AZIZA DA AZIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

AZIZA DA AZIMA 41-50

“Ki yafeni Anty Sultana zan tafi, ba zai yu ba rayu daku ba danni ba mutum bace,zanje neman yar uwata dan mu koma duniyarmu!” 

     Da wannan tunani zuciyarta babu dadi kamar karta tafi dan an saba, ta fito saɗaf-saɗaf.

     Fitowar Aziza ya yi dai-dai da lokacin da su Shaho suka roɗa ma Sultana katako a bayan kai a kan idon Aziza,ihu Aziza ta saka tana fadin

“Antyyyy Sultanaaaa!!!” ganin haka yasa Ɗan Gidan Alhaji Faɗin su haɗa da Aziza su kwamuso.

       ????????????????????

MOMYN AHLAN✍????

[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????

    ????✨ *AZIMA DA AZIZA*????✨

    (???? _Macizai ne_????)

    MALLAKAR.

*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din

0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.

Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*MARUBUCIYAR.*

1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._

2- _GUDU A JEJI._

3- _SHUHADA._

4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._

5- _WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200)._

6- _COLONEL UBAIDULLAH._

7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._

8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._

9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._

10- _DA NA SANI NA._

  11- _BADAWIYYAH_

12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_

Now

13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)_

_Follow me on wattpad,@Fateemah’0_

   ????????????????????

 _GOOD MORNING????_  ☕☕????????

*PAID.*

????️=4️⃣9️⃣↪️5️⃣0️⃣

Dan haka suka bugawa Aziza katako a kai sau daya,jiri ne ya ɗibeta amma bata suma ba, ta hau kokawa dasu dan ta kwace Sultana daga hannunsa, Shaho yasa katako ya dinga sauke mata shi a gefen kai har ta suma kanta ya fashe yana zubar da jini, sannan suka daukesu suka saka a mota.

     Basu zarce ko ina dasu ba sai wani gidan Ɗan Gidan Alhaji da Babansa ya gina masa, suna zuwa su Shaho suka fito dasu Sultana da Aziza wanda suke sume, suka shige dasu, suna shiga dasu suka kwantar dasu a parlour, D’an Gidan Alhaji ya ce a bari su farka, Shaho yace ba sai an jira sun farka ba dan babu lokaci, a yayyafa musu ruwa kawai su farka, ga wannan yarinyar ba mamaki ita ma kanwarsa ce dan naji ta kiran wannan da Anty, wai cakwai kenan gata kirjinta a cike yake,yaran dai za a shana fa” Dan Gidan Alhaji ya yi murmushi yana lashe baki tare da binsu da kallo, Shaho ne ya kawo ruwa cikin bokati ya shekawa su Sultana da Aziza tun daga kansu har kafarsu, a firgice Sultana ta farka ita ce ta fara dawowa hayyacinta tana riƙe bayan wuyarta dake mata tsami, ware idanunta ta yi a kan Ɗan Gidan Alhaji, tayi saurin ja da baya tana girgiza kai,tana juya idonta ta sauke shi a kan Aziza wacce bata riga da ta farka ba, a razane Sultana ta hau jijjiga Aziza tana kuka tana kiran sunanta ganin yadda jini ke b’ulb’ula a kan Aziza, cikin kuka Sultana ta ce

“Wlh idan Yayana ya sani dukkanku babu wanda zai tsira” D’an Gidan Alhaji ya ce

“Kafin nan Ubana ya min biza na bar kasar, kuma ko da zai sani sai mun miki mummunar tab’o,ko nace sai munyi muku mummunar illa!” Ya fada yana sa hannu zai damki Sultana Aziza ta cafki hannunsa gam tana daga kwance dan duk taji abunda yake fadi, cafka bana wasa ba Aziza ta yiwa hannun Ɗan Gidan Alhaji, da mugun mamaki Sultana ke kallon Aziza wacce take kwance idonta rufe ga jini, cikin rawar murya Sultana ta ce

“A….ziii…..zaaa…! dan Allah ku kai min ƙanwata asibiti kar ta mutu, baku da imani!! Ku azzalumai ne!!” Shaho ya yi kan Sultana yana zuwa zai kai mata mari Aziza tasa kafa ta tokaresa sai da ya yi sama kafin ya bugu da bango ya faɗi kasa, da sauri Dan Gidan Alhaji ya ce

“Kai wannan yarinyar fa na ga alama tana ji da kanta, ga shi ta riƙe min hannuna kamar zata b’alla, ke dan uwarki da Ubanki! Sakar min hannuna” ya fada yana jan hannunsa da karfi amma Aziza ta ƙi sakewa, Sultana kuwa tana takure a jikin Aziza tana kokarin yadda zata tsaida jinin da ke fita akan Azizan.

      “Shaho, yarinyar nan fa taƙi sakina!!” Shaho wanda ya sha ƙasa ya miƙe a fusace yana fadin

“Wannan yarinyar sai fa mun nuna mata cewa ni cikakken dan iska ne, ban taba kisan kai ba, amma inaji zan fara a kanta, dan naga tana fama da tashen balaga, ko dazu bugu ɗaya nayi wa dayar ta suma amma ita sai da na mata biyar! dan haka ba zata sakeka ta dadi ba,bari ka gani” Shaho ya faɗa yana jan wani karfe a bayan windown labule, ganin haka yasa Sultana fasa ihu dan ta ga gadan-gadan ya nufi Aziza dake kwance, a haukace Sultana ta hau faɗin

“Dan Allah Aziza ki sakesa, ba danni ba Dan Girman Allah, kinga munyi sallama da Mom lafiya-lafiya kar a koma mata da gawawwakinmu, dan Allah Aziza ki sakesa! Ki sakesa nace!!” Sultana ta faɗa da karfi a tsawance, sake masa hannu Aziza ta yi, tana sakinsa ji ya yi tamƙar kashin hannunsa ta tsatstsage,a hankali tasa hannu a tsakiyar gashin kanta ta dafe,da kyar ta miƙe zaune sabida jirin dake dibarta dan ta bugu sosai a kai,inda yake saurin musu illa kenan shine duka a kai, amma duk sauran jiki dan sun bugu aikin banza ne.

     Kanta a duƙe tana riƙe da kai da hannunta daya, dayan hannun ta yi musu nuni da yatsarta manuniya cike da gargaɗi ta ce

“Duk wanda baya so Uwarsa! ta haifi wani, to kar ya kuskura ya sake ya taba mini Antyna, ku maidamu inda kuka dauko mu!” dariya Shaho da ɗan Gidan Alhaji da ɗayan suka yi, ƊAN GIDAN ALHAJI ya ce

“Zamu maidaku bayan mun yaga muku rigar mutunci! Ke kuma mai bamu umarni kar mu tabata, Yayanta ne yasa aka kullemu watanmu biyar a kurkuku da kyar mahaifina ya fiddomu, dabadin shi ba ma da har yanzu bamu fito ba, ai kema bamu san kanwarsa ba ce! Mun daɗe muna neman hanyar fansa! Sai ga shi ta kawo kanta har zaria, abun ya bada kala fa, dan haka ke ki fara zuba ido ki ga yadda zamu mata kafin a gama da ita a zo kanki, Shaho ku banƙaremin ita!” kukan tashin hankali Sultana ta saka tana kokarin kama Aziza su Shaho suka fizgota suka bajeta a kan carpet ɗaya ya riƙe mata hannaye ɗaya ya riƙe mata kafafu, kuka Sultana take yi tana ambatar sunan Allah da Yayanta da Mom da Aziza da Khalil, Aziza sai yunkurin tashi take yi ta kasa, ganin Ɗan Gidan Alhaji ya fara sa hannu yana tattaro doguwar rigar dake jikin Sultana yana yin sama da shi rintse ido Sultana ta yi, ta sadaƙar kawai,ganin haka yasa Aziza ware gashin kanta tasa hannu ta b’alli daya tasa a bakin, wani gurnani ta saki tare da hucin Maciji????, jin hucin maciji yasa Sultana buɗe ido da sauri dan tasan irin wa innan abubuwan tunda tana yawan kallonsu, saurin juyowa suma Ɗan Gidan Alhaji da muƙarrabansa sukayi suna kallon Aziza wacce take tsaye gashi ya rufe mata fuska, kwashe gashin ta yi ta tattare ta maida shi baya ta ƙulle,bata da wani mafita wanda ya wuce haka, idan har ta bari tana kallo aka yiwa Sultana fyaɗe ba zata yafewa kanta ba, dole Sultana tasan asalin wacece ita a yau, tana tsaye jini na kan wanke mata fuska, dama idonta a rufe yake,hannu tasa ta shafe kanta nan take aka nemi ciwo aka rasa, bama iyakar Ɗan gidan Alhaji da mutanensa ba, harta Sultana ware ido ta yi kamar zasu faɗo kasa yayinda zuciyarta ya yi wani mugun tsinkewa, Shaho ne ya yi karfin halin faɗin

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button