AUREN KADDARA KO BIYAYYA Complete Hausa NovelHAUSA NOVEL

AUREN KADDARA KO BIYAYYA Complete Hausa Novel

“Dady ya tsurama Munneerah idanu????????wai wannan ‘yar yarinyarce matarsa, yarinyar dasuka gama d’auka kwanan nan, jibima k’irjin bakomai dukda dai akwai gyale ajikinta.
Sadiq ya tab’ashi please oga in kayi hakuri jibi iyanzu tana gidanka.
Banza yay masa kamar bai jiba
” anty lubna tataso tana fad’in kai ‘yan kannena kunyi kyau sosai, takama hannun dady d’an k’anina please zokayi lallashi, k’ila idan kaine tayi shiru, tun d’azu take kuka yanzu haka zazzab’ine ajikinta da k’ar tayarda akaimata kwalliyar nanma.
“Dady ya daure yace anty batasha maganiba ne??

“Tak’i sha kasan Munneerah Allura???? da magani????????duk mak’iyantane”

Cikin tsokana jafar yace oga aje ayi lallashi, kuma shi kad’ai akace karka zarce, dariya sukasa, dady ya hararesa zan kamaka wlh zakasan dawanda kakeyi
Anty lubna taja hannunsa kaga k’yalesa in kun had’u kwayi…….

.
[8/16, 11:58 AM] ???? “???? ” D’????⭕Y????????: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ ????????_*
[8/16, 12:00 PM] ???? “???? ” D’????⭕Y????????: ????AUREN K’ADDARA????
????Ko BIYAYYA????

.

Page 06 «*****»

.

tana zaune zaune inda sukai mata kwalliyar, dayake d’annesa dasu, bayan anty lubna ta kaishi suka bar gurin itada anty Nafisa.
“A’a anty Nafisa ina zaku jene”
“Anty Nafisa tayi dariya dady kugama tafad’a suna tafiya”

Yajawo kujera ya zauna suna fuskantar juna, kanta nak’asa tana wasa da ???? zoben hannunta hawaye nazuba akumatunta, hancinta na shakar daddad’an k’amshin turarensa.

Yatsura mata idanu na tsawon minti biyu, cikin sanyin murya yace Munneerah ?
“Na’am. Ta amsa cikin muryar kuka”
“Miyasa kike kuka kuma ance kink’i shan magani gashi bakida lafiya??
Ta d’an d’ago idonta ta kallesa ganin ya tsura mata idanu yasata saurin maida kanta kasa,
“Yace ina saurarenki?
“Tace bakomai””
Shikenan bari nakira antylubna takawo miki abinci da magani.

Ya kalli inda su anty lubna suke hankalin su baya kansu sunacan suna hira da dariya,sai wasu k’alilan ke kallonsu irinsu marak’isiyya, su madeena, wad’anda su dadyn suke kallo danya birgesu dazai taya zasu sallama, kamar anty lubna tasan tajuyo tana kallonsu, hannu yasa ya kirata, anty lubna tazo ya akayi dady ?
“Anty akawo mata abinci da maga nin zatasha”
Anty lubna tace ina zuwa.

Saratu ta tab’a pii pii,kai anty pii gayen can ya had’u wlh tanuna dady,
Madina tace aiduk cikin amarannan Munneerah tafi kowa dacewa wlh, dukda angunan suna kama da juna, amma nata yafi kyau sosai, marak’isiyya tace saidai daga gani zaiyi miskilanci da girman kai,
Madina tace nikam banga laifinsaba dan ya had’u tako ina kinga kuwa dan yayi girman kai bashi da laifi.
Saratu tace kaini dazaice yana sona wlh yarda zanyi dan naji har zuciyata takamu da k’aunarsa.
Ai yakai asoshi cewar anty pii, gabad’aya sukasa dariya……

kairat k’anwar dady tana jinsu, gaskiya ‘yammatan nan suka fad’a, yayan su mai kyawune dan duk ciki family d’insu na uwa dana uba bawanda yakai shi k’yawu, dayawa mutane nacewa ya biyo kakansu na wajan uwa,ABDUL’AZIZ, wanda dadyn yaci sunansa, tacigaba da saurren hirarsu madina, dasuketa kod’a k’yawun yayanata.

Anty lubna takawo abincin da ruwa da magani ????????????,
Harzata tafi dady yace my anty jimana,ya nuna mata kujera,tazauna.
“Dady yace wai dan ALLAH anty waye yayi wannan hadd’in??
” Tace wana had’in?
“Nida Munneerah mana”
Su baffa mana
Yaja nummfashi, to su mom sun manta halin danake ciki agidana ne, kuma abin dubawa ananma, Munneerah ai bata isa aureba duka yaushe tagama zana (SSCE) d’inta ma.

Anty lubna tayi murmurmushi kawai batace komai ba.
Dady yacigaba inda had’in sukeso dasai su bari sai nan gaba inta k’ara girma jibe tafa dan ALLAH,
Anty lubna tace to ai ba matsala idan taje gidanka saika barta tak’ara girman, yace anty lubna dan ALLAH ga wani taimako daza kimini,
Tace ina jinka,
Mizai hana kibama su dad shawara abarta sai nan da shekara uku saita tare sannan tad’an k’ara girma, amma yanzu shekara 17 ai tayi k’arama.

Anty lubna tayi dariya kaini dady baruwana kaji yara nawane kamarta akayima aure suka zauna, kai harma wad’anda basu kaitaba jeka Ruga kagani,ko d’iyar baffa shehu zuwaira nawa take ba Munneerah ta girmeta bama, amma ga tanan harda yaronta da wani cikin,bare Munneerah shekara 17.

Hawayen Munneerah suka k’aru to tun yanzuma kenan inaga ankaini gidansa, saikace angaji da ita, damma yarainata ita yakece ma yarinya bata isa aureba,zaiga yarinta ganin idonsa indai nice, mutum sai miskilancin tsiya,
Maga nar anty lubna ta katseta k’anina kaga mu binne wannan maganar anan gurin kafin su baffa suji suci k’aniyarka wlh.

Ta mik’e kasata taci abincin muna jiranku tayi tafiyarta
Dady yabita da kallo,waishi miyasa kowa yakasa fahimtarsa ne……..

da sauri yajuyo danjin kukan Munneerah, jiyayi tamkar ya nausheta???????? dan haushi, shi bayyi kukaba ma sai ita da aka kakabamasa, amma sai ya b’oye b’acin ransa,cikin taushin murya yace kinga Munneearah daina kuka, kinga kanki zaiyyi ciwo dama gashi bakida lafiya,nan ya lallab’ata taci abinci,dak’yar yasamu tasha maganin,sannan sukaje akayi hotunan.

***************
Aranar da daddare akakai amare d’akunansu, Munneerah kuma sai gobe za akawota kano, tabi gayyar ‘yankai amare batare da kowa yasaniba, saida taje gidan kowa’gidan Ni’ima ne k’arshe, tanacan suna magana da Ni’ima motoci suka tafi akabarta sai masu kwana kawai,
Afirgice tadawo cikin gidan tana kiran anty Ni’ima!! Nashiga uku motocin duk sun tafi!!!
“Kai dan ALLAH”
“Wallahi kuwa, nabani idan akaduba ba aganniba”
“Naji kamar k’arar mota jeki gani”

“Su dady suka fito daga motar suna dariya, dady yad’ago kai zaiyi magana, karaf idonsa akan Munneerah tafito tana dube dube, azuciyarsa yace illar auren yaran kenan,Sadiq ya tab’osa kai malam mikake kallone??
“Yace Munneerah!!
“Harsuna had’a baki wajan fad’in Munneerah kuma, suka kalli inda yake kallo,
Cikin mamaki Sadiq yace to ubanwa ma yakawota nan,
“Kirata yayi cikin fad’a,
“Cikin tsoro tazo dantasan ya Sadiq sarai,
“Ubanwa ya baki izinin zuwa nan, cikin rawar murya tace nabiyo ‘yan kawo amaryane kuma sai suka tafi,
Ya harareta da sanin wa kika fito?
Tace bakowa.
Yad’aga hannu zai mareta jabir yarik’e hannun, kai my man, saurara matar aurece fa, to dan matar aure ce baza’a hukunta taba.
“Za’a hukunta ta amma mijinta ne keda wannan ikon”
Dady dai baice komaiba yana tsaye jingine da mota yana kallonsu.

Sadiq yadaka mata tsawa kafin nafara jibgarki anan kishiga ki had’o yanaki yanaki kizo mutafi dan can unguwar zamu koma, in kuma bahakaba yay kwafa, tasan halinsa zai iya zaneta, tace ba abinda zan d’akko,
Ta d’an saci kallon dady ya d’aure fuska tamau ko kallon inda take yak’iyi,

Suka shiga mota Sadiq yana tuk’i jafar na gefensa, sai safwan abaya daga hannun haggu, dady yashiga tsakkiya Munneerah na gefen dama tawani takure jikinta ajikin mota, shikam dady ko kallo bata isheshiba.
Suka ajiyeta agida saida tashiga suka wuce masaukinsu……

KANO, kano dai basusan ahagalin da ake cikiba, sunsan dai ana biki agidan su mom, dan abban Sadiq baffa Muh’d saida yagayya cesu, amma suka kawo uzirin suna da ayyuka ranar,
Sai bayan an d’aura aure wani magul maci yakira abban ikilima, wai ya baigansu wajan d’aurin auren d’ansuba Abdul’aziz? abban ikileema yace a’a ai banda Abdul’aziz yaran alhaji muh’d ne zasuyi aure,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button