AUREN KADDARA KO BIYAYYA Complete Hausa NovelHAUSA NOVEL

AUREN KADDARA KO BIYAYYA Complete Hausa Novel

Husna tamik’e kai dai kasani miskilin banza, mutum kullum ba dariya sai kace wanda uwarsa ta mutu.
Ikileema kam kwanciya tayi bisa kujera tana fad’in saika nemi mai bin dokarka dan wallahi ba ‘yan aiki aka kawo makaba masifaffe.

Itama dai husnar yanda yazata haka ya tarar fanko ce, haha suka cigaba da zama,ikileema da husna kullum fad’a kamar karnuka,arana saisuyi dambe sau uku,ga cin mutun cin iyayensu kamar ba ‘yan uwan junaba,
Shikam baya kulasu dan bayason hayaniya,
»«°°°°°°°°°°»«°°°°°°°°°°°°°»«
Jin anturo kofa ya bud’e idanunsa farare tas masu yalwar gashi ya kalli k’ofar,
Husnace yaja doguwar ajiyar zuciya,
“Tace my one ga abinci canfa yana jiranka.
Yace kun gama damben ne? Ta yatsine fuska ai ita taja, kasan ta da rainin hankali.

Yata shi zaune kudai kuka sani,niba wannan na tan bayekiba,
Tad’an tab’e baki, nidai ga abinci can nace,

“Na koshi aikinsan bana cin girkin ‘yan aiki, ta waro ido waje???????? kar dai gayannan ya k’i cin abincinnan,in baiciba ai ta banu yanda mamy ta gargad’eta akan tatabbatar yaci dan ba k’aramin kudi ta kasheba wajan amso maganin da aka dafa abincin dashi ba????????,
Tuna nin mikikeyi inata magana,
Tai saurin dai daita natsuwarta, aiba ‘yan aiki suka girkaba nina girka dakaina,

Cikin masifa yace to nace na k’oshi ko dolene saina ci? dalla ficemin ad’aki ina buk’atar hutu, ya koma ya kwanta…..
.

Ina fatan dai zuwa yanzu kun fara fahimtar inda littafin nan ya dosa???

.
[8/16, 11:56 AM] ???? “???? ” D’????⭕Y????????: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ ????????_*
[8/16, 11:56 AM] ???? “???? ” D’????⭕Y????????: ????AUREN K’ADDARA????
????Ko BIYAYYA????

.

Page 04 «*****»

.

tsaki taja amma baijiba dan tasan inhar yaji sai yaci k’aniyarta, duk iskancinsu saidai suyi iyasu kad’ai amma basa sakashi ciki,suna mugun jin tsoronsa,

“Yau dai antashi da ruwan safe, dan haka garin ya d’au sanyi, dady yana cikin bargo ad’akinsa saboda ruwa baije aikiba ,barci yake mai dad’i,saiya jiyo hayaniyar su husna yaja tsaki yagyara kwanciyarsa, jin abun bana k’arewa bane ya tashi cikin fushi yanufi falon,ikileema ce ta shak’e husna tanata jibga,kamar uwarta,

“Dady yadaka musu tsawa kunsan ALLAH in har baku bariba zan zaneku,dukda dukan mace baya cikin tsarina,kainifa na gaji da iskancin nan naku wallahi gab nake da kora ko waCce gidan ubanta idan kuma kunji karya kuci gaba ya fad’a yana nufar d’akinsa”

“Kan gado yafad’a rubda ciki,yadafe kai ni ABDUL~AZIZ naga takaina wannan wace irin rayuwace, AUREN KADDARA ko BIYAYYA za a kira aurena,
Hayaniyar su ikileema yaji sun cigaba da fad’an,yace nidai shike nan an aura mini jaraba,
Mikewa yayi yacanza kaya ko wanka baiyiba,ya d’auki key d’in mota da wayoyinsa ya fito,ko kallo basu isheshiba ya wucesu afalo suna danbe,
Gindansu yanufa su mom suna falo harda ‘yan biyu sunata hirarsu,sallamarsa sukaji ‘yan biyu suka mik’e da gudu suka rungumesa.
“Yace oh ku waibakusan kun girmaba??
Sukai dariya yaya mubamu wani girma ba sai nan gaba,
Ya zauna yana gaishe da iyayensa, suka amsa masa cikin fara’a,
Mom tace babana inji dai lafiya naga kamar da damuwa atare dakai,
“Yay d’an tsaki mom barci nakeji wallahi, to miya hanaka yi? Kataho nan acikin ruwannan,???????? baka tsoron mura?
To mom ina tare da karnuka???????? yaza’ayi subarni nayi barci,
Ya mik’e ransa a b’ace yanufi d’akin mom,
Binsa sukai da kallo cikin tausayi duk yarame sai fari da dogon hanci, dad yakalli mom dolene munema ma yaronnan mafita Bilkisu, mom tace gaskiya kam alhaji nima lamarinsa ya fara bani tsoro,
Kairat tace ALLAH dad kubar mu muje mu koya musu hankali, dan wallahi baza mubari su kashemana d’an uwa ba,mom tace a’a bamu aikekuba.

Gadon mom ya haye abinsa cikin minti goma barci yay awan gaba dashi….

su mom sun yanke shawarar zuwa yola amma nikaina bansan abinda zasuje yiba,
Kamar kullum yakanzo yagaida iyayensa, yashigo falon mom ce kawai sai kausar tana karatu,guri ya nema yazauna,ya gaida mom d’insa kausar ta gaidashi,yace ina kairat?
“kausar tace tana d’aki tana barci yaya”
“Yar gata barci yanzu da yamma’
“Mom tace jibi zamuje yola in sha ALLAH”
Zamu dawo ranar lahadi.

To mom ALLAH ya kaimu,ke nanma sai ansaka ranar auren su safwan,tunda on Saturday ne?
Ai dama shiyasa zamukai Sunday,
To ALLAH ya kaiku lafiya kudawo lafiya, nima naso zuwa to munada wani taro na likitoci ranar Saturday,

To ALLAH ya taimaka aigara ka tsaya wajan aikin, tunda bikin ma kusa za asaka,
Dan ina ganinma harda Munneera za ahad’a,
“Munneera kuma mom wannan ‘yar yarinyar za aima aure ince bana ta gama secondary d’inta??
Mom tai dariya to ai ta isa auren ko, koda yake ku yaran yanzu kunfison auren manya sa’anninku, amma ai auren yarinya yafi komai dad’i, duk training d’in dakai mata dashi zata tashi,
“To amma mom aizaka sha shirme, dan auren ‘yar seventeen year ai aikine, ya tab’e baki koda yake mijin yaga zai iyane,
Mom tace kace bazaka iya auren ‘yar shekara 17 ba kenan,
“Tab haba mom aini ko ‘yar shekara 25 ma bazan auraba, inji da wad’ancan biyun dasuke neman sakamini hypotension, yanzu haka barosu nayi suna ‘yar zage zage daciwa iyayensu mutinci,to yanzu mom na auro ta uku ai sai wataran an kashe wata,
Mom tace to ALLAH ya shiryasu ya kuma kiyaye faruwar haka,
“Ameen mom”
“Ni bari nawuce gida ina da aikin dare yau,
To ALLAH ya tsare babana,
Ya kalli kausar da barci ya kwashe, oh kema kinyi barcin,
Mom tace aiyanzu zasu tashi tunda magriba ta kusa……..

Su mom sunje yola kwanansu biyu suka dawo,ban bisuba shiyyasa bansan misukayo ba.
(“”*”””””*<>*****<>””””””*””)

Bayan sati shidda da zuwan su mom yola dad ya kira dady,bayan sun gaisa dad yace babana, ranar juma’a d’aurin aurensu sadiq kai yaushe zaka wuce ne??

Dad nasani amma gashi ranar inada wata tiyata dazan yi karfe 6:am amma ina gamawa zan biyo jirgi,karfe 8:am zan fito inssa ALLAH, nama sanar dasu Sadiq d’in,
“To ai shikenan hakamma yayi ALLAH yakaimu”
“Ameen dad”
Dad yamik’o masa leda gashi kasa wad’annan kayan dan nasanka kana iya sawo k’ananun kayan naka nafama,
Dady yay dariya ya karb’a had’e dago diya sannan yatafi,
Koda yaje gida wanka yafarayi dan yaji ‘yan matan gidan shiru,da alama barci sukeyi kokuma yau shaid’ancin baya kansu ne oho,ledan da dad yabashi yad’akko yaduba farar shaddace riga da wando da babbar riga, tasha aikin surfani green sai hula itama green takalmi green,yay murmushi dad d’ina kenan wannan kaya haka saikace nine angon,yad’aukesu yasaka aledan ya kwanta ya huta kafin ‘yan dambennan su fara????????????????
Su mom sun wuce tun ranar laraba itada ‘yan biyu,dad kuma ranar alhamis da yamma yabi jirgi,

Dady kam sai ranar juma’a yabi ✈ safe, karfe 10: am jirginsu ya sauka ayola, sadiq da jafar sukazo tar barsa,suka run gume juna cikin tsananin farin ciki,dady yace brothers kunyi nisan kiwo saidai awaya????, ina safwan shi shine baizo tarba taba, yace abaka hakuri ana k’arasa masa wani aikine agidansa, dady yay dariya kaga anguna kunsha k’amshi, sadiq da jafar suka kalli juna suka tuntsire da dariya, sadiq yace zandai sha zuwa jibi insha ALLAH nida wannan d’an iskan yafad’a yana kaima jafar duka,jafar ya kauce yana dariya, dady yace kai tsaya waida gaske kakeyi harda jafar toko shi za abama munneera ne,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button