji kabir
Hussein 80k????????
[08/10/2018, 02:34] 80k: ???????? *AUREN JINYA*????????
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION.*
Rubutawa
____________
*AMAH ALHAJI KABIR*
*DA*
*HUSSAIN 80K*
LABARI:
__________
*AMA ALHAJI KABIR*
SADAUKARWA
__________________
*GA SAMARI DA ‘YAM MATA.*
KIRKIRARREN LABARI NE.
Page3
Taba ka lasa, yaro ne Matashi Mai jin she wani ne saka makun tsabar baiwar da Allah yayi masa da kyau, sannan gargado yanada dan kudinsa. Amma fa karyarda a azama ma kansa tayi yawa domin in munyi laakari da yadda yake kashe kudi zakayi mamakin ina yake samunsu, Amma da sannu mai karatu zai fahimta .
Faisal a ainihin sunan sa abukaninsa da yam matanda yake hudda da su ne sunka saka mishi wannan suna taba ka lasa, domin Allah ya aza mishi jarabar son mata kuma duk budurwar da ya kyalla ido ya gani, ya ji tayimasa zai yi iya yinsa yaga ya samita ya biya bukatarsa, Sai yayi gaba.
Yau ma kamar kullum nana ce tare da meenatu hanyarsu ta zuwa kasuwa siyayya, Sai kuma akayi rashin Sa’a ana zananin zafin rana, kuma ga rashin abin hawa.
Sunfi minti talatin suna jiran abin hawa, meenatu ta kalli nana ta ce ina ganin fa nana yau bamu fito a sa’a ba, kalli tun dazu muke jiran abin hawa mun kasa samu.
Wai ko hakura zamuyi da xuwan kasuwar cewar meenatu tana kallon Nana.
Haba meenatu ke na ganin tafiyar zata fasu duk wahalarda munka sha, gaskiya mu dai kara jira Inji Nana.
Shikenan ai mai rabon shan duka baya ji sai yasha in ji meenatu.
Wata mota sun kaga tayi faking kusa dasu, wani saurayi mai matukar kyawa sun ka gani, cikin muryarsa da ya saba yudara yam mata, yayi musu sallama.
Nana ce ta amsa cikin yanga da jin aji domin kallo daya tayi masa ta ga tasamu irin mijin da take mafalkin samu , domin ko baa fadamata ba tasan mai kudi ne ko dan mai kydi, uwa uba kuma yaro matashi mai kyau.
Koda ita a rayuwarta bada damu da ko ya mutum ya ke ba muddin yana da yayan banki, lokaci guda tana rokon Allah yasa ba dan meenatu ya tsaya ba, domin some times hakan yasha faruwa sai ta san ranta da mutun karshe ya ce meenatu yake so.
Ita ko meenatu tayi masa korai kare ayi biyu babu bata dashi meenatu batadashi.
Yam mata adon gari ina zuwa cikin wannan rana ya fada yana kallon meenatu Wanda ita ko samma hankalinta bayama kansa.
Yam mata ina magana cewar saurayin yana kokarin jawo hankalin meenatu gunsa.
Malam kurma ce cewar nana domin samun mafita da cikar burinta, ikon Allah saurayin ya fada cike da jimami, sannan ya meda kallonsa izowa ga nana yana cewa yam mata ina kunka nufa in ajeku domin ni ban cika son ganin kyawawa nasha rana ba.
Cikin dan basarwa nana ta ce kasuwa zamuje motar mu ce tasamu matsala.
Salin halin nana da meenatu tayi baisa ta mamaki ba asali ma cigaba tayi da kallon abibin hawa da ke wu cewa, amma cikin ranta tana mamakin Irin halin nana.
Domin yau in tayi tsammaninta nan gobe zata wuce sanin ta, shiyasa bata da tabbas ga nana, abinda kawai tasani nana na mugun sonta sannan abin Nana nata ne.
Taba taji nana tayi alamun maganar kurami tana nuna mata da ta shiga mota, ba karamin dariya abin ya bata ba yadda nana ta meda ta kurma lokaci guda.
Ama Alhaji kabir
Hussein 80k????????
[08/10/2018, 15:42] 80k: ???????? *AUREN JINYA*????????
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION.*
Rubutawa
____________
*AMAH ALHAJI KABIR*
*DA*
*HUSSAIN 80K*
LABARI:
__________
*AMA ALHAJI KABIR*
SADAUKARWA
__________________
*GA SAMARI DA ‘YAM MATA.*
KIRKIRARREN LABARI NE.
Page4
Ba’a karamin dariya nana, ta bata ba na medata kurma da tayi lokaci guda, ko daya ke inda sabo ya ci ta saba da halin nana.
Sanin halin nana da meenatu tayi shiyasa ta shiga motar ba tare da tsawa gardama ba, Amma kallo daya zaka yimata kasan baa son ranta ta shigaba, Wanda har saurayin sai da ya fahimta .
Yam mata ina munka nufa ya kuma ce fama nana tambayar, kasuwa babba, nana ta bashi amsa a takaice, Dan murmushi yayi irin naso na yan duniya, ya dan sake kallo meenatu da ke bayan mota shidai haka Kawai yarinyar ta burgishi, kuma hakikanin gaskiya Don ta ya tsaya, Sai akayi rashin sa ‘a ita den kurma ce.
Yam ta Don Allah in babu damuwa yaya sunanki, Dan murmushi tayi sannan ta ce bakayi sauri ba ko? Domin sunana fa nada matukar tsada.
Haba haba aiko nafi kowa sanin irinku yam mata masu matukar kyau zakuyi tsada, Amma Kada ke damu ko nawa ne zan iya saya.
Amma dai da farko ni yakamata na fara fada miki sunana, sunana faisal Ahmad, Don Allah ke gayamin sunanki .
Nana sunana kawata ko meenatu, Allah sarki sunan duka naku nada dadi .
Kana saurayin ya kira sunanta niko na tambayiki Don Allah? Bai Jira amsarta ba ya dura tambayar wai meenatu haka anka haifita da lalurar ko kuma daga baya abin ya Samita .
Kai tsaye ta bashi amsa da haka anka haifita, ikon Allah cewar faisal, naso ace daga bayane gaskiya da nawa wani abukina magana lilkita ne, nasan zai taimaka mata.
AI ba komi ko yanzu mungode cewar Nana, dai dai da sun ka kawo bakin kasuwar, ya samu wajin faking ya tsayarda motar .
Yasa hannunsa aljihu ya zago kudi Wanda baisan ko nawa ne ba ya mekama nana, ya ce to gimbiya nana ga shi ku sai Sweet.
Karba tayi tare da godiya, nana ya kera sunanta cikin sanyi murya Don Allah ke taimakamin da number wayarki, karanta masa tayi shikuma ya na rubutawa.
Tau gimbiyatah ki gaida gida sai kinji kira ya ce bayan ya tayarda mota.
Yana wuce Nana ta rika hannun meenatu tana dariya tau kawata yar uwata kulma zo muje, bige hannunta meenatu tayi tare da cewa don Allah malama sakemin Hannu nah je zuwa neman kurma wlh.
Haba kawata sanin halinki ne fa yasa na cemasa ke kurma ce, domin nasan zaki batamin shiri, kalli Don Allah kudinda ya bamu, gaskiya mai kudi yaji dadinsa.
Tsaki meenatu nana bakisan rashin adarcin maza ba ne, shifa namiji ba mai kudi ba tallaka wajin rashin mutumci sai IN basu samu dama ba.
Shiyasa kin ga namiji wlh baya gabana, zasu zo da dadin baki suyita lallabaki kamar kwai, da Kin shiga hannunsu babu abin walakan tawa sai ke.
Inji wa cewar nana kedai wlh meenatu ke tsani maza da yawa kuma fa kinsan babu yadda zakiyi rayuwa ta jin dadi ba da da namiji ba.
Inji uban wa cewar meenatu Cikin hasala , mummy da ke rayuwa bada namiji ba ta mutu ne, ko kuma ta kasa daukar nauyin Kanta da nawa.