AZIMA DA AZIZA Macizai Ne 1
Tana kwance a gadon kara, rabin jikinta macijiya sai juyi take yi kanta a hargitse, Aziza ta shigo da sallama ko amsawa Azima bata yi ba, Aziza ta ce
“Ba ki jin Baffa na kiranki ne?”
“Mtswwwww! Na ji mana, tunda dai ni ba kurma ba ce! Je ki ce ba zan zo ba!” a fusace Aziza ta sa hannnu ta janyo wuyar Azima ta ce
“Wallahi! Wallahi! Wallahi! Kinji na rantse miki ko? To sai kinje, kuma dole ki ba wa Baffa amsar tambayoyin da zai miki, za ki tashi ne ko sai na b’ace dake a dakin nan na wujijjigaki!?” Aziza ta karasa maganar idonta da fatar jikinta suna canza kala, ganin haka yasa Azima miƙewa fuuuu ta fice, rufe ido Aziza ta yi ta dawo dai-dai sannan ta bi bayan Azima, a tsaye ta sameta Baffa na tuhumarta inda ta samo zaren sakar dana, cike da rashin tsoro da rashin kunya ta ce
“A inda ake samu na samo!”
“AZIMA!!!” Aziza ta faɗa a tsawance ta yi kanta dan ta kai mata mari, da sauri Hajja ta ja hannun Aziza sannan ta fashe da kuka, murguɗa baki Azima ta yi ta fice a gidan ma gabadaya, Baffa kuwa suman tsaye ya yi, Aziza kuma tana lallashin Hajja dake kuka.
Cikin kuka Hajja ta ce
“Wai ni meke shirin faruwa dani ne kam? Me yasa Azima ta zama haka? Kwata-kwata yanzu bata shakkar gaya mana magana! Aziza dame ku ke so naji? Idan ba ki taimakawa yar uwarki ki gyara mata halinta wa zai iya yin hakan?” Hajja ta ci gaba da kuka, Baffa kuma bukka ya shige ya zube a bakin gadon kara jikinsa na rawa, hakika jejin lore ɗan adam baya shiganta ya fito lafiya, duk ɗan adam din da ya shiga jejin lore to sunansa gawa! Shi ma sanadiyyar shigarsa jejin lore ya yanko zaren saƙar dana sadda zasu gwabza da Banju ne, rass! rass! rass! gaban Baffa ya bada nan zufa ta shiga tsatstsafo masa ta ko wace kusurwar gashi dake gangar jikinsa, a fili ya ce
“AZIMA BA MUTUM BA CE! TAYA ZAN GWADATA NA GANE HAKAN DAN NA WARKARWA ZUCIYATA TANTAMA DA ZARGI!? INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN! YA ALLAH KASA KAR ABUN DA NAKE KWANA NAKE TASHI DA SHI YA ZAMA GASKIYA!” Baffa ya karasa maganarsa hannunsa a sama hawaye na gangarowa.
Da kyar Aziza ta ɗaga Hajja ta shigar da ita bukkarta tana lallashinta amma ina Hajja ta kasa tsaida hawayenta, kasa juran kukan nata Aziza ta yi ta miƙe a hankali ta fita zuwa randar kasar dake tsakar gidansu ta ɗibo ruwa a kwarya ta bude bakinta ta zuba abu a ciki sannan ta koma ta ba wa Hajja, ƙin karba Hajja ta yi ta ci gaba da kuka, Aziza ta ce
“Dan Allah Hajja kiyi shuru ki daina kuka, kin ga gidan nan bamu da sauran ganyen magunguna balle na haɗa miki ki sha idan kanki ya fara ciwo, zan yiwa Azima magana ga ruwan nan ki sha zuciyarki ta yi sanyi” da kyar Hajja tasa hannu ta karbi ruwan ta sha, tana shan ruwa ko minti uku bata yi ba, ta zube a jikin Aziza, hawaye ne masu zafi sosai suka zubowa Aziza a fuskarta a fili ta ce
“Kiyi hakuri Hajja ki yafe min ba zan iya ci gaba da kallon kukanki ba, baccinki shine mafi alkhairi, tun a yau da ba ki san su waye mu ba kina irin wannan kukan ran da kika sani za ki hadiyi zuciya ne Hajja? Ina ba zan bari hakan ta faru ba! Ba zan iya rasaki ke da Baffana ba! Zan ci gaba da boyewa tare da dakatar da yar uwata, ko da kuwa zamu kashe juna” Aziza ta karasa maganarta tana sake rungume Hajja, ta sha kuka sosai kafin ta gyarawa Hajja kwanciya ta fita.
sallama ta yi a bukkan Baffa, da sauri Baffa ya share hawayensa ya ce
“Shigo Aziza” cikin natsuwa ta shigo,zama ta yi kusa da kafarsa ta ce
“Baffa kuka kake yi?” girgiza kai Baffa ya yi ya ce
“A’a ba kuka nake yi ba Aziza” shuru Aziza ta ɗan yi kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ce “Baffa
ina so na san meke ƙunshe da wannan zaren da Azima ta saƙa”
“Me kuma kike so ki sani bayan wanda na gaya miki Aziza? Hatsarin da ke cikin wannan zaren ba zai faɗu a baki ba tsananin yawanta, da ace za a dauki kwaya ɗaya tak! A jefata a cikin rafin jimulo, ina mai tabbatar miki duk wanda ya sha ruwan wannan rafi zai mutu!” dam! dam! dam! gaban Aziza ya bada nan ta shiga saƙe-saƙe a ranta tare da tunane-tunane, shin wa Azima take son kashewa da wannan zaren? *”BAFFA”* wata zuciyar ta bata amsa da sauri ta miƙe tsaye a firgice tana zare ido tare girgiza kai gami da fadin
“A’a karya ne! Ba zai yu ba! Ba zan bari hakan ta faru ba!” ganin yadda ta ruɗe lokaci ɗaya ne yasa Baffa tashi da sassarfa ya kama hannunta ya zaunar da ita ya ce
“Aziza natsu mana! Tsaya…kina ji? Menene? Gaya mini? Miye ba za ki bari ya faru ba?” kuka Aziza ta fashe da shi mai tsanani tana kwanciya a jikin Baffa, sosai hankalin Baffa ya tashi yana tambayar Aziza meke faruwa!.
Cikin kuka Aziza ke faɗin
“Me yasa! Me yasa! Me yasa!” da kyar Baffa ya shawo kan Aziza ta yi shuru ta daina kuka, Baffa ya ce
“Aziza meke faruwa ki gaya min gaskiya karki boye min komai, ni mahaifinki ne” saita natsuwarta Aziza ta yi ta ce
“Baffa, haihuwarmu ta yi muku rana?”
“Subhanallahi! Wannan wace irin magana ce kike faɗi Aziza?”
“Baffa kukan da Hajja ta yi a kan Azima dazu bazan sake bari hakan ta faru ba, ba zan sake bari ba!” ajiyar zuciya Baffa ya sauke,ita kuwa Aziza ta yi hakane dan kawar da shakku a zuciyar Baffa, shuru na ɗan wani lokaci ne ya ratsa wajan kafin Aziza ta ce
“Amm Baffa? Taya za a lalata zaren saƙar danar da yake hannu Azima?”
“Wannan ba shi bane abunda nake tunani Aziza, yadda aka yi Azima ta samu zaren nake tunani”
“Amm amma Baffa ta ce inda ake samu ta samu! Ya matsayin hatsarin jejin lore yake?”
“Aziza faɗin hatsarin jejin lore ba zai yu ba, dan yafi karfin ki fasalta shi da komai, taya har Azima zata shiga wannan ƙasurgumin jejin ta fito tana yar adam? Wannan shine tambayar da nake yiwa zuciyata amma na kasa samun amsa, ban san meke shirin faruwa da mahaifana ba”
“Baffa ka rabu da maganar Azima, kasan wani lokaci ba hankali gareta ba, yawwa kuma Baffa na mance ne ban gaya maka ba, Azima kamar tana da aljanu! Dan cikin dare sai na dinga ji kamar tana ta buge-buge da sambatu ita dayanta, Baffa na tabbata su ne suke saka ta rashin kunya,kuma ba mamaki karya take yi ba ita taje jejin lore ba, sai dai idan aljanun ne suka je suka kawo mata, ka yarda dani Baffa gaskiya nake gaya maka” Aziza ta karasa maganarta tana riƙo hannun Baffa, jinjina kai Baffa ya yi ya ce
“Kenan wani irin aljanu Azima ke da shi? Wanda har zasu iya kawo mata zaren saƙar dana? Me zata yi da shi? Kuma har tasan yadda ake saƙata?” zare ido Aziza ta yi ta hau rawar murya tare da in’ina
“Amm….eh…..umm….ohh…Baff….Baffa ….kar…ka…da..mu…da…Azima…ni nan zanji da ita, zan mata hayaƙin aljanu zata warke da yardan Allah na san ka yarda dani ko Baffa?” murmushi Baffa ya yi yana jin kaunar Aziza a cikin ransa, hakika ba zai ce baya son Azima ba tunda ita ma ƴarsa ce, amma aka ce mai kyautata maka shi ne wanda yake rayuwa a cikin zuciyarka,
“Na Yarda da ke Aziza, Allah ya miki albarka” murmushi Aziza ta yi ta miƙe tsaya tare da fadin “Amin Baffana” fita ta zo yi a bukkan har ta duƙa sai kuma ta ɗago tare da juyowa ta ce
“Amm Baffa? Baka faɗa mini abunda zai iya lalata zaren saƙar dana ba?”
“Aziza sanin wannan ba sauki garesa ba, har sai an koma jejin lore, jejin da mutane ba su shiga”
“To amma Baffa kai a garin yaya ka shiga ka fito?”