AZIZA DA AZIMA 41-50

“Yanzu mu fara biyawa mu karbo kayanki na wajan tela, yawwa dama ina so na tambayeki,kin iya karatu?”
Aziza ta gya ɗa kai ta ce
“Nayi sauƙan al’kur’ani mai girma a kauyenmu, sannan na karanta litattafai da dama,na iya rubutu kamar irinsu ko da wasika idan Baffanmu zai rubuta idan rubutun tayi masa yawa ina tayasa rubutawa amma ba da irin rubutunku ba, da harafin su Alif kamar ajimi haka”
Sultana ta ce
“Ahh Ma sha Allah ki ce malama ce” ta faɗa a mamakince dan kuwa ta sha mamaki ɗin sosai, murmushi Aziza ta yi ta ce
“A’a ina dai kan neman ilmin”
To shikenan zan koya miki karatun hausa da turanci ta yadda zaki iya duka,idan har kina ganewa da wuri zan cewa Yayana ya nema miki skull mafi kusa da saurin ganewa,sannan matsalar idonkin nan ya nema miki medicalglass”
“A’a Anty Sultana karki gaya masa,ki bari kawai idan kika koya mini ma ya isa, idona kuma haka yake haka aka haifeni dan Allah ko wa Mom ne karki ce mata komai” Sultana ta yi murmushi ta ce
“To shikenan”
Bayan sunje sun karbo kayan suka koma gida a daki suka samu Mom, Mom tace “sannunku da dawowa ‘yan matana har kun dawo” Aziza ta duka kasa Sultana kuma ta zauna a gefen gadon Mom, ta ce
“E Mom mun dawo barka da gida, dazu muna shagon salon Yaya ya kirani wai yana hanya mun kiraki baki daga ba”
“E munyi waya da shi daga baya,kema na kiraki bai shiga bane, lokacin da ya kirani ashe na tashi na bar wayar a parlour shiyasa, yanzu dai ku tashi kuje ku gyarawa Yayan naku dakinsa, idan kun gama sai ku shiga kitchen” dan mom bata yarda da lalaci ba dan babu irin girkin da Sultana bata yi shiyasa da shike basu da yawa a gidan kuma ba yara garesu ba shiyasa mai aiki daya kawai suke dauka, suka amsa da to, Aziza ce ta fara tashi ta fita, Sultana ta ce “zo muje part din Yayan” tayi gaba Aziza na binta a baya, suna fita sai ga wani ɗan ƙofa madaidaici Sultana ta buɗe suka shiga,parlour a kasa har da step wani sashene mai zaman kansa a wajan tabbas an tsara parlourn ya tsaru, Aziza matowa tayi da kallon parlour,idonta ne ya sauka a wani pic babba a parlourn shi daya da kuma wani a gefe su biyu, dukkansu fuskarsu babu murmushi,tabe baki Aziza ta yi,dan ita bata ga abum gyara a wajan ba,ganin yadda take kallon hoton ne yasa Sultana fadin “wannan shine Babban Aminin Yaya baya da wani sama da shi, a tare suke a america tare suka yi karatu gabaɗayansu kuma likitoci ne, karki ga fuskarsu haka a haɗe barin ma yadda kika ga na Abokin Yaya,to wlh yafi Yaya Nawaz sauƙin kai,kawai dai shi magana ce bai cika yi ba da dariya,amma idan kina neman zafin zuciya kika samu Yaya Nawaz kin gama” jinjina kai Aziza tayi ba tare da tayi magana ba,suka hau sama yadda k’asan ya tsaru haka ma saman ya tsaru haka de ta dinga bin Sultana har suka gama suka saka masa turaren wuta sannan suka wuce kitchen suka hau girki, dama Sultana na koyawa Aziza yanayin girkinsu,duk abunda ta koya mata sau daya kuma cikin ikon Allah ta riƙe kenan babu mantuwa, idan tazo yi kuma sai tayi wanda yafi na Sultana daɗi, haka suka yi girki a tare suka gama duk da ba wani hira sukeyi ba,tunda Sultana ta fahimci Aziza bata son yawan magana yasa itama bata takura ba,ita kuwa ba zata fahimci tashin hankalin da take ciki bane,bata fata su gano cewa ita ba mutum bace macijiya ce har su rabu tinda zama dasu na wucin gadi ne, bayan sun gama girki Sultana ta ce
“Aziza je kiyi wanka ki canza kaya, sai ki kwanta ki huta idan kika huta da dare sai mu fara karatun ko?”
“Dazu fa kafin muje wajan wankin kai nayi wanka”
“E na sani,ai ita tsafta bata yawa sai dai tayi kaɗan, zaki dinga yi ne dai-dai gwargwaɗon iyawarki,kuma gwara ki saba da shi tun daga yanzu dan bamu sani ba watakila Mom ta samu surki a nan garin” wani wawan faduwar gaba ne ya ziyarci Aziza ta sake maimaita kalman sirki a ranta, da kyar tayi murmushin karfin hali ta amsa da to a sanyaye sannan ta wuce daki,itama Sultana sama ta haura, Aziza na shiga daki ta wuce toilet, tana shiga ta maida kofa ta rufe ta rintse idonta ya sake komawa fari, fatar jikinta ma fari yana sab’ulewa, daga ƙasarta ta fara rikiɗewa nan ta zama rabi mutum rabi macijiya sannan ta zauna a gefen bath din wanka ta hau kuka, tunowa da maganar Arɗo da Baffa Mandi, na cewa ba zata warke ba har sai sunyi aure, kuma ita warakanta yana tattare da Azima wacce bata ma san a wani duniya Azima take ba, sai bayan da ta gama shan kukan nata kafin ta yi wankan ta fito.
????????????????
Sai huɗu Nawaz ya samu damar isowa, ko da ya iso wajan Mom ya nufa nan take masa sannu da zuwa tare da fadin
“Nawaz sai yanzu?”
“Wlh Mom motata ce ta ɗan samu matsala a hanya sai da aka mata gyara”
“Subhanallahi! Karfen nasara babu tabbas Allah ya kara kiyayewa”
“Amin Mom bari na samu na ɗan watsa ruwa sai na fito na ci abinci,ina Sultana?”
“Ba mamaki tana dakinta,bata ji shigowarka ba ai da ka ganta da gudu” murmushi ya yi kawai ya fice, part dinsa ya shiga ya samu na tashin kamshi bai tsaya wani bata lokaci ba ya yi wanka ya shirya ya fito, ji yayi ba zai iya komawa babban parlour ba dan haka ya kira Sultana ta kawo masa abincin part dinsa.
*PAID.*
????️=4️⃣3️⃣↪️4️⃣4️⃣
Da sauri Sultana ta fito tana kwalawa Aziza kira, fitowa Aziza ta yi ta ce
“Gani Anty Sultana”
“Yawwa Aziza dan Allah zo ki tayani kwashe tray zan kai wa Yaya abinci ashe ya dawo”
“Oh har ya dawo?”
“Nima wlh ban sani ba sai da ya kirani a waya”
“Ayye” cewar Aziza ta duƙa tana daukar tray din da Sultana ta gama jera su plates, sannan itama ta dau ɗaya tayi gaba Aziza ta rakata a baya.
Da sallama suka shiga Sultana ce a gaba sai Aziza dake binta a baya kanta a duƙe cikin hijabi gabanta na faduwa, yana kwance a dogon kujera yana sanye da jallabiyya, amsa sallamar tasu ya yi yana tashi zaune, da sauri Sultana ta ajiye tray din hannunta ta zauna kusa da shi tana masa sannu da zuwa,kanta ya shafa cikin kulawa yana amsawa, duƙawa kasa Aziza ta yi bakinta na rawa ta ce
“Ina wuni *HAMMA NAWAZ* ya hanya?” rassrassras! gaban Nawaz ya faɗi ya ƙura mata ido amma ta gefen ido yana kallon yadda take rirriƙe yatsun hannunta jikinta na rawa daga nesa yake karantar yanayinta duk da ta boye fuskarta cikin hijabi sai saitin ƙaramin bakinta da yake iya hangowa wanda shi ma ke b’ari,
“HAMMA NAWAZ!” yake ta nanatawa a ransa, Aziza kuwa jin bai amsa mata gaisuwarta ba alhali ya amsa na kanwarsa yasa ta tashi a hankali jiki a sanyaye zata fita, watakila baya amsa gaisuwar masu aiki, har ta kai bakin kofa sai taji Sultana na faɗin Aziza ina kuma zakije?”
“Amm dama Anty Sultana dama akwai kayan da ban….kwa. She…ba…ina…so..ne…naje….na kwashe” ta karasa maganar da in-ina tana fita da sauri, cikin fuskar tausayi Sultana ta juyo ta kalli Yayanta ta ce
“Bro,wlh Aziza bata ji dadi ba, ta gaisheka baka amsa ba fa,kuma kamar ma naga tsoronka takeji”
“Za ki yi serving ɗina ne ko zaki cika min ciki da magana?” ya faɗa ba tare da ya kalleta ba, kasancewar tasan halinsa yasa ta zuba masa abincin ta ajiye masa komai sannan ta fice itama,tana fita ya dauki spoon zai kai abincin bakinsa sai ya tsinci kansa cikin rashin jin dadin amsa gaisuwarta da bai yi ba, HAMMA NAWAZ! ya faɗa a fili ya saki murmushi jin yadda ta kira cike da harshen fullaci kuma sai sunan ya yi daɗi a bakinta, da kyar ya lallaba ya ci abinci dan kuwa yaji dadin abincin sosai yaci yasha zobon da suka haɗa ya yi hamdala, nan ya zauna suna waya da amininsa yana gaya masa ranar thursday In sha Allahu yana hanya zai bi jirgi amma sai ya ƙara komawa ta abuja, Allah ya kawo shi lafiya ya yi masa,yana kan waya har aka kira sallar magriba dan haka yace masa za shi masallaci suka yi sallama akan cewa sai sunyi waya anjima, alwala Nawaz ya yi ya tafi masallaci bai dawo ba sai da ya haɗa da isha’i, ko da ya shigo gida babban parlourn gidansu ya wuce da sallama ya shiga a lokacin Aziza na riƙe da kaskon turaren wuta ita kadai ce ma a parlourn, jin sallamarsa yasa jikinta ya dauki rawa wanda bata san dalilin hakan ba, cikin rawar murya ta amsa sallamar ta shi ta ajiye kaskon hannunta tana shirin shigewa daki da gudu taji muryarsa kamar daga sama