AUREN JINYA Complete Hausa NovelHAUSA NOVEL

AUREN JINYA Complete Hausa Novel

 

Ama Alhaji kabir
Hussein 80k????????
[02/04, 22:36] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

???????? *AUREN JINYA*????????

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION.*

 

Rubutawa
____________
*AMAH ALHAJI KABIR*
*DA*
*HUSSAIN 80K*

 

LABARI:
__________
*AMA ALHAJI KABIR*

 

 

SADAUKARWA
__________________
*GA SAMARI DA ‘YAM MATA.*

 

KIRKIRARREN LABARI NE.

 

Page 13

 

 

Cikin kankanin lokaci ameer ya mugun sabo da mummy mahaifiyar meenatu , yakan ware lokaci yaje gidan ya bawa fulayoyin gidan ruwa haka mummy zai dan shiga wajanta ya gaidata koma su dan tafa fira, har cikin ransa yana matukar jin mutanin gidan dumin ya fahimci sunada wata matsala wadda ta addabi rayuwarsu , kuma matsalar ta yi mugun shiga cikin jikinsu ta taba komi na rayuwarsu , sannan ya fahimci mummy macce CE mai taka tsantsan da duniya , mai yawan addini , ya kanyi mamaki miyasa suke rayuwa su kadai da ga mummy sai meenatu sai kuma masu yi musu hidimar gida .

Ta gefin garbati ko bakadan yake son ameer ba yakan jishi kamar wani dan uwansa yakanji tamkar tun taso warsa yasan ameer dumin ya fahimci ameer yaro ne mai good mu’amala da mutane sannan yakanyi mamaki yadda yana talakka amma abin hannusa bai rufe masa ido , duk da albashinsa ya amsa yakan mekama garbati yace ya dauki rabi ya Adana mishi rabin . saboda karyar samun aikinda yayimai na gadi da dade shiyasa ameer baya kwana shagon garbati saboda ya gwada bai karda dadi ba Abu ga dan Hutu .

Yau ya kudiri kaima mummy ziyara kasan cewar yau babu aiki yasan tana gida ,hakama yana San ran samun meenatu a gidan ,

Wani farin yadi ne , dinkin wando da Riga , da ganin yadin Kasan na masu karamin karfi ne , amma babu laifi kayan sunyi mai matukar kyau hulla baka da takalmi baki yasa ba karamin fitowa yayi ba , bakin shagon garbati yake , garbati na xolayarsa , kaga kanina kamar sabon ango cewar garbati , anya ba wajan surukata zaka je ba wannan gayen haka ? Ya fada cikin siggar xola , shema ameer dariya garbati ya bashi amma dai ya kasa CE masa komi kawai yadai yi murmushi ya dan dade zaune wajan sannan ya sulale ya gidan su meenatu .

 

Cikin natsowa yake tafiyarsa har ya kai get den gidan ya dan kwan kwasa baa Dauke lokaci ba yaji baba mai gadi nacewa wa a nan ??? Cikin girmamawa kamar yana kusa dashi yace nini baba , ina zuwa yaron kirki cewar baba mai gadi dama haka yake kiran ameer tun farkon haduwar su .

Sannu da zuwa yaron kirki cewar baba bayan ya bude get den gidan , yauwa baba , barka da safiya ya aiki ya koma manyanci inji ameer hannu yasa cikin aljihun rigarsa ya fidda kullin goro ya mika ma baba .

 

Mi munka samu kuma yaron kirki cewar baba tare da meka hannunsa ya anshin goron , kai maddalla wlh kamar kasan yau koda na tashi banda goron , na gode so sai ubangiji yayi maka albarka yasa ka gama da duniya lafiya , muemushi ameer keyi yana cewa ameen ameen baba nima nagode da addu’arka Allah ya sakama da mafificin alhirinsa .

 

Sun dan taba fira ameer ya cema baba zan shiga ciki na gaida mummy , ya kamata gaskiya cewar baba mai gadi.

Sallama yayi bakin kofar shiga falon gidan cikin siririyar murya Anka amsa mishi sallamar , muryarda ko a wani hali zai iya shaidata watun muryam meenatu , shigo ta CE a takaici , ba karamin mamaki ta bashi ba yau , ganin duk zuwanda yakeyi gidan bakinta bai taba haduwa da nashiba sai yau , bayan ya shiga ya samu daya daga. Cikin kujirun falon ya zauna , ba ta koma cimai kalaba ta ci gaba da garan farantan ta , shima bai bi ta kantaba ya ci gaba da zamansa amma cikin hikima dukan hankalinsa na kanta , ba karamin burgeshi yatsan hannunta yayi ba , komi na meenatu mai kyau ne kamar yadda take mai kyau , ya dade zaune bai ga alamun mummy ba haka bai ga ladidi ba , don Allah yimin magana da mummy in tana gidan cewar ameer sai da ta yi kamar bazatayi magana ba sannan nace mummy na bacci , kala bata koma cewa ba ta ci gaba da garan farantanta , ladidi ce tayi sallama cikin falon Duke da ruwan Lipton cikin kufi da tere ta gaje gaban meenatu tace uwar dakina ga liptonp na hada miki , sai da tayi murmushi sannan tace ina godiya , sannu da xowa ta gaida ameer shima cikin sakin fuska ya kai da ita .

Ina fa jin hajiya tayi hushi da kai dumin ya kai sati take cewa Allah yasa lafiya , ta bar jinka kuma gashi baka bata number wayarka ba,

 

Ladidi wa yace miki mutum na hushi da dansa??? mummy CE mai fadin haka tana kokarin shiguwa cikin falon ,

Har kasa ya duskus ya gaida mummy cikin mutumta juna suke gaisawa , gaskiya ameer saura kadan nayi hushi da kai mummy ta fada cikin tsoke fuskarta , ina ta tunanin lafiya , najika shiro kwana biyu , kasan kuma halin rayuwa ,

Ayi hakuri mummy wlh wajin da nake aiki ne babu Hutu shiyasa Cesar ameer cikin girmamawa , ladidi je ke hada muna abinci nida yarona cewar mummy .

 

Tare suke cin abincin su hankali kwance kamar da da uwa , ba karamin mamaki abin ya baiwa meenatu ba , yadda mummy tayi sabo da ameer haka , sai kawai taji tana kishin ameer har cikin zurciyarta .

 

Tashi tayi ta bar falon saboda ta fahimci kamar mummy ma ta manta da ita har zata fice cikin falon taji mummy na cewa ke baki tashi cin abinci ba , nakushi ta baiwa mummy a taikaice .

Sun dade suna fira duniya da inda mummy ke dan tambayarsa abubuwa da sunka shafishi na rayuwa matsayin karatunsa da kyauyensa .

Ita dai haka kawai takewa ameer kallon da koma ya kwanta mata a zurciyarta sanan yanai mata kama da wani Wanda tayi tarayya abubuwa da yawa dashi a baya .

 

Ya dan dade sannan ya ce ma mummy zai je gida , meenatu ta kwallama kira , tana cikin daki ta amsa mata , ke dukumin jikkar hannuna cewar mummy , baa wani dadewa ba ta duko jikkar saida ta dan runsuna ta meka mata jikkar .

 

Waya ce saboda fil cikin kwalinta ta duko cikin jikkar ta meka ma ameer gashi akwai layi a cikin mu rika gaisawa ,cewar mummy .

 

Murna ya nuna tare da godeya so sai yace mummy da baki waharda kanki ba wlh ,

Yanzu don na sayama waya kake gani wahala ce ta jefa mishi tambaya? Shiro yayi ya kasa cewa komi , saidai cikin zurciyarsa ya mai jinjina irin hali na mummy.

 

 

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button