AZIMA DA AZIZA Macizai NeHAUSA NOVEL

AZIMA DA AZIZA Macizai Ne 1

” *NI MACIJIYA CE!*” Aziza ta bada amsa, wannan halittar ya ce
“Ke ba iyakar macijiya ba ce, akwai wani sirri a tattare dake, dan haka ko ba mu baki makarin zaren saƙar dana ba,kaifin gubar dake jikinki zai iya ƙonasa! Amma kasancewar sau daya tak! Muke bada alfarma zamu baki taimako guda daya, zamu ƙara miki karfi, da kinje ki hurawa zaren wuta ta idon ki zai ƙone ƙurmuss! Ga wannan” ya faɗa yana daukar wata kyakkyawar dutse mai cike da hasken gaske ya hura mata shi ya shige ta goshinta, abun na shiga jikin Aziza sai da ta girgiza ta yi kamar zata faɗi amma ta yi iyakar iyawarta bata faɗi ba,dama tana tsaye ne ita ba a sama ba ita ba a kasa ba, abun na shiga jikin Aziza nan ta kalli fatar jikinta ta ga yana sab’ulewa har yana komawa wata fari-fari, kafin ta gama dawowa hayyacinta tuni ta fara rikiɗewa tana komawa macijiya, nan ta zama wata shirgiɗeɗiyar macijiya mai cike da abun tsoro, nan aka hau guɗa wanda yasa duk jejin lore ya dauka, kafin wannan katon halittan ya ce a maidata gida lafiya, nan suka fizgi Aziza,wacce tunda suka fizgeta bata kara sanin ina kanta yake ba, sanyin asuba ne ya farkar da ita,tana buɗe ido ta ganta a kofar gida, saurin tashi ta yi tana karkaɗe jikinta, nan abunda ya faru a daren jiya ya hau dawo mata, lallai kam jejin lore ba jejin mutane bane, da kyar ta saita kanta jin yadda jikinta ke mata ciwo, da sanɗa ta shiga cikin gida, tana shiga Baffa na fitowa daga kewaye ya yi alwala zai je masallaci, ya ce
“Aziza har kin farka? To shiga ki tada Hajjarku sannan ki tashi Azima su yi sallah”
“To Baffa” Aziza ta faɗa ta shiga ta tada Hajja sannan ta fito ta shige bukkarsu, ko da ta shiga bata gan Azima ba, a ranta ta ce ko ina taje oho mata, kayanta ta ajiye sannan ta fito ta yi alwala ta yi sallah ta jima tana addua sannan ta tashi.

Abu na gaba da zata yi shine daukar zaren saƙar dana taje ta kona shi, to amma abun tambayar a nan shine a ina Azima ta ajiyesa? “zaki iya dubawa ki gani ta tafin hannunki ai an baki karfi a daren jiya a jejin lore” wata zuciyar ta bata amsa da haka, da sauri ta buɗe tafin hannunta na dama tasa hannun hagunta tana shafe tafin hannun daman tare da lumshe ido, nan ta ga ashe ma a cikin kayanta Azima ta ajiye zaren saƙar danar, tasan tabbas Aziza sai ta binciko,kuma duk bincikenta ba zata duba kayanta ba tunda ba zata yi tunanin zata saka a ciki ba, da sauri Aziza ta buɗe ido tana fadin “lallai Azima ke shaiɗaniya ce! A cikin kayana kika ma ajiye?” da sauri ta wargaza kayanta ta dauki zaren wanda Azima ta saƙa shi ya yi tsayi, lullubi ta yi ta boyesa a cikin mayafinta ta fito a hankali dan gari ya yi haske, har ta kai bakin kofa zata fita ta ji Hajja na kwala mata kira da gudu ta fice dan bata son ta rasa wannan damar, jejin kwana taje ta ajiye zaren bayan ta duba babu kowa a wajan, da ido ta kalli zaren yayinda idon nata ya koma jajur kamar garwashin wuta,nan wani jar wuta ya fito daga idonta ya kama zaren,nan zaren ya kama da wuta har yana wani irin ƙara passpasspass! Da sauri Aziza ta ja da baya, nan zaren ya ƙone ƙurmuss! tokar Aziza tasa hannu ta shafe shi ya b’ace nan ta sauke ajiyar zuciya mai karfin gaske tare da fashewa da kuka tana zubewa a kan guiwowinta tasa goshinta a kasa ta yi sujjadar shukur, ta yi tsammanin ta kashe wannan bala’in bata san wanda yake shirin ci ba.

 

????????????????

*AZIMA.*

tun fitarta a gida tana kwance a kan bishiya a macijiya tana jiran isowar Innu maciji, sai bayan da garin Allah ya fara wayewa ta ga wasu yan matasan samari biyu sun zo sun tsaya a jikin bishiyar da take kwance, dayan ya ce
“To ma ban da abun Mai Unguwa taya zamu iya kare Innu Maciji da za a wani turo mu dan mu tarbesa”
“Nima dai abun da na gani kenan” saurin zare ido Azima ta yi ta kallesu da kyau sannan ta yi murmushi
“Ohhho kenan yan fadar mai unguwa ne! Aiko su ya yi, shin na bar ma su bada labari ne? Idan kuma suka tona min asiri fa?” nan ta haɗe rai tare da sulalowa daga bishiyar ta zama mutum, hannu ta miƙa sama sai ga kwaryan nono, murmushi ta yi ta buɗe kwaryan wanda yake cike da nono kindirmo fari sol abun sha’awa ta watsa dafi a ciki sannan ta gyara mayafinta tayi lullubi ta rufe fuskarta ta nufi inda suke, cikin karairaya ta musu sallama, su kuwa sun ga ƴar budurwa har rige-rigen amsawa suke yi,cikin harshen fulatanci suke magana ta ce musu
“Ga fa nono, daga ina ku ke da sassafen nan haka ku ka zo ku ka zaune a tsakanin yanki?”.

 

“Wlh mai unguwa ne ya aiko mu, kin san ai masifar da ake fama da shi a yankin nan na macizai, to yau Innu Maciji zai zo wanda yake yankin ja’i shine mai unguwa ya aiko mu dan mu tarbesa,kin san kwanaki da Jarman macizai ya zo gawarsa kawai muka gani, kai duk wannan macijin da yake kisan nan ko take kisan nan ko humm idan Innu Maciji ya zo zan ce ya bani dama na kashesa da hannuna” cije baki Azima ta yi ta ce “da gaske?”
“Aradun Allah kuwa! Sanda zan sha na dinga roɗewa macijin kai har sai ya koma ga Allah” damƙe hannu Azima ta yi jin yadda ranta ya b’aci zuciyarta na tafasa amma ta daure tare ta k’wak’ulo murmushin mugunta ta ce
“Ai kuwa nima ina da wasu sirrika a kan macizai, kafin na gaya muku ga wannan nonon ku sha” ta fada tana tura musu kwaryan, dayan ya ce
“Allah sarki! Ashe kin san yau da yunwa muka tashi, ga shi kafin mu karya karin kumallo aka turomu yanki” murmushi kawai Azima ta yi ba tare da ta sake magana ba, nan suka buɗe nonon nan suka hau sha, sai da suka shanye tass har suna mata godiya, Azima ta kyalkyale da dariya tare da yaye mayafin fuskarta nan blue eyes dinta ya bayyana, tare da rikiɗewa ta hau komawa macijiya, tsananin tsoro da firgici yasa suka kasa motsi illa junansu da suka rungume gagam!, bayan Azima ta zama macijiya sannan ta koma ta zama mutum ta matso kusa dasu ta duka ta ce
“NI CE AZIMA MACIJIYA! WACCE DUK KASHE-KASHEN DA AKE YI NI NA KE YI! NI! NI! NI CEEEE! SANNAN KU TAKU TA KARE DAN DAGA NAN BABU WANDA ZAI MOTSA A CIKINKU, DAN KUN SHA GUBANA” tana gama faɗi kuwa suka hau aman jini, su na riƙe wuyarsu tsananin azaba, jini na fita ta baki da hanci, suna birgiman fitar rai Azima na ta sheƙa dariya, da haka har suka daina motsi, bayan sun mutu ta kwashesu ta maida su gefe ta ajiye sannan ta ci gaba da tsumayin jiran isowar Innu Maciji, ba jimawa sai ga shi nan kuwa ya yanko a kan dokinsa, daka gansa ka ga basamudan bafulatani mai ji da kansa, wuyarsa rataye da maciji, Azima na ganinsa ta hau murmushi tare da gyara lullubinta ta zo ta tsaya a kan hanya, (ga Azima ga Innu Maciji, ya zata kaya?).

Kamar yadda ta yiwa jarman macizai haka ta yiwa Innu Maciji, shi ma kalar tambayar da jarman macizai ya mata shi ya mata
“Mutum ko aljan?” murmushi ta yi tare da fadin
” *RUWA BIYU!*” sannan ta juyo gami da yaye mayafinta, Innu Maciji na ganin kwayar idonta nan ya sauƙo da sauri tare da zare takwabinsa yana fadin
“Keeeee!” haɗe rai ta yi ta ce
“Ajali ya kiraka!”

Gyara tsayuwarsa ya yi ya ce
“Kina tunanin zan mutu a hannunki ne?”

“Ashe dai baka cika ba! Tunda har ba zaka iya bambance wacece ni ba, amma ina so ka sani ba zaka shiga yankin nan ba,kamar yadda ba zaka koma yankinku ba” tana gama fadi ta yi kansa tare da komawa macijiya,ganin haka yasa Innu Maciji saurin b’acewa dan ya ga da karfinta ta nufosa, Azima gani ta yi Innu Maciji ya b’ace yasa ta koma mutum tana ta kalle-kalle,ji tayi an tokareta ta baya nan ta fadi kasa ta bugu tukunna Innu Maciji ya bayyana yana dariya yana kallonta ya ce
“Ba mamaki baki da labarin waye Innu Maciji ko? Humm ni ne nan mai fada da aljanu da mayu, sabida shaharata yasa sadda aka raba kambun girmamawa ni ne nan nayi na daya, dan haka sai na baki wahala! Na galabaitar dake sannan na daukeki na kaiki wajan mutanen yankinku na nuna musu ke!” yana gama fadin haka ya zaro wani dogon igiya ya naɗe Azima da shi, ya hau bugunta tare da watsa mata wani ruwan magani wanda da ya watsa mata zata kurma ihu, fatar jikinta ya koma blue sabida karfin dafinta ne ke raguwa, haka Innu ya ci gaba da ganawa Azima azaba wanda izuwa yanzu fadin halin da take ciki b’ata lokaci ne, sai da ya ga bata iya motsin kirki sannan ya kyaleta yana shirin daukarta ya ɗorata a dokinsa yaje ya nunawa jama’ar yankin kwana, har ya dauketa Azima ta buɗe ido a galabai ce, a ranta ta ce
“Yanzu idan aka kaini Baffa da kansa na san zai kasheni! To ina kuma daukar fansata!? Inaaa ba zan bari hakan ta faru ba! Ba zan bar yankin nan ba, ba tare da burina na son maida yankin kwana maƙabarta ba, sannan ba zan bari na mutu ba tare da na shiga cikin gari ba” tana gama fadi ta yanki gashin kanta ta haɗiye ta rintse ido ta mamayi Innu Maciji wanda ya sab’ata a wuya yana shirin ɗorata a kan doki, nan ta zama macijiya tasa jelarta ta shaƙe wuyar Innu Maciji, shaƙa bana wasa ba, sannan tasa hannu ta b’abb’alle guru da layoyin dake jikinsa ta zubar, sannan tasa ihu ta koma macijiya gaba dayarta ta hau sarensa,duk yadda Innu Maciji ya so kwacewa ina hakan bai samu ba, Azima sai da ta ga Innu Macijiya ya zube kasa babu rai a tattare da shi sannan ta sulale gefe ta koma mutum tana sauke ajiyar zuciya idanunta jajur, kallon Innu Maciji take yi na wasu lokuta sannan ta ja samari biyun da ta kashe ta haɗa da innu maciji sannan ta bar wajan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button