HAUSA NOVEL

BAKIN CIKIN KISHIYATA Complete Hausa Novel

Kukafa sosai jamcy keyi tana tonawa kanta asirin duk abinda ta aikata don gaba daya bata hayyacinta saboda azabar da takesha,

Shikuwa faruk wani irin tsana da kyamar jamcyn yadinga yi,cike da k’unar zuci ya d’aga hannunshi da niyar zabga mata mari saidai kyamkyamin gaba fuskartata yanashi Marin da yai niyya don gurajen harsun fara fashewa suna wani irin wari wasu kuma duk sun duri ruwa gaba daya fuskar bakyan gani,

“Allah ya isa! Tsakanina dake makira, muguwa, azzalima wallahi kin cuceni kin sa nacutar da baiwar Allah da batayimin komaiba, kisani ba zan taba yafe muku cutar da kukayiminba daga ke har muguwar uwarki, kuma kar wannan kazamin Bakin naki ya kara kirana da mijinki don na yanke igiyoyin dake tsakanina dake, NA SAKEKI SAKI UKU, kuma gwandalata baza ta yi kukaba don ayi miki magani insha allahu ahaka zaku kare karshenku bara akan titi,”

sai kuma ya juya gun mahaifiyarshi datai mutuwar tsaye jin abinda jamcyn keta fadin ta yiwa baiwar Allah Fatima,

“Mamy ki kalli irin matar da kika Dage sai na aura, mamy me Fatima ta aikata miki har kikayi hakan agareta? Mamy tunda na auri Fatima baki taba sa manna albarka a aurenmu ba saima balain da kika jefa rayuwarmu aciki, mamy da wanne idon zaki kalli Momyn fatima, wannan shine sakayyar dazakiyi mata na soyayyar data nunawa jininki? Ke kuma kika kyamaci nata jinin? Mamy ke mahaifiyata CE ba zan iya yi miki ko wanne hukunciba Amman ki sani kin cutar dani kin cutar da mata ta don kece silar faruwar komai Amman tun wuri ki nemi yafiyar Fatima tun kafin alhakinta ya kamaki,”

Gurin Momy husna yaje ya d’urk’usa yana Neman yafiyarta akan abinda ya aikatawa yarta d’agoshi tayi tana girgizamai kai don ta kasa magana , juyawa tayi ta fice daga dakin a can harabar asibitin ta Tarar da fatiman ta kifa kanta a bango tana wani irin kuka, janyota tayi ta rungume ajikinta cikecda tausayinta tana bubbuga bayanta alamar rarrashi, hakika wani irin zafi da zugi takeji azuciyarta na cutar da akayiwa ‘ya d’aya tilo da take matukarso da kauna azuciyarta,tabbas da ace ansalwantar mata da ita baza ta taba yafewa ba, kuma awannan karan dole ta dauko matakin Raba wannan Auren don baza ta yarda acigaba da cutar mata da ‘yaba tana kallo, wannan aisai yasa zuciyarta ta buga aiko ita duk hakurinta baza ta iya hakurin da fatiman tayi ba Amman dai komai tazo karshe,

Mijin jiddan ne ya iso wajen yana sanardasu jiddan ta haihu ,gaba daya suka dunguma d’akin da aka maida jiddan don hutawa, aciki suka Tarar da HAJJO idanun nan NATA jajawur alamar taci kuka ta koshhi,rike take da hannun jiddan tana bats hakuri Ganin sun shigone yasa ta maida ban hakurin Kansu,

“Bayin Allah Ku taimaka Ku taimaka tsufana Ku yafemin abinda naiwa yarinyarku, wallahi shartin shaidanne, nasan takurawar danayi matane ya janyo mata hawan jini da har yai sanadiyyar yin jijjigar da tayi,oh ni yasu yauda yarinyar nan ta mutu me zanje incewa ubangiji na, nagodewa Allah data rayu harna nemi yafiyarta kuma Ku yafemin,”

Mamy fiddausin CE race sun yafe mata ba komai don ita ma yanzu Neman yafiyar takeyi

, godiya HAJJO n tayi musu sannan tace wa d’an nata yazo yakaita tasha ta koma k’auye don baza ta kara zama agidanba balle ta takura musu, sallama tayiwa yan dakin suka fice, tace baza ta kara zuwa ba saidai su sunje sukai mata ziyara,

Hakan akayi kuwa saida Bilyamin d’in ya sata a mota ta tafi sannan ya dawo asibitin, nan yazo ya Tatar har an basu sallama suna jiran ya dawo, mamyn CE ta kalle shi tace

,” toyanzu dai saidai mu tafi da Jidda gida saboda bata da lfy zuwa intai 40 sai ta koma,”

Dagowa yayi ya kalleta sannan yace………….!
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️
BAK’IN CIKIN KISHIYATA
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️

Story and written
By
Fatima umar kas
(Mummyn mihal)

*بسم الله الرحمن الرحيم*

®????
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *…*????✍????
[ “`Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women“`]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

*_Z• W• F•????_*
Page 97

“Shikenan mamy ba komai Ku tafi da ita Allah ya bata lfy,”
Da amin ta amsa sannan ta Goya jaririyar suka fito Dan tafiya gida,

Bayan sun dawo nandai aka dinga zuwa yiwa jiddan sannu tare da ganin ‘ya ranar suna ba ai taroba kasancewar mai jegon ba lfy ba a bukatar hayaniya, inda yarinyar taci sunan mahaifiyar Bilyaminu wato HAJJO,
ahaka dai lokaci yaci gaba da tafiya har tsawon sati 2 Amman har zuwa wannan lokacin faruq baisa Fatima a idonshiba tun ranar da suka dawo daga asibiti rabonshi da ita,gashi ko yaran baya gani sosai yake bukatar ganin iyalennashi Amman Abu ya faskara, kullum sai ya gwada kiran number fatiman Amman baya samu, yana matukarson ko muryarta yaji Amman Abu ya gagara, gashi su daddy har yanzu basuce mai komai game da komawarta ba tsoranshi daya kar a rabashi da fatiman don yadda yakeji in akace za a rabasu tamkar rabashi da numfashinshine,
yaudai gurin mamyn ya nufa ko da abinda zata iyayi akan abun, azaune ya Tarar da ita tana sawa jaririyar Jidda kaya ita kuma jiddan ta shiga wanna, guri ya samu ya zauna ya gaida mamyn, bayan ta amsa sannan ya fara fad’in.

“Mamy ya dace kiyi wani Abu akan komawar Fatima dakinta wallahi mamy ina azabtuwa da rashin ganinta kojin muryarta, mamy inason na nemi yafiyarta Amman har yanzu ban sami kebewa da ita a, ina matukar jin nauyin momy ba zan iya zuwa sashintaba ayanzu,Amman ke ya dace ki gyara abin nan mamy tunda ke kika lalatashi Dan Allah kiyi wani Abu akai,”

Ajiyar zuciya ta sauke mai k’arfi sannan tace,

“Wallahi duk yadda kakejin nauyin zuwa sashen husna baka kainiba, kasani husna Nada hakuri sosai tun Tini nasan da hakan Amman tunda kaga tayi shiru da al amarin tabbas bango aka kaita, hakika har gobe ina matukar Dana sanin abinda na aikata, nayi iyakar kokarina nason gano dalilin dayasa na d’aurawa husna tsana hartazo ta shafi fatima, Amman na rasa kwakwkwaran dalili sai wani dalili nawa Mara tushe, kuma tabbas shaid’anne yai galaba a kaina da kuma Sharrin zuciya su suka dinga ingizani har na aikata abinda nayi, Amman ina mai baka hakuri akan tilasta ka danayi akan abinda bakaso don ina matsayin mahaifiyarka, ayanzu babu abinda zan iyayi saidai kaje kaci gaba da addua, nima zan tayaka in da rabon zaku k’ara zaman aure to Allah ya tabbatar inkuma zaman ya kare to saimuyi fatan ubangiji yabaka wata,”

“A a mamy nikam ba zan iya rabuwa da Fatima ba insha allahu nine mijinta har a aljannah, Nina yarda da kaddara nasan kaddararmuce tazo ahaka Amman Nina jima da yafe miki ubangiji ya yafe mana gaba d’aya,”

Jiddan CE ta amsa da amin don duk taji abinda suke tattaunawa itama dai saidai tabi da addu a akan Allah ya daidaitasu don tasan Indai ya yan nata nata ya rasa Fatima tabbas yayi rashin dabazai maida tamkarshiba,

Tashi yayi ya fita cike da damuwa don yanzu baisan Wanda zai tunkara da maganarba daman mamyn yake tinanin zata taimakamai to itama tace saidai ta tayashi da addua,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button