BAKAR INUWA 20

Alhmdllhi kamar yanda su Bappi suka yanke shawara an kai kuɗin auren Raudha Hutawa, dan Bappi ya dakatar da M. Dauda sake zuwa Bingo da yay niyyaryi akan son lallaɓa Asabe ta koma aurensa, yace yay haƙuri suɗan kammala wasu abubuwan. Shima M. Gambo ya bashi shawarar ya zauna su taya Ramadhan campaign anan daga baya sa san dabarar lallaɓa Asaben, sai shima ya gamsu.
An amshi kuɗin auren Raudha harda hakimi, hakama dangin M. Dauda kowa so yake ace da shi akayi. Anba M. Dauda zaɓin tsaida lokaci, babu wani tunani ya yanke watanni huɗu. Duk da ba haka Bappi yaso ba sai baice komaiba sukai fatan ALLAH yasa haka shi yafi alkairi. Dan shima Ramadhan ɗin koda ya tuntuɓesa cayay wata huɗun, dan yafi son maida hankali akan wannan maganar campaign ɗin, ya kuma kawo hujjar idan akai auren yanzu za’aga kamar yayine dan amfani da Raudha wajen campaign. Sai dai abinda Bappi bai sani ba Ramadhan so yake ya zamewa auren, so yake kafin wata huɗun ya samu wani ya aurama Raudha ɗin batare da sanin su Bappi ba.
★★★
A ɓangaren ƴan jam’iyya babu ɓata lokaci aka hau campaign ta kowanne ɓangare bayan an bada damar hakan ga ƴan takara ta kowanne fanni. Duk wani ɗan uwa da abokin arziƙi ya fito domin tallata _ Brr Ramadhan B. Hameed Taura (Young millioner)_ kamar yanda matasa ke kiransa. Ta ko ina posters nashine ke yawo. Matashi na matasa kenan.
Duk wani ƙarfin halin Ramadhan da tunanin zai iya sai abin ya koma bashi tsoro, lallai siyasa ba wasa bace ba. Ƙoƙari yake yaga ya hana duk wani ɗora matasa akan ta’addaci na basu ƙwaya da makamai da wasu manya keyi amma hakan ya gagara. Dan su Alhaji Yaro glass sun rigada sun kammala shirinsu tsaf a bayan fage. Hasalima Ramadhan baida maraba da hoto game da kowanne irin tsari nasu. Sai dai duk wani tsari nasu mara kyau sun binne iya su. Mai ƙyawunne kawai suka fiddo garesa. Hakan yasa yake cigaba da musu kallon mutanen kirki.
Tabbas an kaɗa gangar siyasa. Mutanen ƙasa kuma sun amsa. sannan Alhmdllhi ta ko ina Ramadhan ya samu karɓuwa musamman a wajen matasa ƴan uwansa. Dan suna ganin wannan karonfa yaƙin nasune bana kowaba. A gefe kuma ƴan siyasa nata yarfe ga abokan hamayya. Musamman Ramadhan da tako’ina aka sakashi tsakkiya akan bai cancantaba. Ta yaya wanda ko aure baida shi zai iya riƙa ƙasar NAYA. Taya mai ƙarancin shekaru irinsa zai iya riƙa ƙasar NAYA? Taya ɗan gata irinsa zai iya riƙa ƙasar NAYA? Taya… Taya… Tay…. Dayawa suketa faman lissafi.
Sai dai kuma masu iya magana kance zakaran da ALLAH ya nufa da cara ko ana mazuru ana shaho sai yayi. To hakanne kam ga Ramadhan, dan tako ina bakajin sunan kowa sai na Young millioner ga ƙuruciya ga kuɗi ga gayu ga ƙyawu.
A ɓangaren ƴammata suma ba’a barsu abaya ba wajen yaƙin ganin sun ture gwamnatin Raudha sun maye gurbinta. Wasuko gani suke koda ita babu abinda za’a fasa fatansu dai Ramadhan ya amshi tayi kawai. Dukan saƙonsu da shishshiginsu yana hankalce da shi. Sai dai kuma basune agabansaba yanzun. Ita kanta da aka saka masa ranar auren da ita bata gabansa. Dan yakanma manta da wata saranar aure dake a kansa gaba daya. Shi hatta sunan Raudha sai abakin ƴan siyasa ma ya fara jinsa. Kuma bazaice ya riƙeba duk da ana yawan ambata saboda yarfe da ake masa akan batun aure dama auren nata da mutane kan fassarasa a siga kala-kala.
Kallo ɗaya zakai masa ya baka tausai, duk ya rame yayi duhu saboda wahalar campaign da rashin barci. Duk ƙoƙarinsa nason ganin kowa ya fahimcesa hakan bai hana wasu jifansa da kalmar Mai girman kai ba susukance ya cika girman kan tsiya da izza. Duk lokacin da kalmar nan ta fito a bakin wani ɗan siyasa yakanyi murmushi, dan shi dai wannan girman kai nasa da aketa faɗa har yanzu bai ganinsa……….✍