AZIMA DA AZIZA Macizai NeHAUSA NOVEL

AZIMA DA AZIZA Macizai Ne 1

*FREE..*
????️==1️⃣1️⃣↪️1️⃣2️⃣

 

Da washe gari asubanci yankin jimo suka yi, takwas na safe su na yankin kwana,a maƙabarta jikin ƙabarin Jarman macizai, kuka sosai sarki Haruna yake yi shi da jama’ar yankinsa wa inda suka zo, an sha musu mutuwa amma farat ɗaya na Jarman macizai wanda yake jarumi a yankinsu ya gigita tunaninsu, haka suka ƙarashi koke-kokensu suka gama dan ba dawowa zai yi ba, haka jamar’ar kwana suka taru ƙwansu da ƙwarƙwatansu suka sake yiwa yankin jimo ta’aziyya tare da ban hakuri, daga fuskarsu kawai zaka kalla ka gane su na cikin mugun damuwa da tashin hankali, babu yadda yankin jimo suka iya dole suka hakura tunda dai Jarman Macizai ba dawowa zaiyi ba ya tafi kenan, sai dai fatan Allah ya yafe masa.

 

@@@@@

 

Bayan kwana biyu an gama ƙuri’u, inda aka samu sab’anin ra’ayi, jama’ar da suka fi rinjaye shine wa inda suka ce aje yankin ja’i neman taimako kar aje yankin tudu a fara zuwa yankin ja’i, dan ba za a zauna da matsala ba tare da an bukaci taimakon Allah da wa inda zasu shawo kan matsalar ba, shi dai Baffa shuru ya yi bai ce kanzil ba, haka aka sa mai rubuta wasika ya rubuta aka yiwa yankin ja’i aike da shi.

????????????????????

Sarkin fulanin yankin ja’i na zaune Maga Isar da Sakon yankin ya zo ya zube a gabansa yana fadin
“Allah ya taimakeka! Hakika a yau nasara tamu ce” wazirin fulani ya ce
“Maga Isar da Sako meke tafe da kai ne?” murmushi Maga Isar da sako ya yi ya ce
“Hakika yau muke da nasara, sako ce ta isko mu daga yankin kwana! su na cikin bala’i shine suke bukatar taimako daga yankinmu, yanzu haka ga takwabi sarkin kwana wato Chubaɗo ya aiko mana da shi alaman sun sakar mana igiyar, munyi nasara su sun faɗi, wannan takwabi da Chubaɗo ya aiko mana da shi alama ce na sun duƙawa wannan yanki tamu”

 

Sarkin fulanin yankin ja’i ya ce
“Maga Isar da sako, zai fi kyautuwa da kayi mana bayani dalla-dalla, ko kuma ka buɗe wasikar da suka aiko da shi ka karantawa dukkan wanda yake zaune a wannan fada dan jin meke tafe da sakon”

Ƙara russunawa Maga Isar da sako ya yi ya buɗe wasikar ya fara karantawa kamar haka.

 

” _ASSALAMU ALAIKUM, SAKO CE DAGA YANKIN KWANA IZUWA YANKIN JA’I, MUNA FATAN WANNAN SAƘO TA ISA GAREKA SARKIN FULANIN JA’I WATO SARKI JAWO TARE DA MAI UNGUWAR YANKIN JA’I WATO MAI UNGUWA SODANGI, A YAU MU YANKIN KWANA MUN WAYI GARI CIKIN RUƊU DA RUƊANIN TASHIN HANKALI DA RASHIN ZAMAN LAFIYA, WA HAKA NE MUKA RUBUTO SAƘO DAN YA YI TATTAKI ZUWA GA YANKIN JAMA’AR DA SUKE JA’I GABAƊAYA, AMADADIN NI SARKIN FULANIN YANKIN KWANA CHUBAƊO DA MAI UNGUWAR YANKIN KWANA ORI, DA ARƊO DA TSOHON SARKIN FULANI MANDI, DA MAGAJI BAWA DA DUK WANI WANDA YAKE YANKIN KWANA MUNA NEMAN TAIMAKONKU! MUN GAMU DA IFTILA’IN MACIZAI WANDA SUKE KASHE MANA MUTANE! AN KASHE DUK WASU MASU KAMA MACIZAI NA YANKINMU! MUN NEMI TAIMAKON YANKIN JIMO INDA SUKA TAIMAKA MUKA ROƘI ALFARMA DA JARMAN MACIZAI YA KAWO MANA DAUKI WANDA SHI MA AKA KASHESA KWANA BIYU DA YA WUCE, GA WANNAN TAKWABIN DA MUKA AIKO YANA NUNI NE DA MUN ZUBAR DA MAKAMAN YAƘIN GABAR DAKE TSAKANINMU NA TSAWON LOKACI MUN DUƘAWA YANKINKU, MUN YARDA KUNYI GALABA A KANMU! BA DAN KOMAI BA, SAI DAN MUNA NEMAN ALFARMA DA A TAIMAKA MANA DA TAIMAKON *INNU MACIJI* MUN SAN SHI KA ƊAI NE KAWAI ZAI IYA, TUNDA HAR TA ALJANUN MACIZAI DA MAYU DA ALJANU DUK YANA FAƊA DASU, DAN ALLAH SARKI JAWO DA MAI UNGUWA SODANGI A TAIMAKA MANA, KANMU A ƘASA! A YAU MUN YARDA YANKINKU YANA SAMAN TAMU, SAƘO DAGA YANKIN KWANA, SAI MUNJI DAGA GAREKU, MUN GODE_”

 

Wani murmushi sarkin fulanin ja’i ya yi yana mai kallon Maga Isar da Sako,yayinda jama’ar ja’i suka hau murmushin nasara, dan sun jima suna neman cin galaba a kan yankin kwana amma sun kasa, hakan ya samu asali ne da nasabar da Baffa yake da shi,amma wai yau sai ga shi su da kansu suke cewa sun zubar da makaman yaƙinsu? Wannan ai nasara ce babba a garesu, wakilin yankin ja’i ya ce
“Allah ya taimakeka! Ai mu nasara ce ta tako da kafarta tazo mana har gida, wai shanu daga sama gasheshshe!”

Wazirin ja’i ya ce
“Ai ranka ya daɗe abunda muka jima muna nema ne, shine suka sakar mana shi yanzu,tun yaushe muke neman nasara a kan yankin kwana amma mun kasa samu sabida Magaji Bawa” wazirin fulanin ja’i ya karasa maganarsa yana murmushi, wakilin fulanin ja’i ya kuma cewa
“Ranka ya daɗe kar mu b’ata lokaci kawai mu amsa da cewa e mun amince da bukatarsu” girgiza kai garkuwan fulanin ja’i ya hau yi ya ce
“Shekara da shekaru ake ɗibi ba daɗi tsakanin yankinmu da yankin kwana, rana daya tak su aiko mana da sako su ce sun janye anya babu lauje cikin naɗi? A gaskiya ni ban yarda da yankin kwana ba, sai dai wani shirin kawai suke yi ta yadda zasu shafemu!” garkuwan fulanin ja’i ya karasa maganarsa yana haɗa rai sosai, sarki Jawo ya ce
“Bana tunanin haka! Idan ma kuma hakane karka manta muna da fidda kunyar gasa a yankin nan wato *INNU MACIJI* wanda a halin yanzu shi suke bukatar taimakonsa,Innu Maciji dai duk faɗin yankuna sun san shahararsa! Tunda shi ya lashe kambu na daya a gasar fidda gwajin macizai! Innu Maciji bai ci sunansa a banza ba! Tunda har aljanun maciji da mayu yana yaƙi dasu kuma ya ci nasara, dan haka idan muka tura Innu Maciji dan zuwa taimakawa yankin kwana kamar yadda suka bukata yaje ya dawo ya kake tunanin martaban da yankin ja’i zai samu tare da karramawa daga sauran yankuna?”

Ajiyar zuciya Garkuwan fulanin ja’i ya sauke tare da kallon Sarki Jawo ya ce
“Ranka ya daɗe bana so mu manta da abu daya, a lokacin da aka raba kambu Magaji Bawa ya jima da sauke duk wata gab’ob’in baiwa da yake da shi, na san idan har zaka manta da tarihin Magaji Bawa da Tsohon sarkin ja’i ya baka ba zaka manta da sunansa da ya shahara a sauran yankuna ba, *GWARZON DAFIN MACIZAI!!* ka tuna?” Garkuwan fulanin ja’i na furta wannan kalma sai da mutanen da suke wajan suka firgita, Wakilin Fulanin Ja’i ya ce
“A gaskiya na so na yarda da maganarka Garkuwan ja’i! Me yasa Magaji ba zai yi wani abu a kai ba da zasu dinga bukatar taimakon yankuna! A da shi Magaji a ina ne bai yi taimako ba, gaskiya maganarka abun dubawa ce” Maga Isar da sako ya ce
“Amma shekaru ashirin Magaji Bawa ya ce ya daina duk wani abu na yaƙe-yaƙe da yake yi, bayan ya sauka ne shine aka naɗa Firi jarumin yankin kwana ko ba haka bane? Ni a tunanina da ace Magaji Bawa zai iya wani abu a kai da ba za a zo neman taimakon Innu Maciji ba har su russunawa yankin nan”

“Amma dai kun san da cewa duk wata shahara da Innu Maciji zai yi ba zai taba kamo ko da tsilen takalmin Magaji Bawa ba ko?”

Maga Isar da sako ya ce
“Ni dai bana tunanin haka gaskiya, da ace zai iya da ba zasu zo nan ba” Sarki Jawo ya ce “tabbas haka ne maganarka Maga Isar da sako, yanzu abunda za ayi,aje a cewa mai unguwa Sodangi akwai magana ta gaggawa, a biya a kira Innu Maciji, a rubutawa yankin kwana da cewa su tsumayemu zuwa gobe idan muka gama shawara da tattaunawa zamu tura musu da sako idan ma mun amince ko akasin haka” Sarkin fulanin Ja’i yana gama magana ya miƙe tsaye ya bar wajan.

 

 

????????????????

*YANKIN KWANA*

Maga Isar da sakon yankin kwana ne ya gama karanta wasikar da yankin ja’i suka aiko musu da shi, sarki chubaɗo ya ce
“Ba komai yau da gobe duk daya ne a wajan Allah, Allah ya nuna mana” mai Unguwa Ori ya ce
“Amma Allah ya kara maka yawan rai, anya yankin ja’i zasu yarda su taimakemu kuwa? Gani nake kamar su na neman hanyar da zasu wofantar da bukatarmu ne, tunda mun sanar dasu yankin jimo sun rasa jarman macizai, da mun sani da bamu rubuta musu da cewa an kashe jarman macizai ba” Arɗo ya girgiza kai ya ce
“Maganar duniya bata b’uya, gwanda dai da muka gaya musu gaskiya zai fi, balle kuma abu babba irin haka ya faru ace manyan yankuna basu sani bane? Ai hakan ma ba mai yuwa ba ce, dan naji ance yankin gangare da yankin jauro da yankin ulela da yankin nasare duk sunje yiwa yankin jimo ta’aziyyar jarman macizai”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button