AZIMA DA AZIZA Macizai NeHAUSA NOVEL

AZIMA DA AZIZA Macizai Ne 1

 

????????????????

Bayan Aziza ta koma gida aikin gabanta ta ci gaba da yi, ko kaɗan bata tambayi ina Azima take ba, nan ta yiwa Hajja shara da girki sannan ta hau ɗibar ruwa, sai da ta cika babbar randar kasarsu sannan Hajja ta ce
“Ayye Aziza ba za ki huta ba?” murmushi ta yi ta ce
“Hajja hutuna shine naga Allah ya rabani dake lafiya” Hajja ta yi murmushi jin dadi tare da sa mata albarka,nan suka zaune hira suka shantake sai zuwa anjima Hajja ta ce
“Wai ni ina Azima ne kam?”
“Wa ya san mata” cewar Aziza,
“Bata rafin jimulo ne?”
“Ni dai wlh Hajja har na gama jido ruwa ban ganta ba, da ace tana can dana ganta”
“Ikon Allah!” Hajja ta fada, Aziza ta ce
“Hajja miye amfanin damuwa a kan Azima ita da ba jaririya ba,duk inda taje zata dawo ai” Hajja ta ce
“Hakane” suka ci gaba da hirarsu, sai zuwa can Aziza ta ce
“Hajja wai ina Baffa? Tun fitarsa sallar asuba fa bai dawo ba ga shi yanzu ana neman lokacin azahar” Hajja ta ce
“Oh! Kinga na mance ban gaya miki ba, ai suna can fadar sarkin fulani, Chubaɗo”

“Wani abun ake yi ne?” Aziza ta tambaya cikin rashin sani tana kallon Hajja, Hajja ta ce
“E lafiyar kenan, kin san ai an yiwa yankin ja’i aiken wasikar taimako, har Innu Maciji ma ya ce zai zo yau, to jiran Baffan naku nake yi idan Innun ya iso zai zo ya gaya mana muje can fadar sarkin fulani”

 

Wani firgita Aziza ta yi ta miƙe tsaye ta ce
“Hajja yaushe aka yi aike yankin ja’i har Innu Maciji yace zai zo?” ita ma Hajjar miƙewa ta yi ta ce
“Aziza lafiya kuwa?”
Kama hannunta Aziza ta yi ta ce
“Hajja tun yaushe ne Azima bata gida?” Hajja ta ce
“Ban sani ba Aziza, dan ni tun wayewar garin yau ban ga Azima da idona ba, ba shine nake tambayarki ko kin ganta rafi ba”
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!” Aziza ta faɗa tana jan mayafinta zata fita Hajja na tambayarta ina zata je, har ta kai bakin kofar zanar gidansu bata kai ga fita ba suka yi mugun karo da Baffa wanda ya shigo a fijajan hankalinsa a tafin hannunsa, da sauri Hajja da Aziza suka tare Baffa,ganin yanayin da Baffa yake ciki yasa Aziza fara addua a ranta Allah yasa dai Azima ba Innu Maciji ta kashe ba,idan kuwa ta kashesa tabbas ta b’allowa yankin kwana yaqi.

Da sauri Aziza ta ɗibawa Baffa ruwa ta kawo ta ba wa Hajja, Hajja ta karba ta ba wa Baffa wanda da kyar ya yi kurbi daya wanda ya taho masa da kuka,ganin haka yasa ita ma Aziza ta fashe da kuka, Hajja na ganin Aziza ta fashe da kuka ita ma tasa kuka,nan aka rasa mai rarrashin wani,da kyar cikin kuka Aziza ta kama hannun Baffa tana faɗin
“Dan Allah Baffa ka gaya mana meke faruwa!”

” *AZIZA? JUMALA! AN KASHE INNU MACIJI!! DA MASU TARBAN BAƘIN SHIGOWA YANKIN KWANA SU BIYU!*”

BAFFA na fadin haka Aziza ta sake hannunsa tare da yin zaman yan bori!
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! mai Azima take son zama?” kasa motsin kirki Aziza ta yi illa komawa da ta yi tana bin Baffa da Hajja da suke kuka da ido, sai zuwa can Hajja ta ce
“Ya aka yi da gawar har an binne su ne?” Baffa ya girgiza kai ya ce
“Ba zamu iya hakan ba, ana ganin gawar ba shiri Arɗo da Chubaɗo da Ori suka ce garkuwan fulani da Galadima da Liman da mutum biyar a fada su tafi yankin ja’i da gawan, yanzu Allah ne kadai yasan me zai faru an kashewa yankin ja’i Innu Maciji, taya zasu fara fuskantarmu su fahimce mu? Innalillahi wa inna ilaihirrajun!” nan suka ci gaba da jajinta lamarin inda a karshe Hajja da Baffa zasu fita Hajja ta ce
“Aziza zo muje” murya can kasa wanda take ji da kyar ma take maganar ta ce
“Hajja kuje zan zo”
“To amma kiyi lullubi kafin ki fito anani ko?” Aziza ta gya ɗa kai, kanta a sunkuye, Hajja da Baffa suka fice,dan Aziza tana ji ba zata iya tafiya ba jin kamar kafafunta basu gangar jikinta.

Bayan fitar su Hajja da Baffa kamar da rabin awa sai ga Azima ta shigo babu sallama kamar an wurgota ko kallon Aziza ba ta yi ba, da ido Aziza ta bi Azima tana ji kamar ta haɗa musu guba su sha su mutu ko duniya zata zauna lafiya.

Azima na shiga bukka ta hau dariya kasa-kasa gami da faɗin
“Innu Maciji na kashesa! Yau kuma *MAGAJI BAWA* zaka mutu! Sauran mutanen yankin nan za a kashesu ne idan tarzoma ta tashi, dan nasan yankin ja’i ba zasu hakura ba, ta fada tana murmushi tare da zura hannu dan ta dauko zaren sakar dana da ta saka a kayan Aziza amma ta ji wayam,ido buɗe take warware kayan Aziza amma bata gani ba,kamar mahaukaciya haka Azima ta fito ta zo ta tsaya a kan Aziza
“Ke Aziza Magaji! Nayi ajiya a kayanki amma ban gani ba” dago kai Aziza ta yi ta kalli Azima sannan tasa hannu ta share hawayenta ta miƙe a hankali cikin sanyin murya ta ce
“Me kika ajiye a kayana?”
“Mtswww! Bana son rainin hankali Aziza! Ki bamu abuna!?”
“Wani abunki?”
“Zaren sakar dana da na ajiye a kayanki” Aziza ta jinjina kai ta ce
“Owoohhh zaren dana? Na ƙonasa!!” wani zabura Azima ta yi tasa hannu ta shaqi wuyar Aziza ta ce
“Kin ƙona fa kika ce!? Ke meyasa baki son mu dauki fansa ne kam!? Me yasa ba zaki bari na rama mana abunda aka mana ba! Kin ƙonasa!? Aziza ke mahaukaciyar wace al’karya ce? Na ce ke…..” ture hannunta Aziza ta yi daga wuyarta sannan ta kwalfa mata mari ta ce
“Kin kashe Innu Maciji da samarin fada mutum biyu! Akan me!”

Ɗagowa Azima ta yi ta wanke Aziza da mari ita ma, ta kuma shaƙe mata wuya
“Kin min asara! Shin kin san da cewa jejin lore sau daya tak suke ba wa mutum abu? Kuma dole da zaren sakar dana zan iya kashe Baffa me yasa! Aziza na ce me yasa! To wlh kin jawowa kowa, yau kisan da zanyi ban ga mai dakatar dani ba!” tana gama faɗi ta zama macijiya ta sulale ta fice, ganin haka yasa Aziza ita ma ficewa da gudu.

 

????????????????????

 

COMMENT AND SHARE
BY MOMYN AHLAN BAIWAR ALLAH MASOYIYAR ANNABI MUHAMMADU S,A,W,????????????
[3/21, 12:31 AM] Fatima: ????????????????????????????????????????

????✨ *AZIMA DA AZIZA*????✨
(???? _Macizai ne_????)

MALLAKAR.

*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)_

_Follow me on wattpad,@Fateemah’0_

????????????????????

*STILL FREE..*
????️==1️⃣9️⃣↪️2️⃣0️⃣

 

Amma bata ga inda Azima ta yi ba, rafin jimulo ta je amma ba Azima bare mai kama da ita, hankali tashe Aziza ta hau neman Azima amma bata ganta ba, jejin kwana ta nufa ta hau dubata amma bata ganta ba, riƙe kai Aziza ta yi tare da furta “YA ALLAH! dabadin ace kisan kai haramun bane babu abun da zai hanani ban kashe kanmu a yau ba kowa ya huta, wannan wani irin bala’i ne haka? Ya Allah ka yaye mana, Allah ka bani mafita ka nuna min haske, Ya Allah ka nuna min hanya! Ya Allah ni dai bana da masaniya a kan fansar da Azima take dauka, dan a iya sanina banga wanda ya mana laifin komai ba, Ya Allah idan ita haka halinta yake Allah kai kasan yadda zakayi da ita, Allah ka taimake Baffana da Hajjata da jama’ar mahaifata! Ya Allah ka karesu daga dukkan sharri!” Aziza ta karasa adduar hawaye masu zafi suna wanke mata fuska tare da jinginuwa a jikin bishiya, wani nishi taji na tashi a bayanta da sauri ta buɗe idonta da ta lumshe tana waige daga ina nishin ke fitowa, taji ashe ta bayan bishiyar ne,saurin leƙawa ta yi nan ta iske wata budurwa kwance bakinta sai jini ke bulluƙowa, cike da tashin hankali Aziza ta karasa ta ɗagota, tana dudduba meyasa meta,goshinta ta kalla ta ga bakin maciji wanda yake sara ne na Azima, ihu Aziza ta yi tana ajiye kan budurwar a kasa ta tashi da sauri tana ja da baya ta kuma sakin wani mahaukacin ihu tana furta “AZIIIMAAAAAAA!!!?” da gudu ta bar wajen dan babu taimakon da zata iya yiwa budurwar dan kuwa gubar ya shige mata jiki sosai dan harta idonta da tafin hannunta sun koma blue.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button