AUREN JINYA Complete Hausa NovelHAUSA NOVEL

AUREN JINYA Complete Hausa Novel

 

haba meenatu nifa bashi nake nufiba ke fahimcini ta fada cikin sigga lalleshi, kala meenatu bata kuma cema nana ba duk maganar da take mata.

 

Wanda nana ta riga da tasan halin meenatu da ranta ya bace bata da kai bata koma yima magana.

 

Haka sunka shiga kasuwa sunkayi siyaryarsu, nana kadai kewa meenatu magana in taga Abinda zasu saya.

Zata ce meenatu duba abinnan yayi, kyala meenatu bata ce ma nana, Dama kuma nana Tasan kwanan zan cen.

 

Haka nana suka gama siyayyar sun ka fito kasuwar jiran abin hawa.

Wlh idan mutum ya kuma medani kurma sai munyi bala’i da masifa, cewar meenatu.

lokaci guda nana ta bushe da dariya, dumin maganar ta zo mata ba zata , dariya takeyi kamar ranta zai fita.

Ita ma meenatu abin ya bata dariyar , dariya ita ma ta suma amma ba irin ta nana ba dumin meenatu ba gwanar dariya ba ce.

 

Tab wlh meenatu da ubangiji yayiki kurma da anga muguwar kurma, cewar nana tana Dariya.

Sai Kuma gashi Allah baiyini kurman ba , yadda kikeji haka nake ji sai yaya.

Dariya Nana tayi tace sai kuma meenatu ta zama yar uwar nana kuma kawarta wadda batada kamarta aduniya.

Hakane fa nana cewar meenatu, nana ta meenatu, meenatu ta fada cikin siffar zulaya.

Basu bata lokaci ba Iran dazu wajan samun abin hawa, Dan adaidaita suka samu sai kufar gidansu meenatu ya ajisu.

 

Ama Alhaji kabir
Hussein 80k????????

[23/01, 19:32] 80k: ???????? *AUREN JINYA*????????

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION.*

 

Rubutawa
____________
*AMAH ALHAJI KABIR*
*DA*
*HUSSAIN 80K*

 

LABARI:
__________
*AMA ALHAJI KABIR*

 

 

SADAUKARWA
__________________
*GA SAMARI DA ‘YAM MATA.*

 

KIRKIRARREN LABARI NE.

Page5

 

Kasan cewar mummy meenatu ma aikaciyar gwannati ce , Time den da suka iso gida, tana wajan aiki.

 

Dakin meenatu suka baje kayan da suka sayo, nan nana ta kama fitar wa meenatu nata, komi iri daya ne ita meenatu.

Anko ne na wata kawarsu zatayi aure, sai sarka da yan kunne da abin hannu sai takalma da jaka da mayafi, duka kalar da zata yima ankon dai dai.

Kayan ba karamin burge meenatu sunkayi ba, ta kalli nana gaskiya kayan sunyi kyau, idan Kin batama mutum kisan yanda zaki faranta mishi.

Dariya nana tayi tace, ai kedin ce meenatu sai da zafi wallahi, Amma kafin ke yabamin ke Fara us bawa mummy itada da ta bada kudin siyayyar.

Zaki fara ko nana kesan mummy ta sha fadamiki duk abinda tayimin zata iya yimiki domin kema ‘ya ce a wajanta.

Hakane meenatu kuma na tabbata domin duk abinda uwa kewa diyarta mummy nayimin, Fatana Allah ya bani abin sakamata.

Yanzu dai ga kudinda faisal ya bamu , bare muraba na dauki nawa na baki naki yar kurma, cewar nana cikin zulayar meenatu.

Harara meenatu ta aikama nana kisan wallahi zan rusa duk wani shirinki in kinka Kuma kirana da kurma.

Kuma maganar kudin ki barsu kinfi kowa sanin banda abinda zanyi da kudin, lokaci guda annurin fuskar nana ya gushe ta kalli meenatu ido cikin ido me kike nufi meenatu.

Allah dolenki ke duki naki kaso ko ai kati kena sawa, ita ma meenatu kallon Nana ta keyi, kisan fa mummy kesakamin kati kebar kudin kawai nana, nifa da asun ran na ne dama baki amshi wannan kudin ba.

Nasani meenatu shiyasa ma na rufe bakinki tun farko, kuma dolenki ki karbe naki rabon ko kuma wallahi muyita.

Murmushi meenatu tayi tare da dafa kafadar nana naji zan amsa, amma kije da kudin daga baya zan karba Kada mummy ta gansu sannan ko inbata labarin inda kika samesu.

Alamun tsoro ya baiyana a fuskar nana, domin duk tsiwarta tana tsoron mummy tare da mugun jin kunyar ta bata kaunar tayima mummy laifin da zata yima mata fada.

Meenatu kallo nana tayi tana dan murmushinta, alamun samun nasara rashin amsar kudin.

Ta shi muje na rakkaki tun kafin mummy ta dawo, ba musu nana ta meki tare da dukar ledar kayanda suka yi siyayya.

Suna tafiya suna dan taba firarsu har sunka kai wajanda yakamata meenatu ta koma gida.

Sallama sukawa juna, meenatu ta juya zuwa gida, nana ma tayi gidansu.

Faisal ko tunanin yadda zai ci nasara kan nana ya shiga yi, bayan ya koma gida, tabbas yasan ba wata wahala zai sha ba idan yayi la’ akari da yadda ta sake jiki dashi haduwar farko.

Kuma a hanginsa sai tayi sun kudi Dan haka ya ke ganin abu ne mai sauki cimma gurinsa..

 

Ama Alhaji kabir
Hussein 80k????????
[23/01, 19:32] 80k: ???????? *AUREN JINYA*????????

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION.*

 

Rubutawa
____________
*AMAH ALHAJI KABIR*
*DA*
*HUSSAIN 80K*

 

LABARI:
__________
*AMA ALHAJI KABIR*

 

 

SADAUKARWA
__________________
*GA SAMARI DA ‘YAM MATA.*

 

KIRKIRARREN LABARI NE.

Masoyan auren jinya, muna mai baku hakuri na rashin jinmu kwana biyu, da Bakuyi ba , rashin lafiya ce ta sa haka, Amma insha alluhu komi zai daidaita zaku ci gaba da jinmu.

 

 

Page6

 

Wayarsa ya jawo ya diling numbar nana da yayi seven, kirrrr kirrr yaji kiran ya shiga , Amma ga mamkinsa har wayar ta katse baa duka ba.

Sake kiran yayi cikin sa’a lokacin nana ta fito daga wanka sai ta dauki wayar, tare dayin sallama gimbiya nana barka da maraice cewar faisal.

Ranka ya dade ya yau ya kuma gajiyar dauwainiyar mu cewar nana.

Haba wace dawainiya gimbiyar mata, dama ina son rokon wata alfarma ce a gariki? Ke bani adress den ki na kawo miki ziyara har gida, da fatar zan samu wanna arxikin?

Murmusawa tayi kamar yana ganinta sannan tace haba faisal ai ka wuce wannan guna bare kawai in mun gama wayar zan turuma yanzu.

Godiya ya fara yimata kamar Wanda ta wa wani kyauta.
Kasan Cewar ya San kan mata ya dade yana mu’amala dasu Cikin minti biyu ya ja nana da dan fira, tanan yake tambayarta kawarta kurma, ta ce masa yanzo ma sunka rabu, daga karshe sunkayi sallama.

 

Cikin mintuna biyu nana ta turamasa adress den ta, tare da Dan neman guri aranta, na in yashigo hannunta yadda Zara rika yankansa.

Ameer tun ranar da yaga meenatu yaji ta kwanta mishi a rai, sai dai yana jin tsoron kada ta kasan ce halinta daya da nana.

Amma duk da Haka Zai jaraba sa’arshi ko Allah zaisa ya dace.

Wanka yayi yasamu kayansa masu yar dama ya saka , haka ma ta gifin takalma suma masu dama ya nema ya saka.

Bai wata shan wahala ba wajin gane gidansu meenatu domin ranar farko da ya gansu a skull ya biyo su domin sanin gidan.

Yana xuwa bakin Gidan zurciyarsa ta soma harbawa, karon farko kenan a rayuwar ameer zuwa gidan budurwa da sunan zuwa nemanta.

Cikin sa ‘a ya sami wata yar majalisar samari kusan gidan, nan da nan wata shawara ta fadu mishi garansa, dole ya samu kusanci da daya daga cikin samarin.

Ne!sa da su ya samu ya zauna amma dukan firansu yana ji koma yana fahimtar kowa cikin yan majalisar, nan ne ya fahimci akwai mai wanki da goga cikin yan majalisar, kuma ya fahimci dan cin rani ne daga kauye, haya yakeyi.

Bai wani jimawa ba akazo karba wanki wajan mai wanki, shima cikin hikima yabi mai wankin daga baya domin yaga shagunsa.

Cikin sa’a shagon na Mai wankin baida nisa da gidan su meenatu.

Yana kallo mai wankin ya bude shagonsa ya ba masu karba wankin, kayansu , sallama yawa mai wankin tare da mekamishi hannu, cikin mutumci shema mai wankin ya mekama ameer hannu sunka gaisa .

Don Allah malam neman taimako nakeyi gunka cewar ameer, lokaci guda mai wankin ya meda dukan hankalinsa gun ameer.

Ina jinka malam Allah yasa inada ikon taimaka maka, cewar Mai wanki, shema ameer meda dukan hankalinsa yayi gun mai wanki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button