WATA TAFIYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA TAFIYAR 2

 ????WATA TAFIYAR????       Story & Written

                By

         Jiddarh Umar

????????????????????????????????

*????✨MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION????✨*

https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

 *“`We are the moonlight writers we shine all over the world.“????`* ✍️✍️

بِسم الله الرحمن الرحيم

~~~~~~~????????~~~~~~~

PAID BOOK

                  Free Page    

               02

Ga mai buƙata zai turo 200 ɗari biyu ta wannan Asusun 2284905309,Hauwa Umar Zenith Bank, 

Sai ki turo shaidar biya ta 08141644865.

Ko Katin Waya.

  Nasiha sosai ya yi masu,wanda sai da ya tabbatar da jikin su ya yi sanyi sannan ya ma Nanne sallama ya fita. 

Share guntun hawayen ta ta yi “Nanne ni zan koma, sai zuwa anjima”

“To Fettel Allah ya ƙara kare ki”

“Amin Nanne”shiyan su ta koma,cikin natsuwa ta kammala karyawa,ta dauraye kopin,sallama ta yi dakin Inna Saude wacce har zuwa lokacin suna zaune suna hira da Baba dukda sun gama karyawa, yara kuma duk sun tafi makaranta. 

” Inna ga kofin”

“To ajiye nan Asma’u”

Kasancewar ta ga takalmin Baba a ƙofar yasa ta ce “sannu Baba” Banza ya yi da ita kamar bai jita ba, 

Ƙara mai matawa ta yi “sannu Baba”

Cikin hasala ya taso mata “haba mana ke wacce irin yarinya ce,kin ce sannu ya kyale ki,kin kuma cewa, to ba sai ki rabu da ni ba, aikin banza kawai, 

Dukar da kai ta yi bata ce komai ba,dan indai wannan ne ta rega ta saba gani daga wurin Baba Ɗan Nanne,tashi ta yi ta koma daki tana tunanin me ta tsare mashi haka cikin waɗannan watanni gaba ɗaya ya sauya,dama ba wani dasawa suke sosai da shi ba,amma kuma abin be kai  haka ba. 

tana ganin ta wuce,ta dawo da kallon ta kan shi, 

“Hana Ɗan Nanne, me yasa kake ma yarinyar nan haka ne,bayan ta kasance amana ce a wurin ka”

“Da yaushe ta zama amana a wuri na,to ban dai sanan ko a wurin ki take amana ba,? 

“kar ka manta Asma’u ƴa ce a gareka ko ka ki,ko kaso,domin ɗiyar ƙanwar ka ce,uwa daya uba daya, dan haka dole a kira ta da taka, ni sam wallahi ba na jin daɗin irin yanda kake da yarinyar nan,dan Allah ka dunga sassauta mata”

Turbune fuska ya yi “ina fatan dai kinsan da cewa Uwarta ba mutuwa ta yi ba,kinsan duk abin da ya faru,haka kawai muna fama da kan mu zata kawo mana jin jira ta tsallake ta yi tafiyar ta,yau  kusan shekara nawa ke nan,shekara ishirin da biyu,dan ba zan taɓa mantawa ba,menene dalilin ta nayin haka,shi ne har zaki ce na rinka tausayin ta, ina tsinannun dangin Uban ta,tunda abin ga ya faru kin ga kafar wani acikin su, dan haka ki kamamin bakin ki,nasan abin da nake kuma baƙi isa  ki sa na canza daga yanda nake ba”yana kaiwa nan ya tashi fuww ya bar mata ɗakin, shiyar Nanne ya nufa domin zuwa ya gaishe ta, dan bai samu shiga da suka dawo masallaci ba. 

Da “Allah ya kyauta” Kawai ta bi shi, dan ita kan har ƙasan zuciyar ta,Asma’u kamar ƴar take a wurin ta,kuma tana son yarinyar sosai kamar yan da take son Uwar ta,dan sun yi abotar arziki sosai da ita, shi yasa a koda yaushe take matukar tausayin yarinyar a duk lokacin da ta kalle ta,gaskiya Asma’u ba ta yi dacen aure za tace ba,ko kuwa yama zata saka abun oho, tun da miji na bala’in son ta,kai wannan abin sai dai muce Allah ya mana maganin shi. 

Ganin ta gaji da zaman ne yasa kawai hijabin ta ta fita,lekawa ta yi ta ce ma Inna ta leka gidan su Asiya, a dawo lafiya ta mata, 

  Da sallama ta shiga gidan, Maman Asiya ce ta amsa mata dan haka gaishe ta ta yi “Mama Asiya na ciki kuwa”

“Ban sani ba amma bari in duba”daki ta shiga, zaune ta tadda wata ƴar budurwa wacce za ta zo tsara da Asma’u, tana ganin shi gowar Maman ta, da sauri ta rike mata hannu” Mama dan Allah ki taimake ni,ki rufa min Asiri,ba zan ina ko da zama kusa da Asma’u ba, dan wallahi tsoron ta nake ji, kar tazo  muna hira ta shaƙe ni,kan a kawo min dauki na mutu”

Saura kaɗan Maman ta ta fashe da dariya, ganin yanda Asiyar ta rike mata hannu gam kamar ta ce dole sai  ta je, gashi sai wani zazzare ido take yi, 

“Amma ai naga ƙawar ki ce,tun da tare kuka tashi,ko ba komai akwai kauna a tsakanin ku”

Da sauri ta katse Maman”a da kenan, amma ba yanzun ba,Mama har kin manta irin zanan da na sha da daddare,daga abin arziki,dan kawai na ce zan amso mata tai mako wurin Kawu na,shi ke nan cikin barci a ka min dukan tsiya sai, na tashi ranar jikina duk a farfashe,ni ce har dasu karin ruwa, 

Kuma Mama kun san ba ni kaɗai suka ma haka ba,duk wanda suka ji ya ce ya san wani mai magani ranar sunan mutum Sorry dan ba karin duka da matsa zai sha a hannun suba, to Mama ina dalili, haka kawai ba su samu damar kashe taba, kai dan kallo su wuce da kai, dan haka ki taimake ni, ki ce mata kawai bana nan ”

 ‘Shi kenan “ko da ta fito a tsaye ta same ta in da ta bar ta, nan take Shai da mata Asiya bata nan ” To, Mama sai anjima, in ta dawo ki gaishe ta”tana gama fadar haka ta juya ta fita,dan tsaf ta ji komai da Asiya ke faɗi,ita kuma har ga Allah bata ganin lefin mutane dan sun guje ta,a ganin ta da gaskiyar su, tun da bamai son wahala a rayuwar shi,balle Aljannun ta su wahalar da shi,kasancewar Asiya irin matan nanne masu buɗaɗɗen murya,sha yasa ta ji  duk abin da suke faɗa.

Tana fitowa ƙofar din,samari ne zazzau ne a ƙofar gidan su,wato kofar digan Ɗan Nanne,wasu daga cikin su wadanda ta girma suna ganin suka shiga gaishe ta,yayin da ita kuma ta gaishe da wadanda suka girmeta a wurin,cikin  wasa daya daga cikin su mai suna Muntari “Anty Asma’u mai zan samu ne,dan wallahi ko ƙari ban yi ba”

Murmushi ta yi tana fito da hannun ta daga cikin Hijabi “zoka amsa” Ta faɗa tana mika mashi Naira ɗarin data kwana da shi.

Amsa yayi yana dariya”to bari in cire Hamsin sai in baki canji”

“Ka barshi kawai” Ta ce tana shi gewa cikin gidan. 

Sauran Samarin dake wurin ne sukai mashi caaa a kai”haba Muntari,baka da tausayi ne,yarinya na fama da kanta amma zaka raba ta da ɗan kuɗin ta, kai baka ɓata ba amma shi ne har da wani amsar mata”

“Kar ku manta Asma’u kamar yaya take a wurina,kuma da kuke cewa haka na tabbatar da kun san halinta,in dai zaku faɗa gaskiya,ko da ace na amsa Hasim din nan ko ban amsa ba zata kyautar da shi ne,dan ita abin ta baya tsole mata ido, ko da kuwa shi kaɗai ya rage mata,kuma ma tabbatar koda ku kuka tambaye ta in tana dashi zata baku, bare ni,”

Duk shiru suka yi dan sun san gaskiya ya faɗa,kai Allah dai ya bata lafiya, da Amin suka  amsa. 

 Tana shiga gida ɗakin ta ta koma,zama kawai ta yi tana, daga nan sai gyangyadi, dan kamar yadda take kwana ba bacci haka ta ke yini bata yi,sai dai gyangyadi, dan bata isa ta kwanta ba,dan tana kwanciya za su hau damun ta,da iyayyaku dale ta tashi,rashin bacci masifa ce,shi yasa idan abun ya ishe ta koda rana zakaji ta kuka tana ihu,”waiyo  ku ƙyale ni barci nake ji”to ranar haka take yi,sai in Baba Mudansir zai zauna yana mata karatu shine farkon zata samu damar bacci.

zuwa ƙarfe uku kuwa sai ga Hafiza ta shigo,,cikin jin daɗi kuwa ta tare ta, 

Zama ta yi kuwa suka fara shan hira, zuwa can ta ce daɗin hira yasa ta mike kafa har yana kusa taɓa bangon dakin,,kallon ta Asma’u ta yi “Hafiza ki yi a hankali kar ki taka waɗancan abubuwan da na kashe” wani uban tsalle ta daka sai gata manne da jikin Asma’u. 

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button