Uncategorized

AZIZA DA AZIMA 11-20

“Ya haka?” bata ankare ba ta ji anyi sama da ita an yi kasa da ita, kafin ta girgije ta ji an dauketa ana zagaye iska da ita, sai da aka wujijjigata sosai sannan aka yi wulli da ita, faɗuwa ta yi ta bugu.

    Buɗe baki Aziza tayi a tana macijiyar????ta hau yiwa Azima ruwan macizai???? su na fita suna saren Azima, sai da ta cikata da macizai sannan ta koma mutum tana tsaye tana kallon Azima wanda macizai ke sara, Azima ta kasa tabuka komai, da taji jiki taji tabbas zata iya mutuwa ita kuwa ba zata yarda ta mutu ba tare da ta dauki fansa ba yasa ta ce

“DAN ALLAH AZIZA! KI KWASHE MACIZANKI! ZAN GAYA MIKI WANDA ZAN KASHE!”  jin haka yasa Aziza ware hannu ta janyo macizan sannan ta b’acer dasu, tana janyesu Azima ta zube kasa a galabaice, Aziza ta ce

“Gaya min! Wa za ki kashe da zaren saƙar dana?”

” *BAFFA*” Azima ta faɗa cikin muryan galabaita, saurin ja da baya Aziza ta yi ta ce

“Baffa?”

  

Da jan ido a tsawance Azima ta ɗago idonta ta watsasu a cikin na Aziza ta ce

      “Eh Baffa zan kashe da zaren saƙar dana! Ban san wani irin kalar baiwa Baffa yake da shi ba, amma abunda na sani shine duk wata hanyar guba da nabi dan son kashesa duk basu aiki! Tun ina gwada kashesa a boye har na fara bayyanawa kika sani! Bincikena ya nuna min cewa zaren saƙar dana ne zai kashe Baffa wanda da shine ya…….” maganar da Azima bata karasa ba kenan Aziza ta wanketa da mari, za ta kara Azima ta riƙe hannun Aziza ta ce

“Karki kuskura idan ba haka ba a yau din nan wannan al’karya zata koma toka, kodayaushe kina nuna min karfin dafi da baiwar da kike da shi, ga taken kalmata ta karshe wanda kika sani Aziza, *IDAN KIN ISA KI DAKATAR DANI!*”

     miƙewa tsaye Aziza ta yi ta ce

“Na yarda da maganarki Inno! Domin tsaida zubda jini! Dole ne muma sai mun wanke hannuwanmu da jini! Ke dodon mutan yankin nan ne da Baffa ko Azima? To ki sa a ranki ni nice dodonki, dakatar dake kamar na yi na gama” dariya Azima ta kyalkyale da shi ta ce

“Muje zuwa, ai ba a buga komai a wasan ba! ” ba tare da Aziza ta sake magana ba ta bar wajan, a hankali Azima ta miƙe ta b’alli gashin kanta tsili ɗaya ta hura wani hayaki a jiki sannan ta haɗiye nan inda macizan Aziza suka sareta wajan ya koma ya yi fess sannan ta dauki hanyar gida, Aziza kuwa ba gida ta yi ba, dan bata ga ta zaman gida ba,dole ne taje jejin lore dan lalata zaren sakar dana in ba haka ba kuwa Baffa da sauran jama’a zasu mutu.

     ????????????????

A tunzure ta zo shiga gidan, amma jin maganar da Baffa da Hajja ke yi ya sakata maqalewa a jikin zana tana sauraronsu, Hajja ke faɗin

“Innu maciji kam ina da sa rai a kansa sosai, zai iya kawo mana karshen wannan matsalar da yardan Allah, tunda yana gwagwarmaya da aljanu, a goben zai zo?”

     “In sha Allahu! Haka suka ce zai zo a gobe, amma a gaskiya da a so samuna ne da bamu nemi taimakon yankin ja’i ba sam wollah, karki so ki ga izgilancin da suka mana a cikin wasikarsu kafin su amince da bukatar yankin nan”

    Ajiyar zuciya Hajja ta sauke ta ce

“Koma miye tunda sun amince shikenan Allah ya shiga mana gaba! Idan kuma tsohon gaba ne yanzu kuma ta kau ai, tunda yankin kwana ta duƙa musu” girgiza kai Baffa ya yi ya ce

“Jumala! Ba shi bane abunda nake hange! Idan wani abu ya samu Innu Maciji ko da ƙwarzani ne to fa! Sabon yaƙin da ba ayi ba kwanakin baya shi za ayi yanzu! Duk inda ake neman rashin hakuri masu jiran sammacin yaƙi idan aka samu yankin ja’i to an kai karshen magana, mutanen da jira suke a tab’osu ko kaɗan ne su yiwa mutane cin mutunci, meyasa gabanmu dasu yafi tsanani? Ina sabida yankin kwana taƙi daukar cin mutunci ne, amma al’ummar yankina sun kasa fahimtar abunda nake gaya musu, idonsu ya rufe da neman mafitar wannan bala’i shiyasa duk shawaran da zan basu, ba su gani inda a karshe ma laifi ne suke gani, suna ganin kamar zan iya wani abu a kai amma naki, duka so suke naje na haƙo kayana da na binne wanda haƙo wannan kaya sabon bala’i ne da barazana wa rayuwar su Azima da Aziza har ma dake! Balle kuma ace ni da ake neman fansa a kaina! Su tsaya su saurareni na gaya musu yadda za ayi amma sam!” Baffa ya faɗa yana riƙe kansa dake sara masa, shuru Hajja ta yi ta ce

“Komai ya yi zafi maganinsa Allah Baffan yan biyu, mu dage da addua Allah na nan!” 

“Haka ne Jumala, Allah ya shige mana gaba”

“Amin” Hajja ta fada tana miƙewa da fadin

“Ko inasu Azima da Aziza suke? Kai wannan yara yanzu haka suna can rafin jimulo” Baffa dai bai kuma cewa uffan ba.

       Wani murmushi Azima ta yi da saurin komawa baya, ta ce

“Kai ashe dai ina da babbar mugun ƙulli! Gobe Innu Maciji zai zo, ayya Innu Maciji  ashe kwana ya kare! Ajali ya yi kiranka gobe, wayyo dadi zan so na ci gaba da ganin tashin hankalin wannan yanki, hakika Innu Maciji gobe asalin Macijiya Azima zata kasheka! Wayyo farin ciki! Zanyi tsumayen jiran zuwanka yankin kwana!” ta faɗi tana dariya tare da gyara mayafinta, sannan ta shiga gidan da sallama wanda rabonta da sallama harta manta,tana yin sallamar taji har wani ɗaci wuyarta ke mata, da mamaki Hajja ta amsa ita da Baffa dake zaune, kusa da Baffa Azima ta zauna tana murmushi sai kuma ta koma tayi fuskar tausayi tana kallon Baffa ta ce

“Baffa kayi hakuri da abunda nayi dazu ban san nayi ba, amma Aziza ta fahimtar dani, ka yafe min Baffa ba zan sake ba, ban san lokacin da nake yi ba dan Allah Baffa????????” shuru Baffa ya yi yana kallon Azima a ransa ya ce

“Kenan da gaskiyar Aziza, Azima aljanu gareta?” a fili kuma Baffa ya ce

“Shikenan ya wuce Azima,Allah ya miki albarka, amma ki gaya mini gaskiya ina kika samu zaren saƙar dana?” 

   Turo baki ta yi ta ce

“Baffa ganinsa kawai nayi a hannuna! Yanzu kuma ya b’ace, ban gansa ba”

        Baffa ya sauke ajiyar zuciya har yana hamdala, Azima ta miƙe taje ta rungume Hajja wacce rabon da ta rab’eta ba zata iya tunawa ba ta ce

“Hajja ke ma kiyi hakuri” murmushi Hajja ta yi har kwalla na taruwa a idonta tana shafa fuskar Azima, yatsine fuska Azima ta yi a ranta tana kallon Hajja ta ce

“Ni dai bana jin shaukin komai a tare daku, ko da ba zan ji a kan Baffa ba a matsayinki ta mahaifiyata ya kamata ace naji shaukin uwa da ‘yarta, amma bana ji saboda ni ba mutum ba ce! muguwar macijiya ce, shiyasa ma babu amfanin na dinga rab’anku, abunda nake so shine…..” maganarta ce ya tsaya jin Hajja ta jijjigata tana mata magana, dan tun dazu Hajja ke mata magana amma hankalinta ya yi nisa da tunani

“Na’am Hajja me kika ce?”

“Tunanin me kike yi Azima?”

” kawai Hajja babu komai mai kika ce?”

“Ina Aziza?” tsaki Azima ta yi a boye da tana shirin tace bata sani din ba, sai kuma ta tuno da abunda take son yi ta ce

“Na barota a rafi, Hajja bari na tayaki aikin gida yau” tana gama faɗi ta hau gyara kara a murhu,Hajja har can kasar zuciyarta take jin farin ciki, Baffa ya miƙe yana fadin

“Ba ri naje na gaida Inna Wuro (matar Arɗo) kwana biyu ma tace ba kuje kun gaisheta ba, wai dama Aziza ce yar albarka yar dakinta, ke kam ma Azima ko meyasa jininku bai zo daya ba oho!”

“Ai ni babu wanda jinina ya zo daya da na shi!” Azima ta faɗa tana murmushin gefen baki mai ciki da ma’anoni, Hajja ta ce

“Kinyi magana ne?”

“A’a Hajja ban ce komai ba, bari naje na ɗibo ruwa” ta faɗa tare da daukar tulu ta yi waje.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button