Labarai

Yan Sanda Sun Budewa ‘Yan Shi’a Wuta A Garin Zaria Hotuna

DAGA Muhammad Sadis

Yau Juma’a 29/4/2022 Ƴan shi’a mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky sun yi zanga-zanga da suka saba duk Juma’ar karshe a watan Ramadan, sun yi wannan zanga-zangar ne a garin Zaria da sauran garuruwa na sassa daban-daban na kasar nan.

A garin Zaria dai Ƴan shi’ar sun fito kwan su da kwarkwatan su Inda suka fito mazansu da matan su manya da yara domin nuna wa duniya irin damuwan su akan kisan da Isra’ila takeyi wa Al’ummar Falastine tare da kwace masallaci da uku a daraja wato masallacin
Kudus

Related Articles

  • Sau 12 Ina Mafarkin Na Auri Nafisa Abdullahi, Kuma Ko Tsirara Take Yawo Zan So Na Aure Ta ~ Inji Matashi Abubakar Sadeeq

    5 hours ago

  • Yanzu-Yanzu: Tinubu ya karbi fom din takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC

    16 hours ago

  •  Yadda Aka Sace Dala 50,000 A Hedikwatar APC A Abuja

    2 days ago

Ƴan Shi’ar dai sun dauko Muzahharar tasu ne tun daga masallacin juma’a na kwata dake kasuwan sabon gari Zaria, suna tafiya suna faɗin Free Palastinu, hannayen su dauke da tutoci kalar tutar Palastine, tasowar su keda wuya ƴan sanda suka buɗe musu wuta inda suka harbi wasu tare da jikkata wasu da yawa.

Wannan dai zanga-zangar lumanar sun sabayin ta ne duk shekara domin nuna goyon bayan su ga al’ummar Falasɗinawa da Isra’ila ke musu kisa ba dare ba rana tsawon shekaru, Mabiya mazhabar shi’ar dai suna kiran wannan zanga-zangar ne da Muzahharar Qudus.

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button