AZIZA DA AZIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

AZIZA DA AZIMA 31-40

       Azima bata farka ba sai bakwai na safe tana tashi ta wargaza dakin Hajiya ta kwashi kudin dake dakin kafin ta buɗe dakin ta fito,nan ta ga Hajiya na bacci wani murmushi ta yi na gefen baki, dakin Lantana ta nufa taje ta sameta zaune tana karatun al’kur’ani mai girma, wani wawan jiri ne ya ɗibi Azima,Lantana ganin haka yasata rufewa ta tashi da sauri ta kamo Azima tana tambayarta lafiya? Azima ta ce

“Lafiya lau! Ga wannan kudi ke da mai jiran ƙyauren gidan nan(gateman) ku bar gidan nan ku koma garinku,ke yar wace gari ce?” 

“Ni ‘yar can cikin kauyen kano ne, amma meyasa zamu tafi?” cikin tsawa Azima tace

“Bana son tambaya zaku tafin nan ne ko zaku shiga sahun wa inda za a binne?” jin haka yasa Lantana karban kudi jikinta na rawa dan bata taba jin murya nai amo da firgici irin wannan ba harta kayanta tace ta yafesu dama tsumokara ne, ta ce “ki yafeni Hajiya Azima idan na bata miki sai wata rana” bata jira amsar Azima ba ta fice, ta  kai wa Mai gadi yana tambayarta miye tace masa kawai ya yi ta kansa, sai da Azima ta tabbatar da sun bar gidan kafin ta ja kofa ta koma, shiganta parlour ya yi dai-dai da farkawar Hajiya, bata yi wata-wata ba tasa hannu ta fizgi Azima ta gaura mata mari dai-dai sadda Baby da Zuby suke buɗo kofa dan lokacin haɗa musu tea ya yi, Zuby ce ta ce

“Hajiya me ya faru haka?” cikin kumfar baki Hajiya ta ce

“Wannan ‘yar jeji ni zata bari na kwana a parlour?”

“A parlour kuma?” cewar Baby tana bin Azima da kallo da kanta babu dankwali sai gashinta da ya rufe mata fuska

“Ke ba magana ake miki bane?” cewar Zuby tana hararan Azima dake tsare jikinta na tsuma, hannu Baby tasa taja gashin Azima yana kwashe na fuskarta nan Azima ta ware kwayar idanunta a kan Baby,wani ihu Baby ta saki tana ja da baya, Zuby tasa hannu zata juyo da Azima dan ta ga me Baby take yiwa ihu kafin ta juyo da Azima, Azima ta juyo ta hura mata baƙin hayaki a fuskarta, kafin su farka tuni Azima ta yi juyi ta zama rabi mutum rabi macijiya, fadin yadda su Hajiya suka shiga firgici ba zai misaltu ba, ihu suke yi suna kiran Munir,dariya Azima ta kyalkyale da shi ta ce

“Ya ri  ga ku mutuwa! Yanzu a cikinku wa zai bisa na biyu? Bari na kawo muku shi ku gan shi” Azima ta faɗa tana shiga dakin ta naɗo munir da jelarta ta zo ta jefar da shi a gabansu a tsakiyar parlour, wani kuka su zuby suka saka ita da baby hajiya kuwa jiki na kyarma ta takure jikinta gefe daya.

        A tsawace Azima tace

“NA CE A CIKINKU WA ZAI BISA NA BIYU!!?” cikin kuka da tashin hankali suka hau fadin tayi hakuri karta kashesu basu so su mutu, Azima tace

“Akwai abu daya da zan muku, ruwa zaku sha? Ko abubuwan da kuke sha a robobi zaku sha?” cikin kuka da majina da zufa suka ce ruwa, Azima tasa hannu ta janyo ruwa ta zuba a kofi uku ta ce

“Duk wanda baya son mutuwa ya sha wannan ruwan!” jikinsu na rawa suka dauka suka kafa baki suka kwankwaɗe suna kan bata hakuri, kamar da minti biyu tsakani Hajiya ta hau tari tana rike wuya, da sauri Zuby ta tashi tana fadin Hajiya meya sameki,nan ita ma ta hau riƙe wuya tana tari, Baby ma haka, tari sosai suke yi jini na fita baki da hanci, Azima ta miƙe ta ce

“BANA MANTUWA! BANA YAFIYA! NA RIGA DA NA ZUBA DAFI TA YATSAR HANNUNA!” tana gama fadi ta shiga ta dauki kayanta na fulani da Lantana ta wanke mata ta saka ta fice ta bar gidan.

         ????????????????

Kwanan Aziza biyu a asibiti jikin nata alhamdulillah duk da da ace taso zata iya warkar da kanta amma bata so ta sakawa su Mom da Sultana shakku a ransu su fara zarginta, sannan yanzu idan tace zata gudu bata san duniyar da Azima take ba kuma tana ji a jikinta duk inda Azima take bata shuka alkairi, abu biyu ne ya haɗe mata waje guda ya jagula mata lissafi, bata san taya zata fara neman Azima ba tunda basu al’karya daya, sannan bata san wani hali iyayenta suke ciki ba,duk da tana da yaƙini a kan Baffa zai kula da Hajja sosai shima zai kula da kansa, tana zaune tana tunani, wani dabara ne ya faɗo mata, wannan dabara kuwa shine ta fara yawon bin garurruka! duk garin da suka haɗe da Azima idan ta lumshe ido zata iya hangota ta cikin tauraronsu, da wannan tunani ta samu karfin guiwa,lumshe ido tayi ta shafi tafin hannunta amma bata ga Azima ba, a fili ta ce

“Hakan na nufin bamu gari daya kenan, wannan hajiyar (Mom kenan) ta kira sunan wannan yankin da kaduna ko? Ina gani gwara na tambayi wannan yarinyar tata sunayen yankuna sabida naje na dudduba Azima, amma kuma kafin na tafi dole ina bukatar kudi, hakan yana nufin dole na yi musu aiki dan na tara kudin neman Azima? Idan kuwa haka ne Banju ya cuci rayuwarmu,ga shi wahalar a kaina da Baffa yake karewa” ta karasa maganar da sakin kukan tausayi, tana sakin kukan su Mom da Sultana suna shigowa.

     Ganin tana kuka yasa suka karaso wajanta da sauri suna tambayarta ko akwai inda yake mata ciwo ne? ta girgiza musu kai alaman a’a, Mom ta ce

“Yarinya? Kiyi hakuri kodayaushe kina cikin kuka, ina yan uwanki suke? A wani ruga kuke a garin yola idan yaso gobe sai a maidaki” jin haka yasa Aziza kara sakin sabon kuka,inaa ai ba zata so ta koma ba tare da burin Baffa na su dawo tare da Azima ba, mafita daya ne shine kawai ta yi karya,cikin kuka ta ce

“Yan fashi ne suka fada rugarmu suka kashe mana kowa, nima da kyar na sha,dan Allah Hajiya ki taimaka mini na dinga yi miki aiki kina biyana,yanzu idan na barku ban san inda zan hadu da mutane nagari kamar ku ba dan Allah Hajiya!” Aziza ta fada tana kuka sosai,jikin Mom ne ya yi sanyi sosai, Sultana ma kwalla ya cika a idonta ta kalli Mom ta ce

“Mom mu dauketa kawai,tunda dama kinga Haule ta yi aure,ita wannan ma zata jima ” Mom ta ce

“To shikenan kira mana wani Dr ya zo ya rubuta mana sallama,dan munyi waya da Nawaz yace sai gobe ko jibi zai dawo,kuma yace idan har jikin nata da sauki mu koma gida, to gwanda gidan dai zaman asibiti ba dadi garesa ba”

“To Mom” Sultana ta fice bata jima ba suka dawo da wani likita ya rubuta musu sallama suka yi gida, dakin masu aiki dake kasa wajan cikin parlour bayan step dakin mai aikinsu na da Haule wacce tayi aure,bama iyakar Haule ba duk masu aikinsu nan ne dakin da suke zama,babban daki ne dasu babban gado da wardrope da toilet da komai da komai, Sultana ce ta nuna mata yadda zata yi amfani da komai,bayan ta nuna mata Aziza ta kalleta ta ce

“Na gode Anty Sultana” Sultana ta yi murmushi ta ce

“Ba komai mai kyau, amma meyasa kike son rufe fuskarki? Har yanzu baki saba damu bane?”

Cikin in-ina Aziza ta ce

“Inada matsalar ido ne, tun ina yarinya bana son haske, sannan bana iya kallon mutane da idona shiyasa mahaifiyata ta bani wannan mayafin ina lullubi da shi, gashi na kuma na fiddo da shi dan ya rufe min daya idon da zan dinga ganin hanya”

“Ayya Subhanallah! Idan Brother ya dawo zan gaya masa sai ya duba miki idon, watakila idan aka dace sai ya miki magani”

Da sauri Aziza ta ce

“A’a Anty Sultana karki gaya masa halittatace a haka aka haifeni” 

“To shikenan,bari na bar ki ki huta sai na shigo anjima,idan kika warke sosai akwai abunda zan dinga koya miki,ina sonki da ƙawa! kinga bana da ƙawa bana shiga hidimar mutane amma ke kin shiga raina” murmushi kawai Aziza ta yi dan ita kadai tasan yaƙin da yake gabanta, tashi Sultana ta yi tana fadin

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button