AUREN JINYA Complete Hausa Novel
Don Allah malam wajan zama nake nema na haya ne mutumin kauye ne nazo bida, kuma gashi cikin rashin sa’a ban san kowa ba garin.
Kallo tausayi mai wankin yayi masa, yace insha allahu ka samu masauki , Kai har aiki ma inajin ka samu idan har bai yima kadan ba, domin ina neman yaron da zai ringa taimakamin sai kuma gaka Allah ya kadumin.
Fuskar ameer ta nuna tsantsan farin cikinsa, godiya ya fara zubama mai wankin, sannan ya fadama mai wankin zaije ya doko kayansa wajanda ya fara sauka.
Ama Alhaji kabir
Hussein 80k????????
AUREN JINYA*????????
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION.*
Rubutawa
____________
*AMAH ALHAJI KABIR*
*DA*
*HUSSAIN 80K*
LABARI:
__________
*AMA ALHAJI KABIR*
SADAUKARWA
__________________
*GA SAMARI DA ‘YAM MATA.*
KIRKIRARREN LABARI NE.
*PAGE: 08*
” Hmm nidai har kullum ina nuna miki illar wasu mazan dan wlhy….”, kafin Meenatu ta k’arasa zancen ta tuni Nana ta katseta tana cewa” kinga ni ya isheni haka, nasan fa halinki sarai yanzu kin kama ma mutum wa’azin nan naki, bansan me maza suka miki ba”,
Murmushin tak’aici Meenatu tayi dan tana jin tak’aicin irin wannan hali na k’awarta,
” Naji to na kyaleki bazanyi miki wa’azi ba tunda bakison a fad’a miki gaskiya”, cewar Meenatu,
” Ba wai gaskiya ce banso ba, a,a gani nayi ina laifin Faisal dan Allah ya nuna yana sona kuma nima irin mazan da nakeso ne, to shikenan sai inyi rejecting tayin da yayi min, a,a wlhy ina son abina”,
” Ok to Allah ya kyauta ni kinga zan shige class zaki zo muje ko kuwa jiran masoyin naki zakiyi?,
” Tabb jeki kawai bazan shiga ba jiran Faisal d’ina nakeyi, kawai sai mun had’u”,
Meenatu wucewa tayi ba tare da ta sake cewa komai ba, a ranta cewa take Allah yasa ki gane gaskiya ki daina irin wannan halin, ace mutum ba kamun kai ko d’aya a matsayinki na mace mai daraja.
Umar bai bar skull din ba saida yaga shigar meenatu class sannan yaga fitar nana da faisal a mota, kaitsaye ogansa ya kira ya shaidamishi duk wani abu da yasashi nema ya hadu , ina zai ganshi ya bashi kayanda yasashi nema.
A wani gidansa na hutawa suka hadu , yayi bayan tun fituwar meenatu daga gida ita nana har kawo warsu skull har fitar nana skull den da shigar meenatu Class.
cikin kalilan lokaci ameer ya gama shirinsa ya badda kama kamar yarda ya saba, ya tasar unguwarsu meenatu.
Mashin ya samu ya kaishe bai ajishi ko ina ba sai bakin shagon mai wankin, cikin saa ya samu mai wanki, sallama yayiwa mai wankin, bayan ya amsa ya bashi ixinin shuguwa cikin shagon, ya nuna mishi inda zai aje kayansa, bayan ya aje Sannan mai wankin ya fadamishi sunansa garbati inda ya tambayi ameer sunansa, lokaci guda sunan tanko ya fadumishi arai batare da wata shawara ba ya furta tanko , shema garbati sai da sunan ameer ya bashi dariya, baisan sadda ya furta tanko shin? tanko mai kan cin bashi cewar garbati ya fada yana dariya, sannan ya kara da tanko da garbati a shagon wanki, shima dai ameer dariya sunan nasu ya bashi baisan lokacinda ya dara ba, nan take ya gane garbati mutum ne wanda ya cika Sun ba’a, da zulaya.
Nan ya dan kalli garbati shema cikin siffar xulaya ya ce kasan fa, tunda kai oga na ne bazan rika kiran sunanka ba , zan rika kiranka da oga garbati ko oga kawai.
Shema garbati kallo ameee yayi yace, ah ah tanko kada kesa in rika jina wani babba, don Allah kerani da sunana kawai garbati.
Cikin lokaci kankani ameer ya fara sanin halin garbati cikin ‘yar wannan firar da sukeyi, inda ya fahimci garbati mutumin kirki ne, sannan bai duke kansa bakin komi ba, lokaci guda, ameer yayi niyar taimaka mishi, domin ya fahimci garbati yana cikin irin mutanenda inda Allah yayi su masu kudi, tabbas al ‘umma zasu amfana da dukiyarsu.
Cikin lokaci kadan shagon garbati ya soma cika da samari , nan ameer ya fahimci nan ma wajen firar matasan anguwar ne, duk Wanda yaxo shagon fira ko amsar wanki ko kawo wanki sai garbati ya gabatarda ameer gunsa, inda yake cewa ga dan uwansa nan yaxo daga kauye, wannan abin da garbati keyi yasa ameer kara ganin kemarsa, a idonsa.
Duk firanda Sukeyi su Garbati iyakar ameer dan murmusawa kasan cewarsa mutum ne Wanda bai cika dariya ba da yawan surutu.
Tun lokacinda ya ga Time din tasowar yan poly tayi ya fara baza ido domin cikin bincikenda umar yayi masa ya nuna mishi tanan ne suke bi in zasu skull , kuma tanan suke bi in zasu dawo, karshe ma ba wata hanya ta fitarsu sai ta hanyar shagon garbati,
Baa fi minti ishirin ba sai ga meenatu cikin dan adaidata ya sauketa, cikin shigarta ta kamala kamar kullum.
Tun kafin ta fito a dai daitar ta biya mai motar kudinsa , ta gabansu ta biyo zata wuce ga mamakin ameer sai yaga garbati na kallonta yana dariya, tare da yimata barka da dawowa harda tambayarta mahaifiyarta, cikin mutunci sunka gaisa sannan ta wuce.
Cikin wa yanda ke zaune wani mutumin ya fara cigumin meenatu , yace ga yarinya dai dai aure amma ta kasa fidda mijin aure, duk yadda kuke mutumci da ita da kayimata maganar aure zata rufe ido ta cema mutumci.
Wani yace ai dakaga macce mai kyau dole sai tayi ruwan ido, ba mamaki wani mai mugun kudi take jira, wani kuma saurin katse su yayi , yace wlh banda meenatu domin kudin mutum baya gabanta itadai ta tsani maza, da dai kawarta ka ce da wannan kam kowa yasan mai kudi take jira.
Wani kuma cewa yayi ai da ganin kyawon wannan yarinyar kasan dole tabada aljannu, haka dai fira ta kasance har lokacinda kowa ya kama gabansa saboda kawowar magariba.
Sai alokacin faisal ya aje nana, tare da manyan ledodi, komi ya faru a idon ameer, abin ba karamin bashi haushi yayi ba, itama nana kamar meenatu saida ta gaisa da garbati sannan ta wuce .
Tare sunka je sallah magariba tare sunka dawo, alamun shiguwar sako yaji cikin yar karamar wayarsa ameer, saida sunka zauna sannan ya samu damar duba sakon, umar ne ya turumishi sako, kamar haka,
Sallama ranka ya dade, ya bakunta? gaskiya ranka yadade hankalina ya kasa kwanciya na zamanka wanna shagon, akwai hanyoyi da yawa na neman soyayyar meenatu basai kasa kanka wannan aiki ba.
Murmushi ameer yayi, sannan ya turamishi amsa kamar haka,
Wasallam kada kadamu nasan mi nakeyi , zan kira xuwa gobe idan da yuwuwar haka.
Ama Alhaji kabir
Hussein 80k????????
[23/01, 19:32] 80k: ???????? *AUREN JINYA*????????
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION.*
Rubutawa
____________
*AMAH ALHAJI KABIR*
*DA*
*HUSSAIN 80K*
LABARI:
__________
*AMA ALHAJI KABIR*
SADAUKARWA
__________________
*GA SAMARI DA ‘YAM MATA.*
KIRKIRARREN LABARI NE.
*Page:9*
Ameer bai san kalubale na gabansa ba , saida dare yayi wajan kwanciya bacci , wata ya mutsatsiyar katifa ce garbati ya bashi, she aganinsa ya bala’in karrama ameer, shiko ameer kallo daya yawa wajin kwanciyarsa, yaji gabansa ya balain faduwa, dumin duk acikin shirinsa bai kawo wajin kwanciya ba.
Amma cikin dakewa ya kwanta, sai dai mi? Yana kai bayansa samar katifar yaji dukan bayansa ya amsa, bai san lokacinda ya tashiba, kallon sa garbati yayi , kamar mai karantar wani abu game da ameer, sake kwantawa ameer yayi , cikin dauriya yayi addu ‘ar kwanciya, Sai dai bacci yaki xowa saboda rashin sabo na muhallin, rufe idanuwansa yayi kamar wadda yayi bacci, kusan mintuna goma ya fara jin ansarin garbati, alamun yayi nisa da baccinsa, abinka da Wanda yasha aiki so sai.