AUREN JINYA Complete Hausa NovelHAUSA NOVEL

AUREN JINYA Complete Hausa Novel

 

 

Sannu a hankali ya fidda wayarsa ya hau yanar gixo dumin yasan yau kam babu shi babu bacci, kusan kwana yayi yana danna wayarsa.

 

 

Ta gefin meenatu ko bakaramin dukar zafi tayi da nana ba, domin da safe batama jirata ba wajan zuwa skull , duk da rashin samun isashin bacci, ameer baiyi lattin tashi sallah ba, saida yayi awallah sannan ya tada garbati shema yayi awallah sunka je masallaci, ya dade yana addu’o’insa tare da karatun qur ‘ani Kamar yadda yasaba , haka yakara karama garbati ganin kemar ameer.

 

Suna dawowa shago garbati ya fidda kayanda zasu wanke, wasu irin kaya ne masu mugun yawa, nan da nan hankalin ameer ya tashi domin a tarihin rayuwarsa bai taba wanke komi nasa ba, yana kallo garbati ya hada komi na fara wankin, dole ya taso suka fara saidai abin dariya, yakasa koda dan wanka mayafi, domin rashin iyawa da rashin sabo, lokaci guda yaji hannunsa ya riki dole ya debe hannun, kallonsa garbati keyi, sannan ya kalli hannu har ya dan kumbura, kama hannun garbati yayi.

 

 

wani irin taushi yajiya kamar ya kama auduga, lokaci guda ya koma tsare ameer da kallon kulla yana son sanin wani abu game dashi, tabbas indai ka debe mugun kayanda ke jikin ameer da koma neman taimakon da yaxo to tabbas baka taba cemasa mabukaci ko talakka.

 

 

Sannu garbati ya cema ameer, kanada ciwon sanyi ne? Naga hannun kamar ya Kumbura, ameer samun kansa yayi da sharama garbati karya.

 

 

Eh inadashi oga, kuma bakadan yake wahalalda ni ba, dama dai ina Sun na fadama, domin ina ganin sana’ar ka bata yimin, don haka ka dai taimakamin da wajan zama in yaso ko wani abu na rika biya, garbati kallon ameer yayi cikin tausayawa, ya ce haba tanko da da baka xoba, ai nikadai nake biya, indai wajan kwanciyarka ne kada kadamu nayi niyar taimakama, don haka bazan fasaba, kuma ina rukun Allah yabaka lafiya , sannan Allah yabaka sana’a da zaka taimaki kanka.

 

 

Suna cikin tautaunawa meenatu ta fito da shirinta na zuwa skull, kamar jiya yauma cikin shigarta ta mutumci take ba wata duguwar kwalliya, tunda ta fito ameer yasama ta ido ga mamakinsa sai yaga kaitsaye tayo wajan garbati, cikin mutumci garbati ya soma gaishita, tare da yar zulayarta, hajiya karama yau kuma ina aminiyarki cewar garbati, sai da ta bata fuska sannan ta ce yau ba hanyarmu daya ba, dama mummy ta ce kaje ka amso wanki ya taru .

 

Yanxu ko hajiya karama domin baa wasa da aikin hajiya babba cewar garbati yana nufin mummynta.

 

Shi dai ameer ga badai idonsa na kan meenatu, wata irin kaunarta ya keji da sonta, natsuwarta da kamun kanta yana daya daga cikin abinda yasa tun ganin farko da yayimata yaji ta burgishi.

 

 

Ita ko meenatu gabadai ameer ko kallon banxa bai ishita ba, duk irin Kallonda yake binta dashi batama kulaba.

 

 

A Class suka hadu da nana duk yadda nana taso meenatu ta saurateta abin ya gagara, domin ba karamin daukar zafi tayi da nana ba.

 

 

Ita ko nana gaba dai jin tayi duniya tayi mata zafi hushinda meenatu keyi da ita, domin tare suka taso kumi tare sukeyi sai dai banbancin hali amma duk da haka baisa suka sami matsala.

 

 

Bayan antashi daga lakcar meenatu yau Ko yar firarda take tsayawa cikin abukaninsu bata tsayaba domin bata son saurin nunama Nana zata sauko cikin sauki.

 

Ita ko nana jin kanta takeyi kamar mara lafiya duk nacin Faisal na son ya kuma zuwa skull ya ganta taki barinsa.

 

 

Kamar dai yadda zuwa skull ya kasance da safiya haka , kuma ta kasance ta fannin nana da meenatu.

 

 

Shi ko ameer meenatu na wucewa da safiyar ya shaidama garbati zai Dan shiga gari neman aiki koda gadi ne ko deribanci domin ya taba diriba gidan wani mai kudi a kauyensu, haka dai ya tsara garbati ya shiga gari, tun kafin ya bar shagon ya turama usman sakon ya zo ya dukeshi, wata dankaliliyar mota ce usman ya xo da ita, sannu oga cewar usman yana kunshi dariyarsa, domin ba kadan ameer ke bashi dariya ba cikin wannan kayan, shema ameer dariya gaisuwar ta bashi.

 

 

Ina muka dosa cewar usman? Gidana kai tsaye ameer ya bashi amsa, gaskiya oga tsakanin jiya zuwa yau ka chanza , manta kawai usman abin ba sauki jiya kwata kwata ban runtsaba, yanzu haka Sun nakeyi na raka baccinda ban samu jiya ba .

 

 

Ta gefin nana ko kai tsaye da ta fito daga skull gidansu meenatu tayi, sallama tayi, ciki ciki meenatu ta Amsa sallamar, wajinki nazo meenatu cewar nana , ina jinki domin inada abinyi inji meenatu, sai da ta dafata ta soma magana, keyi hakuri kawata wlh ban iya jure hushinki , sannan kinfi kowa sanin halina, nasan kam inada son abin duniya, amma ke shaidata ce, ni ba yar iska ba ce .

 

Saurin katseta meenatu tayi, da cewa a da kam ina shaidarki amma wlh banda yanzu, jiya Gidan uban wa kuka je keda shi? ta jefa mata tambayar domin itama kanta meenatu da wannan tambayar ta kwana da ita ta tashi .

 

Allah sarki kawata wlh wlh munje wajan hutawa ne, sabuwar wajanda aka bude.

 

Wallahi kisan bazan taba sayarda mutumcina saboda kudi ba, nasan kam ina son kudi amma Son kudina baikai haka ba, jiya xuwa yau meenatu da kina hushi Dani wlh duk duniya tayimin zafi, kiyi hakuri nadaina duk abinda baki so insha allahu.

Itama meenatu ba karamin dauriya tayi ba tsakanin jiya zuwa yau, na rashin nana kusa da ita.

Sauke ajiyar zurciya tayi, ta kalle nana , nima nana ba zarginki na keyiba, inadai yimiki tsoron halin maza, basu da tausayi basuda amana basuda sabo basu da mutumci in sun Tasha cin amanar macce, bale ke ga mugun halinki na son abin duniya.

 

Cikin hikima meenatu ke fada nana gaskiya, baa Dauke dogon lokaci ba fira ta balke tsakanin aminnan.

 

Ama Alhaji kabir
Hussein 80k????????
[23/01, 19:33] 80k: ???????? *AUREN JINYA*????????

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION.*

 

Rubutawa
____________
*AMAH ALHAJI KABIR*
*DA*
*HUSSAIN 80K*

 

LABARI:
__________
*AMA ALHAJI KABIR*

 

 

SADAUKARWA
__________________
*GA SAMARI DA ‘YAM MATA.*

 

KIRKIRARREN LABARI NE.

 

*Page 10*

 

Na san mai karatu zai so sanin waye A) meer? Ameer matashin mai kudi ne, wadda ya tasu cikin arxiki tun ka kanni ka kanni sunkayi gadon arxiki, tsaya lissafa irin arxikin yan family den su ameer abu ne mai matukar wahala.

Baa arxiki kadai sunka tsaya ba dumin gidansu gida ne na sarauta ce, mai matukar girma, mahaifin ameerr duk cikin family densu Allah yafi dukakarsa.

Sunan mahaifinsa Alhaji Abdullah barade, duk jahar sokoto babu wanda bai san sunan ba, family den gidan ana kiransu da barade family.

 

Alhaji abdullah yanada matarsa daya hajiya kubura mahaifiyar su ameer, auren xumunci ne tsakaninsu dumin dan wa da dan kane suke na uwa daya uba daya.

 

Auren soyayya ne sunkayi ba auren hadi ba Sannan suna matukar kaunar junansu, inda Allah ya Basu yara biyar, Hudu maza , daya macce, wanda ameer shene babba, wanda kuma duk kan soyayar uwayensa tafi karkata wajinsa.

Ameer yaro ne wanda ya taso cikin gata da kulawa ta fannin ko ina acikin family dinsu, uwa uba anbashi tarbiya mai kyau, yayi karatunsa na addini so sai domin tun yana dan shikara bakwai iyayinsa suka kaishi madina chan ya samu dukan ilmin addini, bayan nan sannan suka fitarda shi ingila yayi karatun zamani har zuwa matin karshe.

 

Bayan ya dawo gidane fa , ya fara fuskantar matsala wajan yan mata , dana family dinsu dana waje, da kannin abokaninsa, duk maccinda tayi tozali dashi ko taji nasabarshi zata ce tana sonsa , inda shiko yake ganin dukansu ba mai kaunarsa da gaskiya domim yana da yakenin matan wannan zamani basu soyayar Allah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button