AUREN JINYA Complete Hausa NovelHAUSA NOVEL

AUREN JINYA Complete Hausa Novel

 

Cikin family dinsu mata da yawa aka bashi yaki yarda da aurensu, karshe ma ya nunama mahaifinshi shi yanzu sojah yake son yazama.

 

Wadda bakaramin Fama ba yasha wajan ganin yasamu yarda mahaifansa amma sunki yarda , daga karshe ya yanki shawara tunkaran kakansa barade.

 

Wanda babu bata lokaci kakansa ya kammala komi nasa na aikin sojah, baima bi takan mahaifin ameer ba, domin ya dade da raayin aikin shima kansa inda ya samu matsala irin ta ameee ga lokacin iyayinsa suka hana duba da ganin ya fito babban gida gidan sarauta, alokacin yaji ciwon abin, amma saboda baida yadda zaiyi hakura, shiyasa yanzu da jikansa ya zomasa da wannan bukatar, ya yarda mishi , duba da wannan zamani na komi, nah wa kasani ne, wa ya sanka, cikin Kan kannin lokaci komi ya kammala.

A lokacinda komi ya kammala sannan ne ya nemi mahaifan ameer ya shaidamusu zai tura ameer sojah

 

Babu maganar jayayya ko rashin aminciwar su , sai fatar ubangiji yasa ayi asa’a yasa da yawancin rai.

Duba da daurin gindi da kuma shaidar karatu, ameer bai dauki wani lokaci ba da fara aiki ya samu karan girma zuwa matakin sojah babba.

 

Wadda haka ya karamishi farin jini gun mata uwa uba ga kudinda ke garishi, lokacin dukar hutunsa ne ubangiji ya hadashi da meenatu a skull ya badda kama ya shigu skull den kamar yadda ya saba idan yana son sanin me ke faruwa cikin Al’umma .

 

Mundawo labari…..
Faisal ba karamin kama zurciyar Nana yayi ba domin mutum ne wanda ya iya soyayya ga kuma kudinda yake sakamma nana , wadda har abin yaso ya bata tsoro, amma duk wannan abin iya kaci ta waya domin tana gudun kada meenatu ta koma hushi da ita ko ta fadama mummy domin Tasan bakaramin aikin meenatu ba ne.

 

Yau faisal ya kudura sai ya fara dobar kudinsa da yake kashema nana , message ya turama nana na zaizo gidansu, ya gaisa da iyayinta, kasa samun sukuni nana tayi, domin ita a ganinta abin kunya ne ta kawo faisal gidan iyayinta, sannan tasan matsala meenatu tana ganin kamar ta tsani tarayyarta da Faisal, bale ta fada mata ya xo gidansu meenatu, haka ta yini sukuku karshe dai meenatu ce ta tsarita da tambayar meke damunta, dole da taga ba wata hanya ta fadama meenatu Gaskiya, meenatu saida tayi mata fada na nuna mata sanin darajjar gidansu, sannan ta ce ta bare ta fama mummy.

 

A waya ta sanarda mummy halinda ake ciki, inda mummy ta ce so bari ta taso aiki suyi magana .

Karfi hudu dai dai mommy meenatu ta faka motarta cikin get den gidan, mai gadin gidan yayi mata sannu da xuwa idan meenatu da nana suka fitu da gudunsu domin tarbun mommy.

 

Yanayin mommy da meenatu yanayi ne mai matukar burgewa, mu’amalasu dabance domin, duk tashin meenatu banda nana bata rayuwa da kowa sai mummynta , Akwai shakuwa so sai tsakaninsu, soyayyarsu dabance, kaunarda ke tsakaninsu ta musammance, haka rayuwarsu daya ce , babu mai boyema dayansa damuwarsa .

 

Kokarin amsar jakar hannun mummynta takeyi, cikin kulawa ta rugume meenatu kamar Sun shikara basu tare saida ta dan buge bayanta sannan ta ce I miss u, sannan ta sakammata jakar, cikin girmama nana keyi mata sannu da zuwa.

Tare suka jera kamar wasu sa’annin juna har xuwa cikin gidan, babu laifin gidan ya tsaro ikar tsaro irin na masu kudi amma kuma ba wai mahaukatan kudin ba.

 

Kai tsaye mummy dakinta tayi , inda ta rage kayan jikinta, tayi wanka sannan tayi sallah, sannan ta fito babban falon gidan.

 

Suma su meenatu sallah sukayi sannan suka fito babban Falon , cikin kulawa ta kalli nana mummy inda ta suma tambayar nana, waye Faisal.

 

Mommy nima fa ban wani saninshi ba so sai, tare da meenatu muka hadu , shi ne ya matsamin yana son yaxu gidanmu.

 

Taso xo kusa dani cewar mommy, wannan yazama al ‘dal mommy duk lokacinda zatayi musu magana Mai mihimmanci sai ta Kira su kusa dasu sannan kuma sai ta kama hannun mutum.

Kamar kullum yau ma haka ta kasance, saida ta kama Hannun nana duka, sannan ta suma magana

 

Ga dukan alama yana nuna kena son faisal nana, tunda har kinka amince da yaxo gidanku , sai dai abinda nake Sun ke sani mutanin cikin duniya Sun lalace, kafin ka yarda da mutum yanxo dole sai kasan waye shi, mazan yanzu basu da gaskiya basu gabas basuda alkibla, macce da wuya ta gane son gaskiya suke mata ko na shaawa, dun haka dole saida matukar kulawa da takatsan tsan sannan da addu’a da neman zabin Allah.

 

amma zanso haduwa da yaron IN yaxo, kuje kiching kufadama masu aiki abinda kukesu baiwa bakunku, amma lalle ina son ganinsa kafin ya wuce.

 

Ta gefin ameer ko, lokacinda usman ya kai shi karamin gidansa sai da yayi wanka ya karya sannan, ya kwanta domin rasa baccinda bai samu ba jiya.

 

Baccinsa yakeyi cikin kwanciyar hankali , kiran sallah azzahar ya tayardashi wanka yayi sannan yayi alwallah, cikin natsuwa ya ke sallahrsa bayan ya sallama, ya dade yana kai kokansa ga Allah, da kuma neman zabinsa game da mu’amalarsa da meenatu, kai tsaye gida ya nufa domin wata irin kewar mummynsa da kanninsa yake ji.

Dakansa yake jan motar har xuwa gidansu, Cikin matukar girmama ma tsara get din farko suka yimasa sannun da xuwa tare da bude get din.

Bayan ya aje motar get din karshe na shiga gefin hajiya kubura, wata yar kufa yabe sai gashi wajan wata lipta mai matukar kyau da tsare kai zaye ya dannan abin budeta ya shiga, sai gashi kayataicin falon gefin mahaifiyarsa, wani irin sanyi da kamshi ya xiyarci hancinsa da jikinsa, tsaya faden tsaruwar falon zaiyi wahala , Amma dai babu karya falon ya tsaro

 

Mummy mummy haka ameer ya kama kwallama mummynsa kira kamar yaro, asmau ce ta shigo falon cikin murnan jin dan uwanta.

 

Hannunsa ta kama sannu da xuwa ya ameer , yar autar mummy, ina mummy ya jefamata tambaya? Tana palon kasa da Baki , kafin kace kwabo hadimman gidan sun cika shi da kayan frut .

 

Ama Alhaji kabir
Hussein 80k????????
[23/01, 19:33] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

*????????AUREN JINYA????????*

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION.*

 

Rubutawa

*____________*
*AMAH ALHAJI KABIR*
*DA*
*HUSSAIN 80K*

 

LABARI:

*________*
*AMAH ALHAJI KABIR*

 

SADAUKARWA

*___________________*
*GA SAMARI DA ‘YAN MATA.*

 

KIRKIRARREN LABARI NE.

*Page 11*

 

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

 

 

*****Kan kace kwabo tuni hadiman gidan sun cika masa gabansa da kayan marmari kala-kala.

Kwantar da kansa yayi jikin kujerar tare da lumshe idanu, Asma’u kuwa sai surutu take masa shi dai yasan yanda yakeji a zuciyarsa game da Meenatu, Allah ka shige mana gaba akan al’amuran mu, abinda Ameer ya fad’a kenan a cikin ransa.

 

Bai jima sosai da zuwa ba sai ga mummy tazo inda yake, yana ganinta ya fad’ad’a fara’ar sa yana jin k’aunar mummyn tashi.

Mummy ta k’araso tana masa sannu da zuwa, har k’asa ya sauko ya risina ya gaishe ta, ita kuma ta amsa masa cike da fara’a. A kullum k’ara godiya ga ubangiji takeyi na baiwar wannan yaron Ameer da ya basu, yaro mai ladabi da biyayya, bai tab’a tsallake maganar su ba.

 

Hira sukayi sosai irin ta d’a da uwa wa’yanda suke matuk’ar ji da junan su. Ameer ya tambayar abban su, mummy tayi ‘yar dariya tace” ai kai ma kasan ba zaka ga abban ku warhaka ba”.

‘Dan b’ata fuska yayi yace” mummy shi abba bazai huta bane? Kullum cikin hidima ga jama’a ta ko’ina, anya ma yana yin baccin kirki kuwa?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button