AZIZA DA AZIMA 11-20

“Sai na gwada ta wata hanyar!” Aziza ta faɗa tana mikewa tsaye, da sauri Azima ta mike ta ce
“Muje zuwa” tana gama faɗi ta hau ajijiya, Aziza na tsaye tana kallonta.
????????????????
COMMENT AND SHARE
BY
MOMYN AHLAN
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????
????✨ *AZIMA DA AZIZA*????✨
(???? _Macizai ne_????)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
*IDAN AKA CE ƘAWANCE ANA NUFIN AMINTAKA! WANDA WANNAN AMINTAKAR WATA DANƘO CE MAI MANNUWA,ANA SAMUNSA NE IDAN AKA SAMU YARDA DA AMANA! IDAN NA KIRAKI DA SUNAN ƘAWATA BAI KAI INDA ZAN NUNA YADDA NAKE YINKI A CIKIN RAINA BA, HAKIKA MU DIN BA IYAKAR KAWANCE BANE,INAJINKI TAMKAR WACCE MUKA FITO CIKI DAYA,INA MIKI SON SO SABIDA ALLAH! ALLAH YA BAR MINKE ƘAWALLITA _RASHEEDAT USMAN UMMU NASMA&NASREEN_ ALLAH YA ALBARKACI ZURI’ARMU ALLAHUMMA AMIN, INA KU KE MAKARANTA? UWAR NASMA TA YUNƘURO FA A BOOK DINTA MAI SUNA _GELLE ‘BINGEL_ WANDA ZAKU SAME SHI CIKIN FARASHI MAI SAUKI, KU NE ME NI TA LAMBATA DAN ISA GA FASIHIYAR MARUBUCIYAR KAI TSAYE, KARKU BARI A BAKU LABARI, SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*????????
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*????????
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)_
_Follow me on wattpad,@Fateemah’0_
????????????????????
*FREE..*
????️==1️⃣5️⃣↪️1️⃣6️⃣
Bata motsa ba, har Azima ta gama hajijiyarta, ta girgije ta zama macijiya daga ƙasanta, ta ce
“Mu gwada mana Aziza, yau inaji da abunda ba ki ji” murmushi Aziza ta yi ta ce
“Dan kin saƙa zaren dana shine kike tunanin zaki iya dani? Kawai cewa nayi ki faɗa min wanda za ki kashe da shi, idan ba haka ba na gwada ta wata hanyar” sosai Azima ta haɗe rai fuskarta ya fara komawa blue ta ce
“Idan zakiyi kawai kiyi! Bana son magana a baki sai dai a aikace!” Azima na gama faɗi ta daga hannunta ta huro wuta, Aziza na tsaye na kallonta, sai da Azima ta gama hura wutar ya yi jajur sannan ta yi wani gurnani ta hurawa Aziza, Aziza na ganin yadda wutar ya nufota ta yi tsalle ta haɗa wani farin hayaki ta maidawa Azima abunta nan ya sameta patttt! A ƙirji! Zubewa ƙasa ta yi tare da komawa mutum, a hankali Aziza ta zo gabanta ta ɗurkusa tana shirin yi mata magana taji yankan wuƙa a kafadarta ya shige, kafin ta farga Azima ta yi mata kafa ta nausheta a ciki nan ta faɗi kasa numfashinta nayin sama, Azima kuma ta miƙe tana dariyar mugunta gami da cewa.
“Gaskiya bana da burin kasheki yar uwata, amma ya zama dole ko dan na kammala aikina a kan lokaci! dan zaman wannan dajin ya isheni ina da bukatar shiga gari, to amma idan kina raye taya burina zai cika? Ba ki san ta yadda akai na samu zaren saƙar dana ba taya kuwa zan gaya miki wanda zan kashe da shi!? To ba zan faɗa ba! Yanzu kuma idan na kasheki bani da wata sauran damuwa a rayuwata ko abunda zai dinga kawo min cikas da burina!”
Duk maganar da Azima ke yi Aziza na jinta yayinda hannunta daya tana riƙe da kafadarta da yake zubar da jini dayan kuma yana kan cikinta da Azima ta yi mata naushi da kafarta, tsoronta daya shine Allah yasa wuƙar da Azima ta yanketa da shi babu zaren saƙar dana a jiki, idan hakane yana nufin Azima zata yi b’arna? Idan ta kasheta zata kashe sauran mutane sannan ta shiga cikin gari ta tarwatsasu? Inaaa! Hakan ba zai yu ba, dole na dakatar dake ko ta wace hanya! To amma me zanyi yanzu? Aziza take tambayar kanta mafita, Azima kuwa na tsaye ta juyawa Aziza baya tana ta zuba kamar indararo, wata zuciyar ta cewa Aziza
“Kin manta ba zaku iya kashe juna ba? Amma ke zaki iya kashe Azima! Duba Taurarinku dake haɗe ke kaɗai aka yarjema wa dan ki gani da mai zaki dakatar da Azima” a hankali Aziza ta miƙe ta kama bishiya ta ɗan jinginu, ta lumshe ido, nan ta hau gane-gane, tabbas ba zasu iya kashe juna ba amma zata iya karyawa Azima kwarin guiwa, sannan wukar da ta yanketa da shi babu zaren sakar dana a jiki, Aziza na ganin haka tasa hannu ta shafe inda Azima ta yanketa nan wajan ya koma kamar ba a taba saka ma shi wuƙa ba, sannan a ranta ta ce
“Inno Fandi! Yau inaso ki bani abunda kika sha miƙa min ina ƙin karba,ko ta wace hanya ce ina so na dakatar da Azima,ina so na san wa zata kashe da zaren saƙar dana dan na basa kariya,duk da zuciyata tana zargin Baffa Azima take son kashewa! Amma ita baka iya tunanin abunda zatayi dan komai ma zata iya yi! Inno Fandi yau ina so ki bani” Aziza a ranta take magana idonta a lumshe, wata farar tsohuwa ce fara sosai tsohuwa tukuff ta bayyanawa Aziza tana murmushi ta ce
“Wani lokaci domin tsaida zubda jini! Muma sai mun wanke hannayenmu da jini! Magaji Bawa ya ajiye baiwarsa yayinda ya binnesa, na zabi shiga jikinki dan taimaka miki ke da mahaifinki a lokacin da na hango bala’in da zai faru a rayiwarku bayan an haifeku, Magaji ya yi tunanin binne baiwarsa zai ce wannan yanki ta yi sanyi, amma kashe Banju shine babbar bala’i ma wannan al’karya dan yace zai dawo, ba zaki iya jin komai a bakina ba Aziza dan alƙawarin da muka yiwa Magaji cewa daga bakinmu wani nasa ba zai ji tahirinsa ba sai dai idan shine ya bayar, sabida alkhairin da Magaji ya mana ba zan manta da shi ba, hakika Magaji Bawa jarumi ne, Aziza wannan abunda zakiyi ba ƙaramin yaƙi bane wanda ke daya ba zaki iya yi ba,ni kuwa bazan iya tayaki ba, amma ga wannan ki ɗora shi a ɗamtsen hannunki zai taimaka miki sosai,sannan karki taba rabuwa da shi dan wani sirhitaccen karfi ne, duk sadda kike bukatar taimakona ki kirani zan zo!” tana shirin b’acewa da sauri Aziza ta ce
“Inno Fandi! Jejin lore! Ina so naje” zaro ido Inno Fandi ta yi ba tare da ta yiwa Aziza magana ba ta b’ace, a hankali Aziza ta buɗe ido ta kalli Azima wacce har yanzu take tsaye take magana a kan zata kashe Aziza.
Ɗora zaren da Inno Fandi ta bata ta yi a damtsen hannunta sannan ta juya baya ta rintse ido nan fatar jikinta ya hau sab’ulewa alama ce na zata koma macijiya, nan ta zama wata katuwar macijiya????fiye da yadda take zama a da, fara sol sai kyalli take yi, Azima dake ta zuba tin dazu bata san abunda ke faruwa a bayanta ba, sai bayan da ta gama maganarta na karshe da fadin
“Sai fa hakuri! Amma yau za ki mutu! Ni haka nake! Muguwa ce ni! Ban san sani ba! Ban san sabo ba!” tana gama faɗi ta juyo dan cakawa Aziza wuka nan ta ga babu Aziza, ɗaga kan da zata yi ta hangi kanta a can sama, Aziza ta zama katuwar macijiya mai cike da tsoro da firgici, da mugun tsoro Azima ta ja da baya tana fadin