Labarai

Sheikh Gumi ya kafa kungiyar kare hakkin Fulani Makiyaya

Sannannen Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana kafa Kungiyar Kare Hakkin Fulani Makiyaya.

Ya bayyana hakan ne a yayin wa’azi a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna inda yace kungiyar za ta saurari koken makiyayan tare da bi musu hakkinsu.

Gumi ya sanar da cewa sabuwar kungiyar mai suna NORIC za ta samu shugabancin Farfesa Umar Labbo kuma tana kira ga makiyayan da su kai kokensu.

Kaduna – Fitaccen malamin addinin Musulunci, Ahmad Gumi, ya sanar da cewa ya kafa kungiyar assasa kare hakkin Fulani makiyaya.

Gumi ya bada sanarwan kafa kungiyar wacce za a kira ta da Nomadic Rights Concern (NORIC) a yayin tafsirin watan Ramadan a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna.

Ya ce kungiyar za ta tattaro tare da bayyana irin cin zarafi da take hakkokin Fulani makiyaya da ake yi, Premium Times ta ruwaito.

Mun ga dacewar kafa Kungiyar Kula da Hakkokin Makiyaya, NORIC, wacce za ta samu shugabancin Farfesa Umar Labbo. NORIC za ta zama wata hanya da makiyaya za su mika korafinsu da damuwarsu zuwa ga hukumomin da suka dace.

“Da yawa daga cikinsu sun yi korafin cewa sun yi rashin ‘yan uwansu. Wasu kuwa suna gidajen gyaran hali na tsawon shekaru ba tare da suna san laifukansu ba ko kuma na gurfanar da su.

“An kafa wannan kungiyar ne domin magance wadannan matsalolin kuma ana fatan makiyayan za su bi hanyar da ta dace wurin mika kokensu ba tare da tada hankula ba,” Gumi yace.

Ya ce makiyayan za su iya mika korafe-korafensu ga NORIC, wanda zasu taimaka wurin daukan matakin shari’a don kwato musu hakkinsu.

Ku yi koyi da ‘yan uwanku da suka tuba 

Gumi ya yi amfani da wa’azin wurin kira ga ‘yan bindiga da ke barna a kasar nan ballantana arewa maso yamma da su rungumi zaman lafiya tare da ajiye makamansu.

“Mun yi kira gareku da ku ji tsoron Allah tare da daukar hanyar zaman lafiya. Kuyi koyi da wasu daga cikinku da suka ajiye makamai, suka saki wadanda suka sace, suka tuba kuma suka nemi yafiyar Allah,” Gumi yace.

A kan farmakin jirgin kasa na Kaduna, malamin ya yi kira ga ‘yan bindigan da su sako wadanda suka sace tare da mika korafinsu kai waye.

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button