BA CIKI BANE

*Taku har kullum Momyn Musaddiq*????✍????????????????????????????????????
???????????? *BA CIKI NA BANE!*????????????
????????????????????????????????
*STORY WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*????✍????
*DEDICATED TO MY FANS*❤❣
*KUYI HAKURI DA JINA SHIRU DA KUKAYI NAYI TYPING NE YA GOGE TO SAI DA NA SAKE SABO INA FATAN BAN B’ATA MUKU BA*????????????????????❤????
*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳ
ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*Page 6~10*
Tashi yayi cikin sanyin jiki ya d’auki key d’in motar Sa ya fita duk da yasan akan maganar Rahma ne.
Cikin ‘yan minti na ya k’arasa gidan su zaune ya sameta a babban parlour’n ta Wanda ya had’u sosai dan fad’a muku yanda parlour’n yake 6ata lokaci ne.
Sallama yayi yashigo ya zauna a k’asan Carpet sannan ya gaishe ta.
A hankali ta amsa mishi d’an kukan zuci take saboda bata ta6a tsammanin Nawaf zai aikata wannan mummunar aikin ba ashe shiyasa ya nace sai ya aure ta……katse ta yayi da cewa
“Umma gani kin kira ni a gaggauce.”
Kallon shi tayi sannan tace
“Nawaf daman haka halin Ka yake?
Ban ta6a tsammanin zan haifi d’an da zai 6ata mana zuri’a ba” Sai kuma tayi shiru.
Kallon ta yayi cikin girmamawa sannan yace
“Umma kiyi hak’uri na yanke hukunci ban nemi izinin ki ba, amman wallahi bazan iya zama da Rahma ba Umma ciki”……
Katse shi Tayi da cewa
” Nasan komai Nawaf yanzu mahaifiyar ta ta kira ni ta fad’a mun har abinda Ka aikata kafin auren Ku Nawaf ban ta6a tsammani Kaine zaka aikata wannan abin ba, ashe zan haifi d’an da zai 6ata mana zuri’a?
Nawaf ka cuce mu ka aikata laifin da bazan ta6a yafe maka ba” sai kuma tayi shiru amman hawaye yana bin fuskan ta.
Da sauri ya d’aga kai ya kalli mahaifiyar tashi sannan yace
“Umma wanne abu kuma muka aikata kafin Aure?” Ya tambaye ta cikin rashin fahimtar maganar ta.
“Kai Nawaf kar kamaidani yarinya wacce batasan me nakeyi ba!
yanzu nan mahaifiyar Rahma ta kirani tana fad’a mun akan kai kayiwa Rahma ciki tunkan kuyi aure suka rufa maka asiri shine yanzu zaka sake ta ko?
To kayi maza Ka tashi kaje Ka d’auke ta a gidan su yau d’in nan ta kwana a gidan ka mutumin banza kawai.” Ta k’arasa maganar tana huce.
A razane Nawaf ya d’aga kai yana kuka yace
“Umma wallahi *BA CIKI NA BANE!* bansan da cikin ba wallahi Umma tunda muka had’u da Rahma ban ta6a rik’e ko hannun ta ba, Umma wallahi ban ta6a aikata sa6on Ubangiji ba bare kuma zina!
Umma ki yarda da ni kar kisani na dawo da Rahma cikin gida na..”…
Katse shi tayi da cewa
” kai Nawaf Umarni nake baka ba shawara ba ai komai Ka fad’a mun bazan yarda da shiba saboda haka kayi hanzarin dawo da ‘yar mutane tun kan rai na ya 6aci kuma mahaifinka ya dawo yaji mummunar aikin da Ka aikata, ai shiyasa kaki auren Safna dan kasan akwai abinda Ka aikata.”
Kuka ya fashe sannan yace
“Umma ki yarda da ni wallahi *BA CIKI NA BANE!* bansan ya akayi aka samu wannan cikin ba, Umma nasan ke da kanki zaki shedeni akan bazan iya aikata zina ba”… Sai kuma kuka ya kubce mishi.
Hajiya Fatima tashi tayi tabar parlour’n dan bazata iya jin kukan d’anta wanda take ji dashi duk cikin ‘ya ‘yan ta ba.
Nawaf ganin Umma ta bar parlour’n ne yasa shi rushewa da wani sabon kukan.
“Bro kayi hak’uri Ka daina kuka dan kuwa nasan bazaka aikata abinda akace kayi ba” k’anwar shi ce Hindu wacce duk abinda sukayi da Umma a kunnen ta akayi shi.
Kallon ta yayi da jajayen idanun sa sannan yace
“Kece baki yarda ba amman Umma ta yarda ta amince akan nine nayiwa Rahma ciki.”
K’arasowa tayi kusa da shi ta zauna sannan ta d’aura hannun ta kan kafad’ar shi sannan tace
“Hak’uri zakayi Bro kayi amfani da umarnin da Umma ta baka Ka yarda Ka dawo da Rahma gidan Ka.”
Wani irin kallo ya mata sannan yace
“Kema kina nufin na karbi cikin da ba nawa ba?”
“A’a ba haka nake nufi ba, ina nufin kabi Umarnin Umma Ka dawo da Rahma gidan ka ba shine kad’ai burin su ba to sun samu Ka dawo da ita kar kayi mata komai koda zagi kar kayi mata daga nan mu kuma zamuyi abinda muke so.” Gani nayi ta matso kusa da shi tana fad’a mishi magana a kunnen shi, ai kuwa mai kuka ne naga ya koma murmushi sannan yace
“Gaskiya K’anwata kinada basira to yanzu d’auko Mayafinki muje biko.”
Murmushi itama tayi sannan tace
“Yauwa ko da kaifa Bro” ta tashi ta saka mayafinta suka kama hanyan gidan su Rahma.
Zaune take a d’akin ta tayi tagumi tana tunanin yanzu idan Dad d’in ta ya dawo ya tambaye ta cikin waye ya zatayi…katse mata da tunanin ta akayi da cewa
“Aunty Rahma yaushe kika zo?”
Murmushi ta sake mata ganin k’anwar ta Hanifa sannan tace
“D’azu nazo Hanifa lokacin kuna school.”
Kallon ga tayi sannan tace
“Kai Aunty Rahma yake kika fara fita da wuri ?
Kigafa Aunty Mansura ita har yanzu bata fito ba.”
Wani mugun kallo Rahma ta watsa mata sannna tace
“Ke dallah ki fita kibarni bana son surutun banza.”
Ba musu ta fita ta bar mata d’akin.
Hajiya Saratu ce ta shigo ta zauna a bakin bed kusa da Rahma sannan tace
“Ke wai tunanin me kikeyi ne naji tun d’azu shiru kin shiga d’aki kin zauna?”
Ajiyar zuci Tayi sannan tace
“Momy wallahi tsoro nake Dad ya tambaye ni cikin waye ban san me zance ba.”
Kallon ta tayi sannan tayi tsaki tace
“Ke wallahi kin cika yiwa kanki mummunar fata!
Bari kiji dole Hajiya Fatima ta turo Nawaf yazo k’odan gudun 6ata musu zuri’a, idan ma basuzo ba to gobe sai Boka yayi mana aiki akan su, shi kuwa mahaifin ki daman ai sai abinda muka ce mishi ki kwantar da hankalin ki.”
Murmushi tayi tace
“Yauwa Momyna sai yanzu naji dad’i wallahi.”
Hanifa ce ta shigo tace
“Aunty Rahma Ya Nawaf yazo yana parlour” tana gama fad’an haka ta wuce kitchen dan kawo musu drinks.
Wani dad’i ne ya lullu6e Rahma sannan tace
“Momy kinji wai yazo.”
“Eh to ki nitsu kar kiji mishi da wannan rawan kan naki.”
Amsa mata tayi da
“To Momy naji.”
“Yauwa bari ni nazo mu gaisa da shi.” Tana gama fad’an haka ta fita zuwa parlour.
Tana fita Rahma tahau gyara fuska da sauri sannan ta chanza kaya.
Hajiya Saratu a parlour ta sami su Nawaf suna shan ruwa Hanifa ta sasu a gaba sai faman surutu take musu da yake ita ba ruwanta kowa nata ne.
Sallamar Hajiya ne yasa su yin shiru amsa mata sukayi ta k’araso ta zauna.
Har k’asa suka durkusa suka gaida ita, amsa musu Tayi cikin sakin fuska sannan Nawaf yace
“Hajiya ayi hak’uri da abinda ya shiga tsakanin mu da Rahma sharrin shed’an ne amman insha Allah bazai sake faruwa ba.”
Murmushi tayi tace
“Ba komai ai nasan komai ya faru bazai wuce laifin Rahma ba” a zuciyar ta kuwa cewa take zakaci ubanka ne dan iska ai bazaka maida mu mahaukata ba.
Rahma ce ta shigo ganin haka ne yasa Hajiya tashi tabar parlour’n.
Tana shigowa Nawaf ya had’a fuska yace
“To sai ku tashi mu tafi ko?”
Turo baki tayi sannan tace
“Kamar ya mu tafi ko Sorry bazaka ce mun ba.”
Wani kallo ya watsa mata sannan yace
“Naji ki tashi mu tafi kinga dare yanayi kar ki6ata mun lokaci.”
Haka suka mik’e suka tafi duk abinda suka yi da abinda suka fad’a a kunnen Hajiya Saratu.