AUREN JINYA Complete Hausa NovelHAUSA NOVEL

AUREN JINYA Complete Hausa Novel

Mummy tace” karka damu, to ya za’ayi tunda Allah ya bashi wannan matsayin, ni ba ma wannan ba wai har yanzu maganar aure shiru ko? Kullum cikin kawo mana uziri kakeyi an kawo maka yaran ‘yan uwa da abokan arziki amma duk kayi watsi dasu, me kakeso ka zama ne? Ko dai baka da lafiya ne?”

Sunkuyar da kai yayi yana sosa k’eya dan tambayar k’arshe ta saka yaji kunya domin kuwa ya gane nufin ta sarai, shi kuma a yanda yakeji gaskiya idan ba Meenatu ya samu ba to kuwa auren ma zai gagareshi. Yana cikin tunanin ne mummy ta katse shi da cewa” baka da abin fad’a ne kake wani sunne kai? To wllhy babu ruwana idan mahaifin ka yayi maka auren dole”.

Ameer ya zaro ido yace” auren dole kuma mummy? Haba sai kace wata mace?”

Murmushi mummy tayi tace” eh a kanka za’a fara ma maza auren dole tunda ka kasa neman matar da kanka”.

” Mummy dan Allah ki bashi hak’uri ko yayi miki maganar, matan ne sai a hankali kowacce ba dan Allah take nuna ma mutum so ba, amma insha Allah na kusa samu”. Gyad’a kai mummy tayi tace” ah to Allah yasa dai da gaske kakeyi dan ni har na fara tsoron ko baka da lafiya ne”.

Ameer ya mik’e tsaye yace” mummy ki daina cewa haka, ni lafiya ta lau kawai dai lokaci ne bai yi ba, zan tafi amma zan dawo wajen abba mu gaisa”. Nan dai sukayi sallama ya fita.

Wayarsa ya ciro daga aljihu yayi ‘yan danne-danne, kan kace me tuni sai ga Usman yazo wajensa yana cewa” ranka ya dad’e daga nan sai ina kuma?”

Ameer yace” gidana zan koma, kayi zamanka kawai ni kad’ai zanje”. Shi kuma Usman yana jin haka yace” to shikenan an gama ranka ya dad’e a sauka lafiya”.

 

Usman ne ya bud’e masa k’ofar motar inda mazaunin driver yake sannan yayi ma motar key. Mai gadi yana ganin haka ya wangame get tun kafin k’arasowar Ameer d’in dan akwai d’an tafiya tsakanin wajen parking d’in da bakin get saboda gidan girma gareshi ba na wasa ba, gida ne da ya k’unshi b’angarori da dama.

 

Bari mu lek’a wajen su Nana da Meenatu mu ga wace wainar ake toyawa dan yau su Nana ba dama za’ayi bak’o, bak’on ma Faisal mutumin da takeso kamar ranta.

 

Nana na hango anci uwar k’walliya kamar zata je wajen wani dinner, Meenatu dai ba ruwan ta da irin k’walliyar haukan nan bare ma da ba ita zatayi bak’on ba, hasali ma ita bata cikin wannan abu dan karatun ta ne kawai a gabanta, samarin yanzu duk mafi yawansu mayaudara ne ba dan Allah suke zuwa wajen yarinya ba. Shine abin take jiye ma Nana.

 

Kafin Faisal ya k’araso tuni komai ya kammala. ‘Karfe 5pm Faisal ya iso k’ofar gidansu Meenatu kamar yanda Nana ta bashi adress d’in. Faisal ma yau shigar shadda galilah yayi, shigar ta masa kyau ba laifi.

 

Ya samu tarba a wajen Nana haka Meenatu ma ta daure tazo sun gaisa da Faisal fuska ba yabo ba fallasa dan ita fa bata gama yadda cewa Faisal son gaskiya yake ma Nana ba, sai dai kawai yanason yayi amfani da Nana ne dan ganin tana da son abin duniya. Allah ya kyauta.

 

Kafin Faisal ya tafi ya gana da mummyn Meenatu sun gaisa sosai kuma ya nuna auren Nana zaiyi, mummy dai kallon sa tayi sannan tace zata yi shawara da abban Nana duk yanda akayi zai ji.

 

Wata mota ce mai shegen kyau ta karya kwanar gidan su Meenatu, a hankali yake driving cikin nutsuwa, amma ba zaka iya ganin mamallakin motar ba saboda bak’in glass ne ke gareta, babu abinda ke tashi cikin motar sai k’ira’a. Kunsan waye wannan? Ba kowa bane face Ameer.

 

A daidai lokacin kuma Meenatu itama ta fito tana sanye cikin uniform na islamiyya…….

 

 

 

Amah Alhaji Kabir
Hussein 80k????✍????
[27/01, 00:46] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

???????? *AUREN JINYA*????????

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION.*

 

Rubutawa
____________
*AMAH ALHAJI KABIR*
*DA*
*HUSSAIN 80K*

 

LABARI:
__________
*AMA ALHAJI KABIR*

 

 

SADAUKARWA
__________________
*GA SAMARI DA ‘YAM MATA.*

EDITEN BY
Real shaxee????

KIRKIRARREN LABARI NE.

Page 12

Ameer cikin hikima yake bin Meenatu zuwa islamiyyarsu, a gaban idon sa sunka shiga ciki , sannan yakira wayar daya daga cikin yaransa, ya mika mishi motar, ya badda kama, zuwa shagon garbati.

 

Cikin yanayin garbati na koda yushe ya tarbi Ameer, cikin tsoka na, yake cewa .‘’Nafa dauka ka gudu dana ga ka dade ba ka dawo ba dumin ko matasan yanxu baku son aikin wahala.‘’

‘’ Haba oga ai dole mutum ya nemi nakansa kasan fa yanzu ba a son mutum sai yanada, Bale matan yanzu, duka garbati ya kaima Ameer yace.‘’ Dadina dakai kanada hankali wlh kasan duniya so sai , ya maganar aikin da kaje nema da fatar andace?.‘’ Murmushi Ameer yayi yace. ‘’ Ansamu oga gadi ne na dare kwana kawai zan rikayi a chan.‘’

 

Fadada murmushi garbati yayi, yace.‘’ gaskiya naji dade mutumina, ubangiji yasa arzikinka na cikin aikin.‘’ murmushi kawai ameer yayi.

 

‘’Oga ina kayan wankin hajiyar nan ta jiya ka kawo na meka mata su a gida, ka ga har na manta da nace yau za a kaimatasu, duka ga su chan ka meka mata, ka kuma gaisanmin da ita so sai. ‘’

 

Cikin natsuwa Ameer ya donki kayan wankin zuwa gidansu Meenatu, get den gidan ya buga baba mai gadin ya taso ya tambaya waye, mai kawo wanki ne ameer ya bashi amsa.

‘’ Baba na bude get din.‘’ ameer yayi cikin gidan kai tsaye, babu alamar fargaba, bakin kufar falon ya tsaya ya kwankwasa, waye cewar mummyn meenatu, mai kawo wanki ne cewar ameer,.

Kofar mommy ta bude ta bashi damar shigowa cikin falon, cikin girmama ya durkusa ya gaida mommyn Meenatu, bayan ya aje wankin saman daya daga cikin kujirun falon.

Lokaci daya mommy taji Ameer ya kwanta mata har cikin zurciyarta, sai kuma tana yimai kallon wani wanda ta taba sani,

 

Cikin kulawa take Amsa gaisuwar sa, tare da cewa ya tashi ya zauna saman kujeran falon, amma kimimi yaki zauma saidai ya Zauna a kasan kafet din falo.

Ladi mai aiki mommy ta kwallawa kira bayan tazo ta ce ta kawoma Ameer ruwa, bai yi kokaren hanawa ba domin yanason ya samu hanyarda zaibi ya kulla huda da mommy ta mutumci.

 

Laimo mai sanyi ladi ta kawomasa yana sha mommy ta cemai kaini sabon yaron garbati da ya fadamin, cikin girmama ya ce mata eh shine.

Bai wani dade ba yayi mata sallama ya wuce, ko a bakin get den gidan sai da ya dan tsaya yataya baba mai gadi fira, cikin lokaci guda sunka Dan saba, har baba na rokon ameer in yasamu dama ya ringa zuwa suna fira, saboda bai jin dadin zama shikadai kuma gidan mutane basu cika shigarsa ba.

Cikin lokaci kaliln Ameer yayi sabo dasu sai da mommyn meenatu da baba mai gadi da ladidi mai aiki, saidai cikin wannan lakaci ya fahimci mommyn meentu mutum ce mai matukar kamun kai da sanin ya kamata ma’abuciya son addinni, Sai dai ya fahimci tana cikin wata matsala wadda ita ke sata rashin walwala kamar kowa

Duk tsowon wannan lokacin da ya dauka bai taba barin ya hadu da Meenatu ba a gidan, asalima ita meenatun sai dai tanada labarinsa wajan mommynta Ko ladidi mai aiki domin da wuya su zauna fira in ta dawo daga skull baa ce ameer kazaba ko yayi kaza, har mamakin ta keyi yadda ya samu shiga ga kowa na gidan daga kawai kawo wanki ko amsar wanki.

Ta gefin Ameer ko wata irin soyayya yake ma meenatu Wanda ko a labarin tarihin masoya bai taba jin irinta ba, tabbas yasan ubangiji ya jarabcishi da kaunar meenatu, sannan yanada yakin muddin ya samu Meenatu a matsayin matarsa yayi dacen mata, sai dai anashi raayi yafi son ta so shi a matsayin ba kowa ba, saboda yawancin mutanen duniya na yanzo Sun fi daukar kudi da mihimmaci fiye da komi, Bale yam matan wannan zamanin….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button