AZIMA DA AZIZA Macizai Ne 1
Tana zuwa ta sameta kwance a kusa da rafi.
Hannnu tasa ta janyota ta ce
“Kin kashesa ko Azima? Na ce kin kashesa ko!?” dariya ta kyalkyala cikin amo marar dadin sauraro ta ce
“Ai na gaya miki Aziza sai na kashesa!”
Rike kai Aziza ta yi ta ce
“Me kika so ki zama ne kam Azima?”
“Bana son ganin zaman lafiya a wannan yankin! Na fi so ayi ta b’arin jini! Ina so na haɗa maƙotan yankunan nan faɗa, duk wani mai kama macizai wanda za a yi masa aike ya zo yankin nan sai na kashesa! Kin ga daga nan za a fara yaƙi tsakanin yankuna da yankuna, sannan dama akwai y’ar tsama tsakanin yankin kwana da yankin tudu da kuma yankin Ja’i nasan kuma dole mai unguwa zai bukaci taimakonsu, duk wanda aka turo ni kuma zan kashesa! Na tabbata daga lokacin zaman lafiya ya kare, Baffa shine jarumi na farko a wannan yankin wanda da shi aka yi gwagwarmaya kinga kuwa ba mamaki a wajan yaƙin a kashesa!”
????????????????
*DAN ALLAH JIYA NA FARA LITTAFIN NAN, BAN BUƊE PAID GRP BA, SABIDA BAN GAMA FREE PAGES BA,KUYIWA ALLAH IDAN BA KU GA UPDATE DINA A RANA BA KARKU CE ZAKUYI KORAFI, NA SANI DOLE NE TUNDA NA FARA ZAN KARASA DA IZININ ALLAH, SABIDA HAKA KU MIN UZURI RANAR DA BAKU GA UPDATE BA TUNDA BAN GAMA FREE PGS BA, IDAN ZAKI BIYA DARINKI YANZU FYN, IDAN KUMA SAI AN GAMA FREE PG NE DUK DAYA AMMA DAN ALLAH BAN DA KORAFI, MATAR GIDA CE NI MAI IYALAI, UWA UBA KUMA DALIBAR MAKARANTA, FATAN ZAKU FAHIMCENI,INA GODIYA GA MASOYANA MASU GANIN SUN BIYAN KUDIN KARATUNSU, NA GODE DA BIBIYATA DA KUKEYI, ALLAH YA BAR KAUNA, 1 LUV*
COMMENTS AN SHARE
BY
MOMYN AHLAN
[3/21, 12:27 AM] Fatima: https://chat.whatsapp.com/BXDHlYEJdRi65a26Qt5OSe
????????????????????????????????????????
????✨ *AZIMA DA AZIZA*????✨
(???? _Macizai ne_????)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*????????
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)_
????????????????????
????????????????????????
????????????????????????????????????
*YAU TAMBARINA NA MASOYA NE,INA GODIYA DA SAKONNINKU,KIRAN WAYA, KAI MA SHA ALLAH, ALLAH DAI YA BAR KAUNA,INA ALFAHARI DAKU A DUK INDA KU KE MASOYANA, ALKAIRIN ALLAH YA KAI MUKU HAR KUJERAR ZAMANKU????*
*FREE..*
????️==5️⃣↪️6️⃣
Zaro ido Aziza ta yi tana kallon Azima kafin ta ce
“Na rasa dalilinki na son ganin bayan Baffa! A yadda na fahimceki, ke ba ki ƙi kowa ya mutu ke ki rayu ba, idan kika samu dama na tabbata za ki kashe Baffa” dariya Azima ta kyalkyale da shi tana kewaye wajan kafin ta koma ta haɗe rai sosai ta ce
” *AI BA YAU BANE KAWAI NA SHA GWADA HAKAN!* ko a yanzu na samu sarari sai na kashe Baffa! Ko kin manta na sha yunkurin kashesa!? Lokuta da yawa ke ce kika katse min burikana! Ga shi ke ban san ya zanyi dake ba! Ke ta biyu na ce! Ba zan iya kasheki ba! Sabida duk muguntar gubana naki yafi nawa! Kuma ina sonki yar uwata! Da ace nike da karfin dafin da kike da shi da na jima da shafe wannan yankin kakaf dinta!” Azima ta fada tana daga hannuwanta sama.
Aziza ta girgiza kai ta zauna a kasa tare da fashewa da kuka ta ce
“Azima ba zan taba bari ki cutar da Baffa ba,ko da kuwa zaki iya,ni dai a gaskiya inaji a jikina kamar ni da mutum ce! Ban san a garin yaya muka zama macizai ba, miye dalilinki na son kashe Baffa Azima!?” Aziza ta faɗa tana haɗa kai da guiwa tana ci gaba da kuka,duk sadda ta kalli jikinta ta ganta a macijiya tana jin zafi a zuciyarta, ta yi nisa sosai a kuka ta ji wani irin murya na namiji wanda yake abun tsoro an bata amsar maganarta.
” *ZUNUBIN DA BAFFANKU YA AIKATA NE YAKE BIBIYARKU!, TARE DA GOYA MASA BAYAN DA JAMA’AR YANKIN NAN SUKA YI!*” da sauri a matukar firgice Aziza ta dago tana waige ta ga daga ina ne maganar ya fito? Amma bata ga kowa ba illa Azima dake wasa a cikin rafi kana ganinta zaka san tana cikin nishaɗi, ta zama macijiya ta koma ta zama mutum.
Sauri tashi tsaye Aziza ta yi tana waige a fili ta kara furta kalman da ta ji “Zunubin da Baffanmu ya aikata? Me Baffanmu ya yi kuma?” tambayoyi ne maqil a ranta amma babu mai bata amsa, ko dai zata je ta tambayi Baffa ne? Kai amma kuma idan ta yi haka za a gane su ɗin ba mutane bane, riƙe wuyanta ta yi jin kamar zuciyarta yana shirin fitowa bakinta, kallon Azima ta yi ta ce
“Azima ki zo muje gida”
“Tare muka zo dake ne?”
“Idan ma ba tare muka zo ba Hajja ta ce mu dawo tare yanzu, kar Baffa ya dawo….” Aziza ba ta karasa ba Azima ta fito tana fadin
“Ke komai ki ce Baffa?”
“To idan ban kira sunan Baffana ba sunanki zan kira?” murmushi Azima ta yi ta ce
“Yau bana jin yin faɗa dake, dan yau ina cikin farin ciki, nasan idan sako ta iske sarkin yankin jimo an kashe masa Jarman Macizai me kike tunani zai faru Aziza?”
“Ban sani ba!” Aziza ta faɗa a ƙufule ta yi gaba, ita ma Azima a macijiya ta hau bin bayan Aziza, yau tsananin takaici ya hana Aziza ta cewa Azima ta koma mutum, Azima kuwa da gangan take wani abun dan Aziza ta mata magana.
A macijiya ta shiga gidan Allah ya so Hajja na bandaki, zama Aziza ta yi ta buga tagumi, Azima kuwa bukka ta shige, bayan Hajja ta fito ta ga Aziza da tagumi ta ce
“Ah Aziza kun dawo?” shuru Hajja taji dan Aziza ta yi nisa cikin tunani, sai da Hajja ta tabota tukunna ta dawo hayyacinta ta ce
“Na’am Hajja magana kike yi ne?”
“Tunanin me kike yi haka Aziza?” murmushi Aziza ta k’wak’ulo ta ce
“Abunda yake faruwa a mahaifana shine yake tayar min da hankali Hajja”
“Karki ce zaki saka hakan a ranki,addua ita ce mafita,duk abunda ya yi tsanani maganinsa Allah” kuka Aziza ta fashe da shi ta rungume Hajja ta ce
“Dole ne na saka a raina Hajja! Idan mun san abunda ya faru yau ba bamu san me zai faru gobe ba Hajja!” sosai Aziza ke kuka yayinda hankalin Hajja ya tashi, Azima ce ta fito daga bukka dauke da abinci a hannunta zama ta yi ba tare da ta kalli Hajja ko Aziza da ke kuka ba,abincinta ta hau ci hankalinta kwance, Hajja ta kalli Azima wacce ta jima da gane ita damuwar wani bai dameta ba, ta ce
“Azima meke faruwa da yar uwarki!?”
Cikin halin ko in kula ta ce
“Oho mata! Tana son ɗorawa kanta damuwar da bata da mafita a kansa, ta ga zata iya ne, Hajja ki daina damun kanki a kanta!” Hajja zata yi magana sai ga Baffa a fujajan ya shigo ko sallama babu, da sauri hankalin Hajja da Aziza ya koma kan Baffa akasin Azima da ta yi kamar bata san da shigowarsa.