AZIZA DA AZIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

AZIZA DA AZIMA 41-50

“Ina dai basu muku komai ba ko” cewar Hajiya Habiba

“E Ammi basu mana komai ba”

“Na godewa Allah, da me zan cewa Hajiya yara daga zuwa biki ni Habiba,tana can hankalinta tashe wallahi, dan ma dai tana da karfin zuciya” nan aka shiga jajinta lamarin, aka ce su shiga su huta Sultana tace sam ai yanzu kam gida zasuyi, anyi-anyi su bari sai anjima tace sam,ganin haka yasa Hajiya Habiba cewa to jami’an tsaro su rakasu har kaduna har cikin gida, kayansu kawai aka fiddo musu aka sa a both, Sultana ta rungumi Sulaiha ta ce

“Ƙawata kuyi hakuri fa jiya hankalinku ya tashi ga shi ko gidanki ba a kai ki ba”

“Haba Sultana ba dole ba”

“To shikenan ai muna lafiya, kiyi hakuri ba zan samu zuwa gidan ba amma na miki alkawari zan zo idan an kwana biyu, a sha amarci lafiya” daga haka sukayi sallama wata ƙawar Sulaiha ta mikawa Sultana wayarta da kafa ɗayan takalmin Aziza,bayan mota suka shiga jami’an tsaro suka rakasu a baya, har kaduna.

@@@@@@

          Suna isa da gudu Sultana ta shige gida,Mom tana tsaye a parlour ta kasa zama, Sultana na shigowa ta ce “MOM!?” da sauri Mom ta juyo tace

“Sultana” rungumeta tayi, cikin hawaye Mom ke tambayar lafiyar Sultana, shigowa Aziza da yan sanda sukayi, Mom na ganin Aziza ta yi saurin zuwa ta rungumeta tana tambayar lafiyarta,jikin Aziza ne ya kara sanyi, da yanzu ta gudu wani tashin hankali zasu shiga? Da yanzu wannan abun bai faru ba da shikenan ta b’ata rawarta da tsalle, hakika zamanta dasu akwai wani babban sirri da Ubangiji ya boye, shin yanzu su gayawa Mom gaskiya ne ko yaya zasuyi?” Mom ce ta shafo fuskarta tace

“Kina lafiya ‘yata?”

Aziza ta gya ɗa kai,nan yan sanda suka kara yiwa Mom bayani kafin Mom ta musu godiya suka fice,suna fita Hajiya Habiba na kira,nan Mom ta shaida mata ta kwantar da hankalinta sun zo gida lafiya, dama tsautsayi ai baya wuce lokacinsa Allah ya kiyaye na gaba kawai, daga haka suka yi sallama aka rabu lafiya, Mom ta kallesu tace

“Bakuyi wanka ba ko?” suka gya ɗa kai

“Kuje kuyi wanka ku kwanta ku huta idan kuka tashi sai ku ci abinci, tunda yanzu ana neman shaɗayan safe ne” suka amsa da to, Aziza a sanyaye ta shige dakinta, Sultana kuma ta haura sama, sai da ta yi waya da Khalil dinta ta tabbatar masa tana lafiya dan hankalinsa ya tashi bai rintsa ba jiya, ta ba shi labarin ai Aziza ce ta taimakesu, amma bata gaya masa komai a kai ba, dan tayi alkawari ko wa Mom ne ba zata gaya ba har sai Aziza ta yarda, wanka ta yi sannan ta bi lafiyar gado dan bacci takeji sosai, haka ma Aziza ita ma wankan ta yi ta kwanta zuciyarta a cin kushe, ga tunani fal a cikin ranta,ji take kamar kanta zai fashe, ta ɗau minti talatin tana juyi kafin bacci ya kwasheta.

       Basu farka ba kuwa sai hudu na yamma,Mom ma bata tashesu ba, ta dai musu odern abinci, bayan sun farka ruwa suka sake watsawa kafin suka ji sun watstsake, kasancewar suna fashin sallah dukkansu shiyasa basu wani damu ba, Sultana ce ta fara fitowa ta shiga dakin Mom ta sameta suna waya da Nawaz,sai da suka gama Mom tace

“Kin tashi? Kinyi sallah?”

“A’a Mom ina fashin sallah, Aziza ma haka”

“Yaushe kuka fara?”

“Ranar da muka isa zaria”

“Ok ya yi kyau,banda shan zaƙi dai da abu mai sanyi”

“To Mom”

“Kije ki ga idan Azizan ta farka,ku ci abinci”

“To Mom, amm Mom Khalil yace zai dawo a satin nan”

“Lafiya dai ko?”

“Nima ban sani ba, amma yace ya fasa cike sauran watannin” gya ɗa kai Mom tayi ta ce

“Nima maganar da muke yi kenan da Nawaz yace zasu dawo, jin abunda ya faru yace gwara kawai ayi auren kwanan nan a kaiki hankalinsa da nawa ya kwanta nima kuma nayi na’am da abunda yace, dan haka yace zasu dawo dukkansu shi da Son,idan suka dawo sun dawo kenan, nan da wata daya” shuru Sultana tayi dan bata so haka ba, ba tare da tayi magana ba ta fice, kasa ta sauko bata ga Aziza a parlour ba dan haka ta zuba musu abincin tayi dakin da sallama Aziza na zaune a bakin gado, tana sallaman Aziza ta amsa tana shirin rufe fuska, Sultana tace

“Babu amfani ai tunda nasan komai, zo muci abinci” ta fada tana zama kan carpet, zamowa daga gadon Aziza tayi ta kalli Sultana ta ga jikinta a sanyaye Aziza ta ce

“Anty Sultana yana ganki haka akwai matsala ne?”

“Babba ma kuwa Aziza, Khalil jin abunda ya faru yace zai dawo a cikin satin nan, Yaya kuma yace shima zai dawo nan da wata daya dan ayi aurena hankalinsu ya kwanta shi da Mom,kuma Mom tace shi da amininsa zasu dawo, dama yanzu dawowa mai gabadaya zasuyi” Aziza ta ce

“A’a bangane ba,ina da tambaya, shin Hamma Khalil ba shi bane abokin Hamma Nawaz ba wanda suke kasa daya?” dariya Sultana tayi ta ce

“Taya? Khalil fa shi yana paris ne, su Yaya Nawaz kuma suna america ne, sunan babban aminin Yaya ba Khalil bane, ke yanzu duk zamana dake baki san my husband to be ba? sunan babban aminin Yaya Nawaz *AL’MAZEEN NE* shi kuma ɗan Kano ne ba dan kaduna bane,gidansu ne Mom tace zata aikemu nace bazan je ba.

       ????????????????

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button