AZIZA DA AZIMA 11-20

*MASU CEWA CMPLT SUKE SO, ABUNDA KO SATI INAJI BAN KAI DA FARA SAKIN BOOK DIN BA, YANZU NAKE TYPING DINSA.*
*SANARWA*
_WA INDA BASU BIYA KUƊIN KARATUNSU BA, SU KOKARTA SU BIYA NAN DA KWANA UKU, SABIDA NA BUƊE PAID GRP YAU, SANNAN FREE PAGE ZAI IYA YANKEWA NAN DA KWANA UKUN IN SHA ALLAHU, DAGA NAN ZAMU ƊORA NE DAGA PAID GRP, BANA SO AYI WANNAN CAKWAKIYAR BABU KU DAN CAKWAKIYA BA A MA YI KOMAI BA???? KU DAI KU BIYONI DA NAIRA ƊARINKU DAN KUJI YADDA ZATA KAYA A CIKIN LITTAFIN AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE, NGD MASOYANA MASU NUNA MIN ƘAUNA_????????????
*STILL FREE..*
????️==1️⃣9️⃣↪️2️⃣0️⃣
Amma bata ga inda Azima ta yi ba, rafin jimulo ta je amma ba Azima bare mai kama da ita, hankali tashe Aziza ta hau neman Azima amma bata ganta ba, jejin kwana ta nufa ta hau dubata amma bata ganta ba, riƙe kai Aziza ta yi tare da furta “YA ALLAH! dabadin ace kisan kai haramun bane babu abun da zai hanani ban kashe kanmu a yau ba kowa ya huta, wannan wani irin bala’i ne haka? Ya Allah ka yaye mana, Allah ka bani mafita ka nuna min haske, Ya Allah ka nuna min hanya! Ya Allah ni dai bana da masaniya a kan fansar da Azima take dauka, dan a iya sanina banga wanda ya mana laifin komai ba, Ya Allah idan ita haka halinta yake Allah kai kasan yadda zakayi da ita, Allah ka taimake Baffana da Hajjata da jama’ar mahaifata! Ya Allah ka karesu daga dukkan sharri!” Aziza ta karasa adduar hawaye masu zafi suna wanke mata fuska tare da jinginuwa a jikin bishiya, wani nishi taji na tashi a bayanta da sauri ta buɗe idonta da ta lumshe tana waige daga ina nishin ke fitowa, taji ashe ta bayan bishiyar ne,saurin leƙawa ta yi nan ta iske wata budurwa kwance bakinta sai jini ke bulluƙowa, cike da tashin hankali Aziza ta karasa ta ɗagota, tana dudduba meyasa meta,goshinta ta kalla ta ga bakin maciji wanda yake sara ne na Azima, ihu Aziza ta yi tana ajiye kan budurwar a kasa ta tashi da sauri tana ja da baya ta kuma sakin wani mahaukacin ihu tana furta “AZIIIMAAAAAAA!!!?” da gudu ta bar wajen dan babu taimakon da zata iya yiwa budurwar dan kuwa gubar ya shige mata jiki sosai dan harta idonta da tafin hannunta sun koma blue.
Duk inda Aziza take tunanin zata ga Azima amma da ta je sai dai ta iske gawa, hakiƙa fadin yadda hankalin Aziza ya tashi b’ata lokaci ne, ga shi ta rasa yadda zata yi, bata kara shiga ruɗu ba sai da ta yi gamo da gawar mutum takwas wanda Azima ta kashe, daga karshe Aziza ta koma tayi zaman yan bori.
????????????????
*YANKIN JA’I.*
a lokacin da garkuwan fulanin yakin kwana suka isa yankin ja’i da gawar Innu Maciji hakika sun ga tashin hankali, sun ga masifa da bala’i a wajan jama’ar yankin ja’i, ko kaɗan sarkin fulanin yankin ja’i wato Jawo da kuma mai unguwa Sodangi da sauran duk wanda yake yankin ja’i basu tsaya sun saurari su Garkuwan fulanin kwana ba, suna isa da gawar fadar sarki Jawo nan yankin ya ɗauka daga tafiyar Innu Maciji yau yankin kwana sun kashesa, nan jama’ar yankin ja’i suka janyo wuƙaƙe da adduna da sanda kokara,suka yi kan su garkuwan fulanin kwana tare da fadin su ma ba za a barsu a raye ba, Galadima da Liman suka ce yadda suka tunzura gwanda kawai su gudu, garkuwan fulanin kwana ya ce bai kamata su gudu ba tare da sun musu bayanin abunda ya faru ba” Galadiman fulanin kwana ya ce
“Baka da hankali ne garkuwa? Ka ga yadda suka haukace suna ihu ka ce mu tsaya musu bayani taya zasu sauraremu? Ka zo kawai mu gudu dan ceton ranmu daga baya idan suka yi sanyi sai mu dawo! Amma kaga yanzu suna abu kamar wa inda mahaukacin zaki ya cije su” Garkuwa ya ce
“A gaskiya ba zamu tafi ba tare da munyi musu bayani ba,tunda duk abunda ya faru mu muka ja wa kanmu! Da ace mun bi shawaran Magaji da ba haka ba”
“Amma dai garkuwa kasan rashin hakuri irin na yankin ja’i da haukarsu ko? Ka zo mu gudu idan ba haka ba zasu iya kashe m….” maganar da Liman bai karasa ba kenan yaji saukar dutse a goshinsa,nan ya riƙe goshin yana faɗin “Ya Rabbi!” kafin su Garkuwa su dago nan suka ji ihu, inda gaba daya ahalin yankin ja’i mata da mazansu kowa ka gani da makami nan suka yo rututu suna shirin kai wa su Garkuwa farmaki,nan suka hau musu ruwan manyan duwatsu kafin su isosu,ganin haka yasa Galadiman fulanin kwana da Limamin fulanin kwana suka kwasa a guje dan tseratar da ransu, sauran mutum biyar na fada mutum uku su ma suka arce da gudu aka bar Garkuwan fulanin kwana da mutum biyu na fada su uku kenan, kafin Garkuwan fulani ya yi kokarin faɗin wani abu tuni, an rufesu da duka da sanda, yayinda ƙanin Innu Maciji yasa adda ya sare daya daga cikin ɗan fada a wuya yana sare san nan ko minti daya bai yi ba yace ga garinku, ganin haka yasa garkuwan fulanin kwana yace shi da dayan ɗan fada su gudu, da kyar suka kwace suka hau dokinsu ba shiri suka sab’i hanya jikinsu jina-jina da jini, dan garkuwa ma kam an saresa a hannu.
Har mutanen yankin ja’i zasu bi su garkuwa, Sarki Jawo ya ce su dawo ai sun b’allowa kansu yaƙin da basu san wanda zai tare musu ba, za ayi wasika a tura musu su shirya tarban yaƙi,kuma suna da yaƙinin zasuyi nasara ta hanyar shafe al’karyan kwana tunda Magaji Bawa ya yi murabus!.
@@@@@@
*YANKIN KWANA.*
haqiqa yau yankin kwana tana cikin ruɗu da ruɗani,yayinda suka jera gawawwaki har na mutum sha ɗaya wanda saren maciji ne a jikinsu.
Yau da safe mutum biyu sun sha dafin maciji sun mutu, Innu maciji saran maciji ya mutu,yanzu kuma ga gawawwakin mutum sha daya, tsananin tashin hankali yasa suka kasa yiwa gawawwakin jana’iza ga magriba ya gabato, ganin haka yasa sarki Chubaɗo bada umarnin a musu sutura a binnesu kar su yi kwanan keso, da kyar suka yi musu jana’iza suka binnesu, bayan sun fito daga maƙabarta sai ga isowarsu Galadiman kwana shi da Liman a fujajan, da sauri mutanen yankin kwana suka tarbesu suna tambayarsu me ya faru? Baffa ya kalli goshin Galadima dake zubar da jini an fasa masa goshi,Baffa ya ce
“Daga ganin goshin Galadima ba sai an tambaya ba! Mun taro yaƙi ko? Ina su Garkuwa!?”
????????????????
???????????? 1readmore
[ad_2]