AZIZA DA AZIMA 11-20

????????????
Tsaye take a wani jeji suna magana da Inno Fandi, Inno Fandi ta ce
“Aziza jejin lore ba kamar sauran jejin yankin kwana bane! Jeji ne da bai tara komai ba fa ce sai manyan aljanu masu mugun sihiri, babu abunda babu a jejin lore,kina tunanin zaki iya zuwa?”
“Inno Fandi Azima ma taje ta dawo balle ni? Ba ma Azima ba, Baffa da yake mutum ma yaje” murmushin manya Inno Fandi ta yi na yaro-yaro ne ta ce
“Aziza tabbas Baffanku mutum ne amma ba kamar kowa ba”
“Eh ni dai Inno Fandi ko ma miye zanje”
“To shikenan Aziza, dokar tafiya jejin lore, ba a yinta da rana, sai dai ki bari da magriba ki tafi, sannan ki tabbata kafin garin Allah ya waye kin baro jejin! Za ki ta gane-ganen abubuwa amma karki tsorata, dan tsoronki barazana ce ga rayuwarki!”
“To amma Inno Fandi ina ga hakan ai babu amfani tunda ni ba mutum ba ce macijiya ce” sake murmushi Inno Fandi ta yi ta ce
“Sanin kasancewarki ba mutum ba shiyasa nake gaya miki hakan, da ace mutum dan adam ne da ya kama hanyar sunansa gawa! Tun kafin ma ya kai ga shiga” Aziza ta jinjina kai, nan Inno Fandi ta gama gaya mata matakin da zata bi taje jejin ta dawo, godiya sosai Aziza ta mata daga nan Inno Fandi ta b’ace, Aziza ta kamo hanyar gida, tana cikin tafiya har ta kusa isa gida ta haɗu da wasu yan matan yankinsu wanda za a kamasu nan da sati daya wato amare kenan, wanda dukkansu babu wacce ta haura sama da shekara shaɗaya, su hudu suka sha gaban Aziza, dayar mai suna Lantai ta ce
“Ke wacece Azima ce ko Aziza!?” Aziza ta ƙara gyara lullubinta tana rufe gefen idonta da gashinta da ya sauko mata har kirji ta kara dukar da kanta kasa ta ce
“AZIZA” wata mai suna Huwe ta ce
“Yau kwayar idonki muke son gani, da asalin fuskarki!” gaban Aziza ne ya faɗi ta ɗan dago a hankali ta ga rana ya faɗi ga shi dole taje gida ta yi shiri, dan haka ta ce
“Kun ga bana son kalen rigima da jan faɗa ku barni naje gida ni ba sa’arku ba ce!” dariya suka kwashe da shi inda suka hau tureta tana ja da baya, har suna faɗin wai gandamemiya marasa farin jini sun ƙi aure, babu mai sonsu! Gajiya Aziza ta yi inda ta daka musu tsawa sai da suka dare, hannu tasa ta kwashe gashinta na gefen fuskarta farin eyes dinta na mage suka bayyana, da mugun gudu wannan ta yi gabas,daya ta yi kudu,daya arewa,daya kuma ta yi yamma, Aziza ta ce
“Alhamdulillahi! Ni ku ka samu, da ace Azima ce sai dai a aurar da wasu amma ba ku ba” tana gama fadi ta wuce da sauri tana sake rufe gefen fuskarta.
????????????????
“Assalamu alaikum” Aziza ta yi sallama Hajja dake kwashe kaya ta amsa ta ce
“Aziza sai yanzu? Tun dazu nake tambayar Azima tace min kina rafi, sawunta yau biyar tana ɗibo ruwa”
“AZIMAR!?” Aziza ta tambaya a mamakince, Hajja ta ce
“Eh wollah, yana ganki haka Aziza ba ki da lafiya ne?”
“E Hajja kaina ke ciwo sosai, shiyasa ma na zabi na zauna a rafin yau, ammm Hajja ga wannan ki sha”
“Inji waye?” Hajja ta tambayi Aziza
“Ba kowa nina haɗa miki sabida ciwon bayan da kike fama da shi”
“Ayye Aziza ai naji sauki tun wanda kika bani kwanakin can”
“E duk da haka ma ki sha wannan Hajja” ba tare da Hajja ta sake magana ba tasha, tana gama sha Aziza zata yi magana taji ana shelan kiran sallar magriba, hakan ne yasa kawai ta rungume Hajja wacce taji komai na kanta ya dauke, sun ɗau lokaci a haka kafin Aziza ta saki Hajja ta yi alwala ta gabatar da sallar magriba ta jima tana addua kafin ta tashi ta canza kaya ta ɗauki abubuwan da zata dauka ta kara da wa inda Inno Fandi ta bata ta fito ta fice a gidan kafin Baffa ya dawo, tana zuwa bayan zanar gidansu ta rufe ido nan ta b’ace b’atttt!!.
????????????????
Ko da Azima ta dawo gida ita ma shiri gwabzawa ta yi da Innu Maciji,dan ta lashi takwabin kashesa!.
Hajja kuwa bata tambayi inda Aziza take ba.
Tun tsawon dare Azima ta zama macijiya ta sulale a hankali ta fice a gidan, bata zarce ko ina ba sai tsakanin shigowa yankin kwana da yankin ja’i.
????????????????
HAHAH NA HADA MUKU DA PG DIN JIYA DA NA YAU, MUN RABU LAFIYA????????♀️????????♀️????????♀️
COMMENTS AND SHARE by
*FREE..*
????️==1️⃣7️⃣↪️1️⃣8️⃣
A wani ƙasurgumin jeji Aziza ta tsinci kanta, jeji mai cike da wani mugun duhu da abubuwan tsoro tare da wasu mugayen halittu marasa kyawun gani da ban tsoro, haƙiƙa ganin wa innan abubuwa sun tsorata Aziza, amma tunowa da maganar Inno Fandi da cewa kar ta tsorata yasa ta takure tare da tattaro jarumta, ta hau tafiya, tare da furta kalman “makarin zaren saƙar dana!” wani sowa ne taji na tashi ta tsakiyar kanta da wani irin mugun jijjiga nan wasu halittu suka yi sama da ita, saura qiris Aziza ta saki ihu amma kuma ta daure tana karanto dukkan adduar da ya zo zuciyarta, nan halittu suka dauketa suka kara yin sama da ita suka hau tafiya da ita a cikin duhu,amma duk wannan duhu ba shi ya hanata ganin mugayen halittu marasa kyau da ban tsoro ba.
Wa inda suka dauketa basu ajiyeta a ko ina ba sai a gaban wani katon halitta wanda bata san dame zata fasalta halittarsa ba sabida tsananin muni da girmarsa, ana ajiyeta muryar wannan katon abun ya ce
“Keeeee! Me ya kawoki jejin lore!!!” a yadda muryarsa take ɗan adam idan ya jita ya ci ace ya mutu tsananin amo marar daɗi da kaifi, cikin dakiya Aziza ta ce
“Makarin zaren saƙar dana, shi nake so” shewa wannan halittar ya yi,sannan ya ce
“Ya matsayinki yake a halittu!?”
” *NI MACIJIYA CE!*” Aziza ta bada amsa, wannan halittar ya ce
“Ke ba iyakar macijiya ba ce, akwai wani sirri a tattare dake, dan haka ko ba mu baki makarin zaren saƙar dana ba,kaifin gubar dake jikinki zai iya ƙonasa! Amma kasancewar sau daya tak! Muke bada alfarma zamu baki taimako guda daya, zamu ƙara miki karfi, da kinje ki hurawa zaren wuta ta idon ki zai ƙone ƙurmuss! Ga wannan” ya faɗa yana daukar wata kyakkyawar dutse mai cike da hasken gaske ya hura mata shi ya shige ta goshinta, abun na shiga jikin Aziza sai da ta girgiza ta yi kamar zata faɗi amma ta yi iyakar iyawarta bata faɗi ba,dama tana tsaye ne ita ba a sama ba ita ba a kasa ba, abun na shiga jikin Aziza nan ta kalli fatar jikinta ta ga yana sab’ulewa har yana komawa wata fari-fari, kafin ta gama dawowa hayyacinta tuni ta fara rikiɗewa tana komawa macijiya, nan ta zama wata shirgiɗeɗiyar macijiya mai cike da abun tsoro, nan aka hau guɗa wanda yasa duk jejin lore ya dauka, kafin wannan katon halittan ya ce a maidata gida lafiya, nan suka fizgi Aziza,wacce tunda suka fizgeta bata kara sanin ina kanta yake ba, sanyin asuba ne ya farkar da ita,tana buɗe ido ta ganta a kofar gida, saurin tashi ta yi tana karkaɗe jikinta, nan abunda ya faru a daren jiya ya hau dawo mata, lallai kam jejin lore ba jejin mutane bane, da kyar ta saita kanta jin yadda jikinta ke mata ciwo, da sanɗa ta shiga cikin gida, tana shiga Baffa na fitowa daga kewaye ya yi alwala zai je masallaci, ya ce
“Aziza har kin farka? To shiga ki tada Hajjarku sannan ki tashi Azima su yi sallah”
“To Baffa” Aziza ta faɗa ta shiga ta tada Hajja sannan ta fito ta shige bukkarsu, ko da ta shiga bata gan Azima ba, a ranta ta ce ko ina taje oho mata, kayanta ta ajiye sannan ta fito ta yi alwala ta yi sallah ta jima tana addua sannan ta tashi.