AZIZA DA AZIMA 41-50

“Ya kike? ya jikin naki? Yanzu babu inda yake miki ciwo ko?” ya faɗa lokaci daya,cak Aziza taja ta tsaya,a iya saninta Sultana da Mom suna sama,to kenan da ita yake yi? take tambayar kanta, bata amsa ba bata juyo ba sai da taji ya sake fadin
“AZIZA baki ji ina miki magana ne?” sai a sannan ta juyo murya na rawa ta ce
“Alhamdulillah na warke” tana gama fadi ta shige daki, shuru ya ɗan yi yana nazartan yarinyar daga baya kuma ya yi tsaki ya hau sama,dakin Mom ya je ya kwanta a gadonta suna hira, Mom ta ce
“Bana ma kenan a kasar waje zaku sake yin Azumi ga Azumi ya ƙarato, meyasa ba zaka sa amininka ya dawo nigeria kuyi azumi a gida ba? Bana dai ace kunyi sallah a kasarku tare damu”
“Mom kema kin san ba zai dawo ba ko da na faɗa masa, azumi kuma In sha Allahu mai zuwa idan rai ya kaimu ai muna nan a gida In sha Allah” Mom ta sauke ajiyar zuciya ta ce
“Ai ya kamata,ni na ƙagu ku dawo dan ku nemo matar aure ku aura,barin ma Son yana da bukatar mata wacce zata kula da shi”
“Ai ya samu Mom”
Mom ta ce
“A’a gwara dai fa ya samo mai tarbiyya da natsuwa da hankali” Nawaz ya tabe baki ya ce
“Humm wanda yake fadin zai aura ni kwata-kwata bata min ba,bamu shiri da ita ko kadan amma shi yace zai aureta,kuma abun takaicin fa Mom shima ba sonta yakeyi ba”
“To ina ruwanka? kai fa matsalarka Nawaz zafin zuciya” Mom ta fada tana kallonsa
“Mom ai ba zan can ina ruwana bane ko zafin zuciya,magana ce ta gaskiya,kuma ai abunda ya shafesa ya shafeni”
“To kawai ka tayasa da addua shine babban soyayyar da zaka ci gaba da nuna masa”
“In sha Allah Mom” daga haka suka ci gaba da hirarsu,bai baro dakin Mom ba kuwa sai sha biyu na dare yana fitowa ya shiga dakin Sultana bata nan,tana can dakin Aziza tana koya mata karatu,cikin ikon Allah Aziza ke ganewa, da bai ganta a dakin ba ya yi tunanin ko tana toilet ne dan haka ya wuce part dinsa ya kwanta, sai sha biyu da rabi Sultana ta miƙe tana fadin
“To Aziza bari mu dakata da karatun haka sai Allah ya kaimu gobe kuma, yanzu akwai wani horror series film din da nake kalla, 12 ake farawa a gama 1:30 ga shi yanzu har sha biyu da rabi sai dai na kalli karashi,ko zaki zo muje ki kalla ne?” Aziza ta ce
“Me hakan ke nufi? shi horror din” sai da Sultana tayi dariya kafin ta ce
“Ina nufin fina-finan dodanni, kamar irinsu abun tsoro haka da film din macizai!” rassssss! gaban Aziza ya buga ta yi sauri dago fuskarta ta kalli Sultana ta tsakiyar gashinta da ya rufe mata fuska,Sultana ta kwashe da dariya ta ce
“Matsoraciya kawai,daga faɗa miki har kin firgita, wlh kuma fa Yaya ya hanani kalla har cewa yake min ranar da na fara ganinsu a zahiri zan sani, yanzun ma inada tabbacin ya tafi part dinsa,kinga sai da safe” tana fadi ta fice ta bar Aziza da zare ido tana tunanin ranar da Sultana zata ganta a macijiya mai zai faru? Saurin kau da tunanin ta yi tana fadin “taya ma hakan zata faru?” ajiye tunanin tayi a gefe ta shiga ta ɗauro alwala ta tada sallah,ta jima tana addua tana kuka tana neman taimakon mahaliccinta.
????????????????????
Kwana a tashi ba wuya a wajan Allah, Azima duk hankalinta ta karkata shi wajan sakawa su Maman Hanan da Maman Beenah ido ganin manaƙisan da suke kullawa wanda bai ji ba bai gani ba, ta sha jin haushin kanta a kan ƙutse da take yiwa wanda bai san da ita ba kamar yadda itama bata san da shi ba, ga shi duk sadda ta yi yunkurin barin gidan sai taji kamar an ɗaure mata kafafu,wannan gida ya zame mata karfen kafa.
????????????????
Ana gobe Nawaz sai tafi abuja jibi kuma zai wuce america ya yi wani mugun mafarkin da ya gigita duniyarsa, Aziza ce ya gani a jejin da yafi na kullum muni tana kuka tana miƙa masa hannu ya taimaketa, kar ya tafi ya taimaka mata,ƙiri-kiri ya ganta a macijiya.
????????????????
A Lallaba yau aiki yamin yawa????????♀️
MOMYN AHLAN✍????
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????
????✨ *AZIMA DA AZIZA*????✨
(???? _Macizai ne_????)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*????????
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)_
_Follow me on wattpad,@Fateemah’0_
????????????????????
????????????????
MOMYN AHLAN✍????
GARKUWAR MACIZAI????????
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????
????✨ *AZIMA DA AZIZA*????✨
(???? _Macizai ne_????)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*????????
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)_
_Follow me on wattpad,@Fateemah’0_
????????????????????
*PAID.*
????️=4️⃣5️⃣↪️4️⃣6️⃣
Hakika wannan mafarki ya tayar masa da hankali, ko da ya farka da washe gari jikinsa a mace, da kyar ya gama shiryawa ya fito ya yiwa Mom sallama da shike driver ne zai kaisa ya dawo, shiyasa zasu yi fitar wuri, bayan sun gama sallama da Mom suka rakasa har bakin mota, sai ware ido yake yi inda zan hangi Aziza amma bai ganta ba, kallon Sultana ya yi ya ce
“Ina Aziza ne?”
“Ina ga tana dakinta bari na dubota”
“Noo leave her” ya faɗa yana jan murfin mota Mom tana kan yi masa addua yana amsawa da amin, Mom da Sultana basu koma cikin gida ba har sai da motar ta fice a gate gabadaya aka ja gate din kafin suka koma,ko da suka shiga Sultana ta wuce dakin Aziza ta sameta zaune tana ninke kayan Mom da ta wanke, Sultana ta ce