AUREN KADDARA KO BIYAYYA Complete Hausa NovelHAUSA NOVEL

AUREN KADDARA KO BIYAYYA Complete Hausa Novel

Haka dad yatafi gida cikin bacin rai dan yasan wannan auren ba don allah aka kulla shiba akwai wani abu aransu, yasamu mom da maganar dayake macece mai matukar hakuri sai tace bakomai allah yasa alkairi,sai ma tarinka kwantar ma dad hankali, suka kira dady sukai masa nasiha sannan suka sanar dashi abinda ake ciki, shima dayake mai biyayyane saiyace ba komai indai su sun yarda to shi bashi daja,dad yace allah yayima ka albarka babana, amin dad nagode.

Haka aka daura aure rankowa agida su dady bayaso an fara daura na ikileema, sai husna da daddare aka kai amare bikin bawani armshi dan dady ma ko gurin daurin auren bai jeba bai kuma gayyaci kowaba,saisu safwan dasukazo daga yola, tare sukai karatu a amerika, safwan,sadiq,jafar,suna kaunar junansu.

Shi angon ma ranar a asibiti ya kwana abinsa,
Wasa wasa dady yaki yarda su hadu da amaren nasa har tsawon sati biyu, wannan yasa suka wanke kafa fuwa sukakai kararsa wajan dad,
Dad yabasu hakuri yace suje gida zai masa magana,sukace to……

Bayan tafiyar su dad yakira dady yace inya taso aiki yazo gida yana nemasa,
Yace to,bayan yataso daga aiki kai tsaye gidansu yataho,yarussuna ya kwashi gaisuwa wajan tsaffinsa,cikin gimamawa, yace mom ina ‘yan biyu?? Mom tace suna makaranta, to allah yadawo fasu lafiya.

Dad yace ina ganinka mai han kali babana ashe ba haka bane??dady yace dad minayi?? Dad ya gyara zamansa dazu matanka sunzo nan gidan sunce tunda aka aura maka su baka taba shiga dakinsu ba bama su gankaba.
Dady nasan baka son aurennan kayimi biyayya ne kawai,to dan allah ina rokonka kaji tsoron allah ka bi dokar ubangijinka,domin aure bautar allah ne,kaga yanzun hakkinsu akanka yake,dolene kasauke, kadaure ma zuciyarka karinka kamanta adalci agaresu, ka ajiye maganar raashin sonsu gefe, kaima allah biyayya saiyaji tausayinka ya hadaka da wadda kake so nan gaba ko allah ya canja maka halayensu na banza zuwa na kwarai danka amfana.

To shike nan dad nagode zanyi kokari kayi hakuri, sun tattauna sosai sannan yay musu sallama yatafi gida…..

.

Ba,a gane dadin littafi a farkonsa, dole sai tafiya ta fara yin nisa tukunna, don haka ina tabbatar muku da cewar zakuji dadin littafin nan sosai!

Kuci gaba da kasancewa dani kawai!

Mu kwana lafiya….

.
[8/16, 11:55 AM] ???? “???? ” D’????⭕Y????????: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ ????????_*
[8/16, 11:56 AM] ???? “???? ” D’????⭕Y????????: ????AUREN KADDARA????
????ko BIYAYYA????

.

Page 03 «*****»

.

Sanda ya isa gidan, matan nasa na falo zaune, yaturo kofa da sallama yashigo, suduka suka mike suna masa sannu, ya amsa ciki ciki dan haushin su yakeji ,duka suka rakashi dakinsa, suka zauna bakin gado, shikuma ya shiga bayi danyin wanka,dakin ya burge su sosai ba wani tar kace aciki,daga wardrobe sai gado sai madubi, sai katon hotonsa shi kadai saikuma wani shida ‘yan biyu da iyayensa sunyi kyau,sunan suna kalle kalle, ya fito wanka daure da tawul ya ratayo karami a wuyansa yana goge sumar kansa, su duka suka tsura masa idanuwa????, yadanja karamin tsaki amma basu jiba, gaban madubi yanufa yashafa mai, sannan ya canja kaya zuwa kanana,yada wo yazauna kan kujerar madubi ,ya kallesu fuskarsa ba walwala dazu waya baku izinin fita da har kuka kai karata, wajan dad dina.
Ikileema tace kayi hakuri bazamu sakeba husna ma ta baahi hakuri, ya dan tabe baki to naji daga yau duk wadda tasake fita bada izeninaba inhar ba school zataba to zata hadubda fishina,ya mike yana duban agogosa ni nawuce masallaci.

Sukace to adawo lafiya, bawadda ya tanka ma wa ya fice abinsa,suka hada baki wajan kiran jara babbe dole dai azauna damu, suka tun tsure da dariya harda tafawa

************
Bai dawoba saida akayi sallar ishsha’i,kai tsaye dakinsa ya nufa yay kwanciyarsa wajan karfe 9:pm saiga husna tazo cikin kayan barci anata wani karye karyen jiki waisu mata ko kallo bata isheshiba, sai kuma ga ikileema itama cikin kayan barci, cikin mamaki suka kalli juna, ikileema tace husna miya kawo ki dakin mijina, husna ta kalleta kallon raini mijinki kuma canza dai maganarki yarinya

Ikileema tace husna kinsanni niba kanwar lasarki bace, aikin sanni sarai, dady yadaka musu tsawa kunga dallah malamai kumin shiru kudaina yimin hayaniya aka,su duka suka tabe baki sannan kowa ta zagayo gefensa ta kwanta suka sakashi tsakkiya lokaci daya suka kai hannu zasu tabashi, dasauru ya mike zaune suma suka tashi, kallon banza yay musu to dakuka sakani tsakiya mi kuke nufi da ku biyun zan kwana tamkar akasar arna, yavmike kunga ku sasata kanku tukafin guri ya kure muku inba hakaba zakuyi biyu babu wallahi ya shige bayi abinsa….

husna ta watsama ikileema harara, banza mayyar maza saiki kwana, ta tashi tafice dan dama husna akwai zuciya.

Alwala yayo ya fito,ya kalli ikileema data cika tai fam saboda maganar da husna ta fadama ta tayi mata zafi, yace ke tashi kiyo alwala, yanda taga ya hade rai saita mike tayo alwalar ta fito, taje dakinta ta dakko zani da hijjabi,

Sunyi nafila raka’a biyu yay musu addu’oi, sannan ya hau yimata tanba yoyi akan addini?? amma ba wadda ta amsa, tundasu ba islamiyya suke zuwaba,ransa yay zafi yaja tsaki kaini dai wallahi ban moreba, to tayaya za’ayi wannan tabama yaranka tarbiyya?? Azuciyarsa yake wannan maganar,ya tashi ya canja kayansa zuwa na barci yasaka turaren barci, gado ya haye abinsa,itama tamatso kusa da shi dan ganin yanda yakoma karshen gado,
amamakinsa saiyaji tana shafashi, ransa ya kara baci, akasar hausa ansan mace da kunya musaman adarenta na farko,amma yazaiyi tunda matarsace, yakuma tuna nasihar iyayensa ta dazu da rana.dole ya daure ya karbi tayinta yabata hakkinta, bayan nutsuwa tazo musu,sai wani farin ciki ya lullube ikileema tuda take hudda da maza bata taba samun gwarzon namiji wanda ya iya soyayya irin dady ba, gaskiya yau tasami natsuwa sosai, duk da ta lura dady farin shigane, tana ganin ma yaune rana ta farko da fara sanin mace arayuwarsa, dan ta kula bama wani iya harkar yayiba sosai, amma dai yayi kokari.

Shikam wani irin bakinciki ne yacika zuciyarsa, dukda bai taba kusantar maceba, shi likitane na mata kuma yanada ilimin addini musamman na “fikihu”, yayi karatu mai zurfi akansu, yasan dukkanin suffofin mace budurwa, yasan na wadda tasan namiji, ya fitar da huci mai zafi, “ALLAH” kai shaidane ban taba zinaba,amma ka jarabceni da auren mazinaciya,YA ” ALLAH” ina neman afuwarka da gafararka tasanadin hakurin zaman dazanyi da ita,”ALLAH” kafini sanin dalilin yin hakan.ya mike yashiga bayi yay wanka,sanda ya fito har tayi barci, wata muguwar harara ya zabga mata, yaja guntu tsaki, ya dauki filo ya dawo kan kujerar dake dakin ya kwanta,zuciyarsa cike da tsanarta……

Da safe haka ya tashi duk ransa ab’ace wata k’arin tsanarsu yakeji aransa,dan yasan itama husnar duk tafiyar d’ayace,tunda bata da k’awar data wuce ikileema,bayan yayi wanka ya shirya cikin k’ananun kaya yayi kyau, ya tara matan nasa yagaya musu doko kinsa,cikin isa yay musu sallama”
” suka amsa ”

“Yay musu kallon second biyar, yak’ara tsare gida ina san sanar daku hanyar dazamu iya zama lafiya daku in kunso,
Na farko bana son k’azanta,
Na biyu bana son yawo,
Na uku bana son hayaniya,
Na hud’u bana son taron k’awaye acikin gidana, bana cin abincin ‘yan aiki, ban yarda ‘yan aiki sushigar mini d’akiba da nufin gyara, wannan kad’an daga cikin doko kina ida kun kiyaye kun tsira in kuma kun k’iji ba kwak’i ganiba, ya mik’e ya kwashi wayoyin sa da makullin mota yay waje”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button