AZIZA DA AZIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

AZIZA DA AZIMA 41-50

“Azizi baby, ga anko ɗinmu fa”

“Ankonmu kuma?” Aziza ta faɗa tana cikin mamaki tana ɗaga kayan, Sultana ta ce

“E mana, zamu je biki  ne ba tare da kinyi anko ba? Wlh muna zuwa zaki zama kamar bare, shiyasa da na tashi na cewa Bros Nawaz ya turo mana da kudi nayi mana mu biyu” shuru Aziza ta yi sai kuma ta sa kuka, Sultana ta ce

“Miye haka kuma Aziza?” cikin kuka Aziza ta ce

“Anty Sultana, anya dawainiyyar ba zaiyi yawa ba? aiki nake muku amma kun maidani tamƙar yar gida, ni kuwa dame san saka muku? Sai dai na bi ku da addua ke da Mom,Allah ya saka muku da mafificin alkairi” hannu Sultana tasa tana sharewa Aziza hawaye ta ce

“Ni da Mom kawai? Shi kuma Yaya ɗin fa! Yana yawan tambayarki wlh idan muna waya da shi, Aziza kin riga da kin shiga ranmu ne wlh, muna jinki ne a jikinmu, shekaran jiya Mom ke faɗamin cewa ita tana miki kallo ne tamkar ita ta haifeki,kuma tana tausaya miki na rashin iyaye da yan uwa da kika yi, tace ba zata taba wulakantaki ba, dama wulakanci mu ba halinmu bane, duk wanda ya riƙe maraya tsakani da Allah,Allah zai ba shi lada, In sha Allahu ko neman aurenki aka zo yi ba zamu taba cewa ke ba yar gidan nan bane, Allah ne ya saka mana kaunarki a ranmu, sabida hankalinki da natsuwarki, wlh Aziza ina jinki tamkar kanwata uwa daya uba daya, a rayuwata ina son na ganni da ƙanwa, amma ana haifata Allah ya dauki ran mahaifinmu, har kwanan gobe Mom taki kara aure, Yaya shike mana komai da shike Allah ya dafa masa, idan har Allah ya baka dama da dukiya amfaninka shine kai ma ka taimaki wa inda basu da shi, dan haka ki daina sa damuwa a ranki ki saki jikinki nan gida ne, bari naje nayi waya da My Khalil” share hawayen da ya sake zubo mata Aziza tayi ta ce

“Na gode sosai Anty Sultana, Allah ya shayar daku ruwan alkausara, Sultana ta amsa da amin tana fadin

“An fa fara maganar tsaida aurena,wlh ana maganar sai da naji zuciyata ta buga”

“Kai Anty Sulty waya gaya miki?”

“Nima ba gaya min akayi ba,dazu ne zan shiga dakin Mom naji suna magana da Hajiyar su Khalil, akan cewa za a tsaida lokacin bikin”

“To shi da baya kasar ma?” Aziza ta faɗa tana ninke musu anko din, Sultana ta ce

“To nima dai naji Mom na cewa a bari sai Yaya ya dawo, kin san fa sun kusan dawowa gida gabaɗaya, shima Khalil din ya kusan dawowa, wai ko kuma a tsaida ranar sai ya kasance lokacin da zasu dawo kar bikin ya wuce saura wata biyu, na dai ji Mom na cewa wata takwas ko wata tara,kafin nan sun dawo dukkansu kuma sun huta” Aziza ta gya ɗa kai tana fadin

“Allah ya tabbatar mana da alkairi”

“Amin ya Allah, da bikina fa ke ce zaki yi min babbar ƙawa wlh” Aziza na shirin magana wayar Sultana ya dauki ruri tana dubawa ta ga Khalil ɗinta, da sauri ta miƙe tana fadin

“My love ya yi kira sai anjima” tana fadi ta fice da gudu, Aziza kuwa ware idanunta tayi tana jinginuwa da bango sabon hawaye na sake zubo mata, komai yana shirin kwab’e mata, kawai mafita shine zatayi addua Allah ya zaba mata abunda yafi mata alkairi,bata so sam Nawaz ya dawo ya sameta a gidan, dan haka taja akwati ta haɗa kayanta tun daga yau, anko din kuma dakin guga ta yi dasu idan aka goge sai ta miƙawa Sultana nata.

????????????????????

Yau ce ta kama ranar da zasu tafi zaria, gaban Aziza    ke dukan uku-uku tun farkawarta bata da kuzari,ganin haka yasa Mom cewa Aziza meke damunki ne?

“Ba komai Mom”

“A’a Aziza karya ba halinki bane, karki fara meke damunki?” a sanyaye ta ce

“Kaina ke ciwo Mom” 

“Subhanallahi! Idan ba zaki iya tafiyar ba ki bar shi ki huta abunki ita mai biki sai ta tafi” nan Sultana ta yi tsalle ta dira da cewa wlh Aziza bata isa ba,kawai dai son mutane ne da bata yi, Mom ta ce

“A’a Sultana baki zo da gaskiya ba, yarinya tace miki bata da lafiya kice bata isa ba,kinga wuce ki tafi kawai Allah ya kiyaye hanya” Sultana tace ita kuwa idan har Aziza ba zata je ba itama ta fasa, Aziza ta ce

“To ba kin riga da kin gaya mata yau kina hanya ba?”

“Sai na ce mata na fasa????, kuma ai ba ina hanya nace mata ba muna hanya nace mata”

Aziza ta yi murmushi ta ce

“A’a ba za ayi haka ba Antyna ta kaina tashi mu tafi” Mom ta ce

“Ki biyewa Sultana ki kashe kanki”

“A’a mom ai nasha magani, ciwon kan zai sakeni” 

“To Allah ya kiyaye hanya, a gaida su Hajiya Habiba, ai da ace zaku biya ta kano da na baku sako wa su Hajiya Lawiza” haɗe rai Sultana ta yi ta ce

“Gaskiya Mom ba zamu kano ba, daga zaria sai kaduna In sha Allahu” ganin yadda Sultana ta haɗe rai yasa Mom dariya ta ce

“To shikenan Allah ya kare” ta faɗa tana rakosu har jikin mota, ta ce

“Ina dai ba zaku wuce kwana biyun ba ko?”

“In sha Allah Mom ba zamu wuce ba,ai ba zamu je mu zauna mu barki ke ɗaya ba” daga haka driver ya jasu ,Mom tana ɗaga musu hannu.

         Kasancewar tsakanin kaduna da zaria ba nisa nan da nan suka isa aka hau shagali dasu, haka sauran ƙawayen amarya Sulaiha suka ja Aziza a jiki, amma matsalarsu daya da ita shine rufe fuskar da take yi, sai da Sultana tace musu ai ko a gida ma haka take wuni fuska a rufe kasancewar tana da matsalar ido, daga haka suka fara yi mata fatan sauki, sai yaba kyawunta sukeyi da dogon gashinta,ita dai Aziza nata murmushi da godiya, dan duk tunaninta ya raja’a a ta hanyar da zata bi ta gudu, dan suna isowa zaria bata yi kasa a guiwa ba ta duba amma bata ga Azima ba, yanzu garin da take hari taje shine garin da Mom tace zata aiki Sultana idan har zasu je, wato KANO.

       Ranar da suka zo anyi party da washe gari asabar aka ɗaura aure, bayan an daura aure da daddare akwai dinner daga wajan dinner za a wuce da amarya gidan mijinta da washe gari kuma sai su koma kaduna, a daren yau idan suka je dinner shine Aziza tasa a ranta zata gudu.

@@@@@

         Sun sha makeup dinsu, suka cakare cikin net dinsu kalar sky blue sunyi kyau sosai,ita dai Aziza taƙi yarda ayi mata makeup har amarya Sulaiha take fadi cikin wasa ai ita da kyau ɗinta ba sai an mata kwalliya ba tunda bata so a barta.

       Suna can babban hotel din da aka kama ana ci gaba da gudanar da abunda ya tara jama’a, Khalil ya kira Sultana a waya kasancewar bata ji a ciki yasa ta fito waje tana wayar.

      Wasu maza ne su uku a wajan gate din hotel din suna cikin mota sai aikin busa hayaki suke yi, wani ne ya daga ido daga cikinsu ya sauke a kan Sultana dake waya, sai da ya kara goge idanunsa kafin ya ce

“Kaii Ɗan Gidan Alhaji? Wa nake gani a can kamar kanwar Doctor Nawaz?” wanda aka kira da sunan Ɗan Gidan Alhaji ya dago yana ƙarewa Sultana kallo ya ce

“Jar Uba! Ita ce wallahi! To me ya kawota zaria?” ɗayan ya ce

“Ko ma me ya kawota, lokaci ya yi da zamu rama abunda Yayanta ya mana a kanta” Dan Gidan Alhaji ya ce

“To yanzu ya kuke ganin zamuyi?” dayan ya ce

“Ah mu kwamusheta kawai,muje mu huta da ita, ya ɗanɗani abunda mukaji sadda yasa aka kullemu a kan wasu banzan talakawa!”

“Lallai Shaho ka kawo shawara, kuma dabadin Baban Ɗan Alhaji ba wlh da mun ƙare rayuwarmu a kurkuku” Dan Gidan Alhaji ya ce

“Yanzu ku daina wannan maganar tunda ba mutane yanzu a kusa ku fita ku dauko mana ita” sai da suka leka suka leka kafin suka fito daukar Sultana wanda hankalinta ya yi nisa sosai a wayar da take yi da Khalil.

       Aziza na zaune cikin kawaye da ta waiga ido bata ga Sultana ba ta tashi a hankali tana fadin

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button