AZIZA DA AZIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

AZIZA DA AZIMA 41-50

“Aziza baki fito kinyiwa Yaya Allah ya kiyaye hanya ba har sai da ya tambayeki wlh”

“Ayye ban san ya fita ba da shike ina nan ina ninke kayan Mom ne” ta faɗa ba tare da ta dago ba, alhali taji sadda suka sauƙo dasu Mom har sadda ya shiga mota duk tana tsaye tana leƙensu ta window, sai da ta ga motar ta fice a gidan kafin ta koma daki, Sultana ta ce

“To ke miye haɗinki da kaya ina Buba yake?”

“Wlh jiya ne yaji ciwo a hannu shiyasa na karba kayan na wanke”

“Subhanallahi! Allah ya kiyaye gaba amma ai sai ki faɗa ba wai ki wankesu da kanki ba da an nemo mai wankewa,yanzu dai ki gama ɗin sai ki zo muje Mom ta aike mu karbo kulolin azumi wanda ake abincin sadaka dasu gidan wata kawarta a nan malali”

“To Anty Sultana bari na karasa gani nan zuwa”

“To kiyi sauri ki shirya, saura kuma wlh ki zunduma hijabin kin nan, dan Allah ki nemi abaya ki saka ki yafa gyale akwai gidan da zaki rakani mu shiga tare Mom ta bamu sako ma a gidan” da to Aziza ta kara amsa Sultana, Sultana tana fita Aziza ta sauke ajiyar zuciya tana fadin “Allah ya kaika lafiya Hamma Nawaz, ba mamaki ba zaka dawo ka sameni ba” ta fada tana mai lumshe ido, saurin kwashe kayan ta yi ta kaisu dakin guga, sannan ta koma ta shirya shap-shap tasa doguwar abaya baƙi ta dauki ash’color din gyale taja gashin kanta ta nannaɗesa ta daure a tsakiyar kanta ta dau hula ta saka kafin ta dauki mayafin ta yi lullubinta kamar kodayaushe,ko da ta fito parlour Mom da Sultana suna parlour Mom tana kara ba wa Sultana saƙo, itama ta yi shigar bakin abaya, tana fitowa Sultana ta ce

“Yawwa ko ke fa” murmushi kawai Mom tayi ta ce

“Ma sha Allah ‘yan matana, Allah ya kawo miji na gari,kodayake ma yanzu kam sai dai nayiwa ‘yata Aziza dan ita Sultana rana kawai za a saka” 

A sanyaye Aziza ta ce

“Lahh Anty Sultana shine baki gaya mini ba? To Allah ya kaimu Allah ya sanya alkhairi” Mom ta amsa da amin Sultana kuwa ta dukar da kai tayi tana murmushi,bayan Mom ta gama basu saƙon ta ce

“Dan Allah karku kai magriba,Sultana karki ga dan Nawaz baya nan ku kai magriba kin san dai ko da wani lokaci kiran waya yake yi,da ya kira kuma zai ce ina kike, dan haka kuyi ku dawo”

“In sha Allahu Mom” suka faɗa suna ficewa, duk inda aka aikesu nan suka je, har gidan surakanan Sultana, a gidan kuwa wani ƙaninsa ya ga Aziza sai kallonta yake yi, har sai da ya biyo Sultana yana faɗin

“Anty dan Allah wannan fa?”

Murmushi Sultana ta yi tana faɗin

“Kanwata ce,kana ciki ne?”

“E wlh Anty ina ciki” 

“Lallai kam to sai ka gayawa Yayanka”

“To Anty shi da baya kasar ki kirasa ki fara gaya masa,kinga ma sai a haɗa bikin da naku”

“Ahh lallai Walid baka da kunya, wato ma a haɗa da namu?”

“E mana Anty,kodayake ma ku da ba a saka ranar ba, sai a fara namu kafin Yaya ya dawo ke kuma kin gama skull kafin nan kema kin kara girma Anty” ya faɗa cikin tsokana, Sultana ta ce

“Wlh Walid ka rainani,zan haɗaka da Yayanka kuwa”

“Allah ya baki hakuri Anty,ni dai dan Allah ki fara min kamu”  banza da shi Sultana ta yi ta shiga mota ta cewa driver yaja su tafi,basu tsaya ko ina ba sai gida,suna isa Mom ta musu sannu da dawowa tace musu idan sun huta su shiga kitchen suyi girki suka amsa da to.

        @@@@

Da washe gari sai dare Mom ta samu damar yin waya da Nawaz ya shaida mata cewa ya isa lafiya, Mom ta ce

“Ma sha Allah haka akeso,Allah ya taimaka ka gaishemin da son”

“Zaiji Mom,ina Sultana?”

“Suna can daki ita da Aziza suna karatu, dama kuwa ni ina son yi maka magana a kan yarinyar inaso zan nema mata makaranta, tana da kaifin basira, wlh basu kai sati da fara karatu ba amma karka ga yadda kanta ke ja,abun mamaki” Shuru Nawaz ya yi na dan wani lokaci har sai da Mom ta kuma cewa

“Nawaz bakaji me nace bane?”

“Naji Mom duk yadda kikayi dai-daine,  Allah ya baki lada”

“Amin Nawaz” hira suka ɗan taba kafin suka yi sallama da shi.

       ????????????????

Bayan sati biyu da tafiyar Nawaz abubuwa da yawa sun faru daga ciki kuwa harda fara azumi da aka yi, sosai a wannan wata ta ramadan Aziza ta dage da addua Allah ya takaita mata wahalar neman yar uwarta su samu su koma gida, dan ta ƙosa ta koma ta ga iyayenta,kullum da Hajja take kwana take tashi a ranta har ma da Baffanta, ta maida lamuranta ga Allah.

    Ta bangaren Azima kuwa ta kasa gane meke mata dadi, dama duk azumin duniya ita kam ba yinsa take yi ba, to wannan din ma haka ta kasance dan ko daya bata yi ba, sosai kuma take sakawa su Hajjaju ido, duk wani ƙullin da suke yiwa AL’MAZEEN.

       Ana azumi lafiya da yardan Allah, tunda Nawaz ya bar nigeria ya kasa samun natsuwa, ga mafarkin Aziza da ya gallazawa rayuwarsa wanda ya rasa ya zaiyi da wannan mafarki, ga shi ya kasa gayawa kowa, wanda hakan har rama ya fara saka shi, wanda da an tambayesa zai ce azumi ne kuma ya haɗa masa da ba a gida yake yi ba shiyasa.

         Ana saura kwana uku sallah Sultana ta kai musu dinki wajan telarta inda ya cire musu zuƙa-zuƙan dinkuna na gani na fada, laces kala biyu, atampa kala uku, sai shadda da material kala ɗaɗɗaya, da gyalensu da takalminsu dasu sarƙa da ɗankunne, da komai da komai, hakika Mom ta yi kokari,Sultana kuwa ta yi bajinta wajan zabo musu kaya masu kyau, ita ma Azima anyi mata, amma sam basu gabanta dan bata saka a ranta zata yi wani kwalliyar abu sallah ba.

       Ana gobe sallah sai aikin suke yi dukkansu a kitchen har da Mom, Sultana ta ce

“Mom wlh zan yiwa Walid ba dadi, kinga yadda ya takura min wai yana son Aziza?” Mom ta yi murmushi ta ce

“Kai yarinta, duka-duka nawa kike bare kuma Walid? to kuma aje ga maganar Aziza wacce take da 15, Aziza ki maida hankalinki a kan karatunki kinji ko? In sha Allah bayan sallan nan zaki fara zuwa university dinsu Sultana tunda Allah ya baki kwakwalwa karki biyewa shirmen Walid kar ma ki fara kulasa, idan Khalil yaji ma ransa ne zai b’aci” Aziza a ranta ta ce

“Ina kuwa nake da lokacinsa,da yasan wacece ni ba zai so kara yin magana da mai irin sunana ba ma” a fili kuma ta ce

“Ni Mom ina da burika da yawa bana da lokacin kulasa”

“Yawwa Azizata” cewar Mom suka ci gaba da aiki har karfe sha biyun dare kafin suka tattara suka kwanta, da washe gari tunda sukayi sallar asuba basu koma bacci ba, abinci sukayi dukkansu har da Mom, karfe takwas da rabi suka gama, Sultana ta ce

“Aziza kiyi wanka da sauri ki zo muje masallaci” Aziza ta amsa da to.

        Wanka sukayi suka saka shaddarsu, sannan suka saka hijabansu mai alkebba da takalmansu, suka fito har da Mom itama da ta dake cikin lace dinta,  gabadayansu zasuje masallaci dan Mom tace abu daga shekara sai shekara nan ma sai mai tsawon rai wanda Allah ya nufesa da gani.

    Haka akayi idi lafiya, sai fatan Allah ya amshi ibadunmu na alkhairi ya yafe mana kurakurenmu amin.

@@@@@@

   Bayan sun dawo gida, nan yan uwa da abokan arziki suka hau zuwa ana yiwa juna barka da sallah, masu kawo abinci suna kawowa wa inda ake kai musu ana kai musu, Mom tana haɗawa tana bayarwa ana miƙawa bayin Allah, dasu lemuka da purewater, da kuɗi haka Mom ta dinga rabo, Sultana kuwa tana cikin yan uwanta ana shan su pics ana gaisawa an dade ba a hadu ba, Mom ce ta shigo babban parlour ta kira sunan Sultana ta ce

“Sultana ina Aziza ne kam?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button