AZIMA DA AZIZA Macizai Ne 1
“Ga ki kuwa babbar mahaukaciya!” Azima ta faɗa tana dagowa a fusace.
“Dan Allah fadan ya isa haka!” Hajja ta katsesu,
“Kuyi ta addua kawai Allah ya bamu mafita yafi wannan fadar naku” ko uhum basu kuma cewa ba.
????????????????
Da washe gari kamar yadda sako ya iskesu haka kuwa ta kasance inda yankin ja’i da yankin jimo da yankin tudu sukayi cincirindo sun zo yaƙar yankin kwana, amma abun mamaki babu wani daga yankin kwana da ya dauki makami, abun ya basu mamaki, Arɗo shine wanda ya fito ya fara magana kasancewarsa Babba, tsohon bafulatani mai dattako
“Mu ba zamuyi yaƙi daku ba, idan har kuna so duk ku sa takwabi ku kashemu! Har ga Allah munyi imani wannan ita ce kaddararmu! Bamu kashe Innu Maciji ba, a ranar da aka kashe Innu muma munyi rashin mutane a yankin nan har mutum sha huɗu, haka ma jarman macizai, sannan sarkin fulanin tudu bamu aikata muku komai ba kawai neman fitina kukeyi,idan kuma yaronka da aka kashe a yankin nan ne laifi ya aikata aka masa hukunci, na rantse da wanda ya busamin numfashi idan har aka samu ɗan wani yankin kwana da laifi makamanciyar wanda ɗanka yazo yankin nan ya aikata wlh mun yarje muku ku fille kansa ku kawo mana kamar yadda mukayi, ba a barin laifi a ɗoran kasa, dan ba a san mai zai kuma aikatawa a gaba ba, mu sabida muna bin al’ada da ibada shiyasa yankinmu ta yi baƙin jini a wajan sauran yankuna, idan har maganar da nayi baku gamsu ba kuna iya shafemu a doron kasa ko kwayi farin ciki” Arɗo na gama fadi jama’ar kwana suka miƙa wuya,ganin haka yasa yankin jimo jikinsu yayi sanyi suka ce ba zasuyi yaƙi da yankin kwana ba,nan take suka juya, yankin tudu da yankin ja’i kuwa sunce suna nan, sai sun shafe yankin kwana.
@@@@
Gudu Baffa ke yi a dokinsa dan haka yake ji a jikinsa mahaifarsa babu lafiya.
A kwana kuwa ganin yadda yankin ja’i suka fara zubar da yara da manya ta hanyar saresu da takwabi yasa garkuwan fulanin kwana cewa Sarki Chubado da Ardo
“Ranka ya dade, hakika ba zamu tsaya a shafemu ba tare da mun sa hannu ba dan bamu aikata laifi ba, burin yankin ja’i shine su ga sun shafe yankin kwana, dan haka kowa ya dibo makamai mu gwabza tunda haka suke so” mai Unguwa Ori ya ce
“Tabbas hakane” nan garkuwa ya bada umarnin a dauka takwabi a fara maidawa yanki biyu martani.
Duk wannan tarzoma da akeyi Azima na saman bishiya tana kallo tana dariya, Aziza ganin kisan da ake yiwa mutanen yankinta ya yi yawa ne ya sa ta fadi a ranta “inaaa! Burin Baffa shine ya ga ya mutu ya bar yankinsa lafiya, dan haka dole ne na dakatar da yaƙin nan ta ko wani hanya in ba haka ba, tabbas yau babu sauro da zai rage a yankin nan” ta kalli Hajja dake tsaye tana kalman shahada dan yawancin mutane sun sadakar da zasu rayu ta ce
“Hajja ina jin fitsari zanje gida na dawo” ta karasa fadi tare da juyawa,saurin kamo hannunta Hajja ta yi ta ce
“Aziza bakki hankali ashe ban sani ba?kina ganin yadda ake zubar da jini tamƙar ana ɗibo ruwa a rafin jimulo ne ake watsawa kice zaki koma gida kiyi fitsari? Idan kika bincika wasu a nan har da kashi sukayi a jikinsu,dan haka Aziza yi fitsarinki kawai a jikinki, gwanda mu tsaya ta nan idan har Allah yasa aka gama da sauran kafin a iso kanmu,idan kuma Allah yasa Baffanku ya dawo a kan lokaci to, dan shiyasa nace miki mu tsaya a nan sabida ga hanyar da zai fito nan” Hajja ta faɗa tana kara riƙe hannun Aziza, girgiza kai Hajja ta yi ta ce
“Hajja to ni kin riƙeni babu fa Azima a nan” da sauri Hajja ta ce
“Na shiga uku! Azimaaaa!?”
“Kwantar da hankalinki Hajja bari na je nayi fitsari sai na dubota mu dawo tare”
“To dan Allah Aziza ki kula,ki min alkawari zaki dawo lafiya?”
“Na miki alkawari Hajjata zan dawo lafiya” sai da Aziza ta faɗi haka kafin Hajja ta saketa,da gudu Aziza tayi hanyar gida dan ta shirya ta dawo ta tare yaƙin.
@@@@
Haka Baffa ya shigo yankinsa ya samu gagarumin yaƙi, amma da shike baya da lokacin tsayawa gida ya wuce kai tsaye ya haɗa maganin furen surfa, sannan yaje ya kirawo Hajja a inda ya ganta sadda ya shigo, amma ita bata gansa ba, yake tambayarta ina Aziza da Azima? Hajja ta ce
“Aziza tace min zata zo gida ba mamaki tana kewaye cikinta ya tsure sabida wannan tashin hankalin,Azima kuma ban ganta ba dan Aziza tace min idan zata dawo zata dubota su sameni a can”
Baffa ya ce
“Boye a can,ni kuma zan boye a nan karki kuskura kiyi magana kinji ko?” Hajja tana shirin tambayar Baffa me yake son yi ya ce
“Jumala karki tambayeni komai! Zaki ganewa idanunki!ke dai kiyi abunda na sakaki! Yaƙi kuma inada yaƙini a kan garkuwa zai tarewa yankin kwana tunda yasa hannu kafin na gama wannan binciken da zanyi, dan haka karki tambayi komai kawai je ki boye,kuma karki kuskure ki fito” Hajja ta amsa da to, maganin da Baffa ya haɗa ya kewaye kofar shigowa gida da shi, sannan ya zuba wani ya koma ya maqale, Azima dake kwance a jikin bishiya haka kawai taji kamar an tsikareta saurin saukowa tayi a saman bishiyar idonta ya kara canza kala nan ta nufa hanyar gida ba tare da tasan dalilin hakan ba wanda take ji kamar an saka mata kuran karfe ne yake janta.
@@@
Aziza ce ta fito daga kewaye idonta jajur alama ce na taci kuka, tana fitowa ta shige bukkarsu, Baffa dake maqale ta zanar kofar waje ya hangi Azima na tahowa tana layi, tana zuwa zata shiga gidan da aka yi wani sama da ita aka bugata da kasa, yayinda taji ko wani fata ta jikinta na mata zafi, ihu ta saka tana rirriƙe jikinta, ta kafarta ta fara rikidewa, wani wawan zare ido Baffa ya yi,yayinda yayi sumar wucin gadi, wannan shi ake kira tashin hankalin da ba a sa masa rana.
Aziza kuwa shiryawa tayi dan taimakawa yankinta ta zo fitowa kenan har ta sa kafa akayi sama da ita ma, ihu ta saka ta fadi kasa wanwar, girgiza kai ta hau yi jin yadda jikinta ya amsa tana shirin rikidewa ta koma macijiya,cikin dimauta take furta “furen surfa na macizai? Wa ya kawo ya zuba a kofar gida? Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! a’a a’a a’a!!” bata bari hakan ya faru ba ta shige bukka da gudu, Hajja dake kallonta ta zaro ido waje,to meke faruwa da yarta ga Baffansu yace karta fito? Anya zata iya kuwa ba zata fita ta je ta duba me ya samu Aziza ba? Hakuri dai ta yi amma hankalinta na kan Aziza, Aziza kuwa tana shiga bukka ta hau kwalawa Inno Fandi kira yayinda fatar jikinta ya koma fari sol, daga kugunta abunda yayi ƙasa ta koma macijiya????, cikin matsanacin kuka Aziza ke kiran Inno Fandi har ta bayyana, ta ce
“Na shiga ukuna Inno Fandi furen surfa na macizai wa ya zuba?”
Inno fandi ta ce
“Yanzu za a fara Aziza! Ba kowa bane ya haɗa maganin furen surfa illa Magaji, wanda a halin yanzu Azima tana waje tana rikidewa,ke ma haka gaki nan, a yanzu *BAFFANKU YA GANE CEWA AZIMA MACIJIYA CE!* kece kawai bai gani ba, dan haka ki gaya masa gaskiya dan a san yadda za ayi a yi maganin abun”
“To wani irin maganin abun Inno Fandi? Karshe dai nasan kashemu Baffa zaiyi da hannunsa” Inno Fandi ta ce
“Bana da ikon gaya muku komai, idan har na gaya muku zan iya mutuwa, Magaji shine zai gaya muku, yanzu dai me kike da bukata na miki?”
“Ina so naje na tsaida yaƙin da akeyi ne kafin na dawo ayi ta gida, ki taimaka min na fita a gidan nan” Inno fandi ta ce
“An gama” sannan ta dauki Aziza suka b’ace dan zuwa tsaida yaƙi.