AUREN KADDARA KO BIYAYYA Complete Hausa Novel

.An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau – kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau – manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau – Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that – we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that – pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that – our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__
“Kyawawan” dattijaine guda biyu a kayataccen, falonsu dayaji kayan more rayuwa kallo daya zakai musu kagane dattijan ma’auratan suna matukar “so” da kaunar junan su.
Aka kwankwasa kofa tare da sallama suka bada izinin shigowa. Wani kyakykyawan saurayine mai lafiya da kuzari kallo daya zaka masa kagano tsananin kamarsa da dattijan dake zaune afalon dan harya so yafisu kyawu, saboda duk ya hada kyawun dattawan guda biyu,
Yazo ya tsugunnah agaban iyayennasa, barka da yamma dad & mom.
Cikin fara’a suka amsa dad yace babana ya gida ya iyalin ?? Yadan rage fara’a sannan yaca kalau dad. Mom takallesa babanmu yadai naga karage fara’a dan antan bayeka iyalinka, yace bako mai mom.
Dad yace ban yardaba dady akwai matsala, dady bazan juri ganinkaba acikin rashin walwala tabbas nayimasu yaya biyayya kuma kaima kayi mini, dan haka na yanke shawarar kaima yanzu kanemo zabinka ka kara AURE. Da sauri ya dago kai yan kallon dad dinnasa, dad yadaga masa kai alamar hakane
Shima cikin rauni ya girgiza kai tare da fadin dad AURE kuma?? Inji da wadannan ma dad.
Dad kaima dakake da shekaru dayawa aduniya kana mata daya ka hakura saini da ban wuce 30 ba ace inada mata biyu har ana neman nakara ta uku, haba dad dan “ALLAH” KAyi hakuri wallahi bala’in mata biyun nanma neman zautani yakeyi bare uku iba so kuke kurasaniba dad
Bazamu rasakaba dady insha “ALLAHU” sai munga ‘ya ‘yanka. Hasalima wannan kara auren shine zai samamaka zaman lafiya agidanka damu kanmu, yakama ta kasamu mai kwantar maka da hankali babana. Jibi yanda ka rame ka lalace sai dogon hanci????da tsayi duk ka fita hayya cinka acikin shekara daya
Tunda aka fara maganar auren ka da yarannan bamu sake ganin dariyar kaba dan haka kaje kayi nazari akan maganar nan kaji. Kayi hakuri konace ka kara dan “ALLAH” yana tare damasu hakuri ya fada tare da shafa kansa.
Dady yasaki ajiyar zuciya yace to dad na gode in sha allahu zanyi kokari bari nawuce gida , mom sai anjima. Tace to dady kagaida gida tafada cikin raunin murya, ya mike ya fice……..
suka bishi da kallo hawayen da mom ke makalewa suka zubo, dad ya kalleta haba bilkisu ai dama tunda naga kinyi shuru nasan kuka kikeyi, adda’a yaronnan yake bukata agaremu ba kukaba yasa hannu yana share mata hawayen fuskarta.
Tace hakane alhaji, amma al’amarin yaronnan yana damuna matuka.
Hakane amma muci gaba da yimasa addu’a “ALLAH”ya kawo masa mafita.
To amin alhaji.
Shikuwa abdul’aziz wato dady bayan fitarsa daga gidan iyayensa mota yashiga ya nufi gidansa zuciyarsa ba dadi jiyake tamkar kar yakoma gidan yana isa kofar gidan yay hon mai gadi ya bude masa get yaturo hancin motarsa???? zuwa ciki ko gaisuwar mai gadin bai amsaba, bayan yayi parking a ma’ajiyar motocin???????????? yanufi cikin gidan wanda yake da tazara da harabar ajiye motocin
Tunda ya gabato gidan yake jin hayaniya yay tsaki tare da fadin karnukan ???????? banza, yaturo kofar falon yashigo, ilai kuwa matan nasane sukecin uban danbe da zagin fallasa tamkar ba ‘yan uwan junaba
Kallo daya yay musu ya dauke kansa, dakinsa yanufa da sauri ikileema ta sha gabansa tana fadin malam jimana.. yabita da kallon mamaki, tare dafadi bani hanya nawuce. Tarike kugu da hannu daya tace ba inda zakaje saika gayama waccan jakar cewa ita ba komai bace agurinka tafada tana nuna husna da dayan hannunta, husna tazo ta damki wuyan rigar ikileema tace kece jaka banza karamar ‘yar iska aike yakamata ya fadama wannan kalmar baniba shashasha kawai, aifa kan kace me danbe yasake har kumewa har suna kokarin fada masa
tsawa yadaka musu waiku wadanne irin shaidanu ne ko so kuke ku maida mini gida gidan gala ne , dan danan suka nutsu ya watsa musu harara wallahi kunji na rantse duk wadda na sake jin muryar ta acikin ku kunsan “ALLAH” saita kama hanyar gidansu da saka mako mai kyau dan nagaji da iskan cinku, inkuma kun cika cikakkun ‘yan club ku cigaba. Ni nan dakuke gani nafiku iya iskanci. Yashige dakinsa tare da banko kofa da karfin gaske, sukansu sun razana
Kowa tai tsaki tanufi dakinta, dan suna masifar son dady da tsoronsa.
“Shikuwa gadonsa yafada yana fadin na shiga uku ni abdul’aziz wannan wace irin rayuwace ta dabbobi ya “ALLAH” kakawo mini dauki a lamurana….
????
TUSHEN LABARI
alhaji el~mansur adam sa’id sunan mahaifin abdul’aziz (dady) su uku mahaifinsu ya haifa alhaji adam sa’id yola, matan alhaji adam biyu halima wadda suke kira umma itace uwar gida tana da yara biyu ashiru, da salisu,
Sai amarya maryam dasuke kira gwaggo tanada da guda daya mansur, alh adam dan kasuwa ne babba a yola domin in har za a lissafa manyan ‘yan kasuwa na yola zai iya zuwa na goma. Gidan alh. adam anayin zama bana jin dadiba domin uwargidansa haj.halima macace mafada ciya sosai, amaryarsa kam tada matukar hakuri haj.maryam,dan haka yaronta mansur yakasance mai hakuri gashi kuma karami acikinsu
Yaran haj.halima sun gado halinta kaf suna bin hudubar ta daki~daki sun raina gwaggo danma suna tsoron babnsu