AZIMA DA AZIZA Macizai NeHAUSA NOVEL

AZIMA DA AZIZA Macizai Ne 1

“Baffan yan biyu lafiya kuwa na ganka a cikin wannan yanayin?”

 

Sharce zufa Baffa ya yi ya ce
“Jumala ina kuwa lafiya! Ku zo muje gaban gari ana neman dukka mutanen yanki, kin san an kashe Jarman Macizai kuwa?” hannu Hajja ta zuba a kirji tare da fadin
“Ma’asabumin Musibati qalu Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! An kashe jarman macizai to waye kashesa!?”

” *MACIJI! SARAN MACIJI NE A JIKIN JARMAN MACIZAI!*” Baffa ya faɗa yana sauke idonsa a kan Azima wanda hankalinta sam baya kansu, Hajja ta ce
“Ba ri na dauko mayafina mu tafi gaban gari din” Hajja ta karasa maganar tana shigewa bukka, Aziza kuma tana gyara mayafin kanta hankalinta a tashe! Baffa ya ce
“Ke Azima? Ana gaya miki mahaifarki babu lafiya amma kina zaune hankalinki kwance ba tare da kin nuna damuwarki ko a fuska ba kina cin abinci! Za ki tashi ne ko sai na saka sanda na roɗe miki shingen kafafunki nan masu kama da fuffuken sauro!” Baffa ya faɗa yana yin kan Azima da sauri ta tashi tana huci tare da juya baya, hanyar randar kasan dake tsakiyar gidan taje ta ɗibo ruwa a kwarya tare da fakan idon Aziza ta watsa dafi a ciki, sannan ta juyo tana kallon Baffa a ranta take fadin
“Ba zan taba samun salama ba idan har ban kasheka ba!” tunkaro Baffa ta yi har ta zo gabansa tana tura baki ta ce
“Baffa na ga alama kan ka ya dau zafi kaɗan sha ruwa zuciyarka ta huce! Baffa ita fa damuwar duniya bata karewa barin ma idan mutum yasa hannu ko nace mutane suka sa hannu suka jawo bala’i wa kansu, sannan dole akwai abunda ku ka aikata ma wasu yake bibiyarku! Dan haka Baffa a koma a yi tunani da kyau, ga ruwan ka sha” ta mika masa tana sunkuyar da kai kasa sai kace wata ta Allah, shuru Baffa ya yi yana son yayi tunani a kan maganar da ta fada amma tashin hankalin da suke ciki ya ƙi basa damar haka, hannu yasa ya karbi ruwan caraf idon Aziza ya sauka a kan ruwa ta hangi dafi, cikin azama ta ce
“Baffa wani ruwa kuma zaka sha? Ka manta Azima ita bata damuwa da damuwar wani? Kawo ruwan nan Baffa” Aziza ta karba, wani kallo ne Azima ta bi Aziza da shi jikinta har na tafasa tsananin takaicin abunda Aziza ta yi, Aziza na karban ruwan da gangan ta yi tuntube ruwan ya b’are kwaryar kuma ta riɗata da dutse ta fashe, cije baki Azima ta yi, idonta ya kara rinewa tana shirin tunkaro Aziza wacce itama ke kallonta ko gizau bata yi ba, Hajja ce ta kara katse mata hanzari ta fito tana fadin
“Yi hakuri Baffan yan biyu! Na zubar da wake ne na tsaya kwashewa shiyasa ban fito da wuri ba,muje” gaba Baffa ya yi Aziza ta bisa a baya, Azima ta zo fita Hajja ta ce
“Ina mayafinki?”
“Ba zan saka ba! bana jin saka wa Hajja! Raina a b’ace yake karki min maganar wani mayafi!” daskarewa Hajja ta yi jin amsar da Azima ta bata,ita ma Azima bata san lokacin da ta faɗi ba dan bata taba yiwa Hajja magana haka ba,ganin Hajja ta tsaya tana kallonta ne yasa ta cewa “yi hakuri Hajja bara naje na dauko,kuyi gaba zan zo a baya” Hajja dai bata iya cewa komai ba illa bayan su Baffa da Aziza da ta bi wanda sun yi gaba abunsu.

Su na kan tafiya Aziza ta ce
“Baffa?”
“Na’am Aziza yaya ne?”
“Baffa baka taba bani labarin kafuwar mahaifata ba, kullum kana cewa an sha gwagwarmaya da aljanu da mayu, amma baka taba bani labarin kalar gwagwarmayen da ku ka sha dasu ba”
“Yo to banda abunki Aziza ana cikin wannan tashin hankali kina maganar labari? Abunda ya kafu sama da shekaru hamsin? Ki bari Allah ya bamu ikon dakatar da wannan ambaliyar wutar masifan dake tunkaro wannan yankin” shuru Aziza ta yi ba tare da ta sake magana ba, da haka har suka karasa gaban gari inda cincirindon fulani suke tsaye kowa ka gari hankalinsa a tashe, har anyiwa jarman macizai jana’iza an binnesa.

Ana ta shawaran yadda za a rubutawa sarkin fulanin yankin jimo sakon cewa an kashe jarman macizai wanda yankuna sun san shi jarumi ne, idan ka cire yankin ja’i da yankin tudu za a iya cewa babu wani jarumi wanda ya shahara a kama macizai sama da jarman macizai, amma a yankin Ja’i akwai wanda har aljanun macizai yana kamawa tsananin shahararsa wanda har laƙabi ake masa da INNU MACIJI, daga shi kuma sai na yankin tudu wanda shike takawa Innu Maciji baya wato IRO MAGANIN MACIZAI daga shi sai wanda aka kashe na yankin jimo wato JARMAN MACIZAI, lokacin da aka raba kambun girma na wa inda suka shahara a kama macizai aka ba wa INNU MACIJI lamba daya, aka ba wa IRO MAGANIN MACIZAI lamba ta biyu sai kuma JARMAN MACIZAI lamba ta uku, har ta Ilu mai Macizai da Azima ta kashe na yankin kwana shine aka ba wa lamba ta shidda, sannan aka rabawa na ƙasa dasu, tashin hankalin da yankin kwana ke ciki shine rashin jituwar da basu da shi da yankin tudu da yankin ja’i, barin ma yankin ja’i tsatstsauran gaba ce daɗaɗɗiya, dan kuwa an sha gasan kisa a tsakani, yankin tudu kuwa dan sarkin yankin ne ya zo yankin kwana ya yiwa yar yankin fyaɗe bai kyaleta ba har sai da ya kasheta! Hakan ce tasa ARƊO ya bada umarnin a kashesa shi ma,aka gille masa kai aka turawa mahaifinsa da shi daga nan gabar ta soma, yanzu taya zasu fara neman taimakon Yankin Tudu ko kuma yankin ja’i? Yanzu dai ba shi bane tashin hankalin, tashin hankalinn shine yadda zasu fara tunkaran yankin jimo da sakon an kashe jarman macizai.

 

@@@@@@@

Su Baffa sun iso ana kan shawara ba a tsaida mafita ba, sai da Baffa ya karaso aka sake yin shawara a kan a rubuta sako a tura mutum huɗu da suje yiwa yankin jimo ta’aziyya tare da rigan Jarman Macizai wanda yake jina-jina da jini, sannan ayi musu bayanin abunda ya faru bai kai ga yin aikin da yazo yi ba aka iske gawarsa, tare da sakon ban hakuri iri da kala daga wajan mai unguwan yankin kwana da kuma sarkin fulanin yanki kwana tare da Arɗo, hakan ce ta kasance aka tura mutum huɗu izuwa yankin jimo, tare da kayan Jarman Macizai da kuma dokinsa da takwabinsa.

 

Aziza na tsaye a gefe da lullubi hawaye ne cike a idonta,ba dan komai ba illa su na zuwa wajan aka fara darewa ana matsawa babu wanda ya tsaya kusa da ita.

Azima kuwa za ta zo yau ne gobe ne shuru, har aka gama tattaunawar da za ayi Azima bata zo ba.

 

Bayan an fara watsewa Arɗo ya kira Baffa gefe ya ce
“Magaji? A gaskiya ba zan boye maka ba, ka binciki yaranka! Barin ma wannan yarinyar taka Azima,jiya an kawo min wani magana a kanta, bana son na tsawaita zargi dan babu kyau, sannan jikokinane kasan dai ba zan so abunda zai cutar dasu ba, amma ya kamata mu san abunyi,kasa ido sosai a kansu, bana so na kirawo Jumala dan duk abinda za a gaya mata ba yarda zatayi ba, sannan bayan sallar isha’i za a zauna ayi tattauna a faɗar mai unguwa, zamu je neman alfarma a yankin tudu” da sauri Baffa ya ce
“Arɗo yankin tudu kuma?”
“E Magaji, yankin tudu bamu da wani mafita wanda ya wuce hakan”
“To amma Arɗo kana ganin anya Sarkin Tudu zai sauraremu? Ko ka manta abunda ya shiga tsakanin yankinmu da nasu ne? Ɗansa yazo ya yi laifi a yankin nan an masa hukunci hakan ne ta haifar da gaba mai tsauri a tsakani, bana tunanin Sarkin yankin tudu zai yarda Iro Mai maganin macizai zai zo taimakonmu, kana gani duk wasu masu kama macizai da muke dasu a yankin nan sun mutu, a gaskiya inajin tsoron abunda zaije ya dawo, kar bamu gama da wani yaƙin ba mu sake kunna wani, a gaskiya bana so duk shawaran da za ayi ace za a bukaci taimakon yankin tudu da yankin ja’i”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button