HAUSA NOVEL

BAKIN CIKIN KISHIYATA Complete Hausa Novel

Bayan kwana biyu day in wannan faruk din na zaune a harabar gidan kan wata farar kujera ya zuba tagumi gaba d’aya abin duniya ya isheshi ya rasa yadda zaiyi ya shawo kan wannan al amari, alamar shigowar mota yaji d’agowa yayi nan yai tozali da kayan da motar ta kwaso Indai ba gizo idanshi yake yimai ba Mayan d’akin fatima ya gani ana saukewa anayin bangaren Momy husna dasu, mutuwar tsaye yayi agurin zuciyarshi na bugawa da Sauri da sauri, ya kasa motsawa daga inda yakw har aka gama shiga da kayan ciki,

Da kyar ya iyajan k’afafuwanshi zuwa ciki wani irin sarawa kanshi yakeyi ga wani zazzabi dayaji yana Neman kamashi shikenan ta faru ta ta kare Fatima ta barshi tunda gashinan har an kwaso kayanta,

Bayan sallahr ishai yana nad’e akan gado yana makyarkyata Abdul ya zo yacemai yazo daddy na kiranshi, da kyar ya iya saukowa daga gadon da taimakon kanin nashi ya nufi dakin daddyn nasu, bayan yaje guri ya samu ya zauna ya gaidashi sannan yamai sannu da zuwa, ba yabo ba fallasa daddyn ya amsa sannan ya Dora da fadin,

“Nakiraka ne akan inason ka bani takardar fatima, daman mu muka had a auren to yanzuma mu zamu rabashi saboda bazai yiyu mu zuba ido muna kallon yarinya na cutuwaba, ko da bata taba fadar irin zaman da kukeba duk Wanda ya kalli yadda ta lalace yasan ba a kwanciyar hankali takeba don haka na baka zuwa safiya kakawomin TAKARDAR SAKINTA,”

Bani ya bud’e da niyyar yin magana Amman daddyn ya dakatar dashi da fadin bayason jin komai daga gareshi kawai yayi abinda yace, tashi yayi da niyyar fita daga dakin saidai wani irin duhu ya mamayemai ido,anan jiri ya kwasheshi ya zube agurin ji kake yifffff……………………!

Mrs Bilyamin kaita✍????
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️

BAK’IN CIKIN KISHIYATA

????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️

STORY AND WRITTEN
By
FATIMA UMAR KAS
(Mummyn mihal)

Page 98

Mamy ce ta shigo da sauri jin fad’uwar abu daman ta taho ta kawowa daddyn abinci taji abinda ya ke cewa faruk din, saura kad’an kayan abincin su sub’uce daga hannunta saboda rudewa na ganin halinda d’an nata yake ciki, da sauri ta ajiye kayan abincin ta nufi gurin faruk din, jijjigashi takeyi iya k’arfinta Amman ko motsi,kallanta ta maida kan daddyn data ga shiko ajikinshi abincinshima yakeci, cike da takaici tace.

“Haba Alhaji yanzu kana ganin halinda yaron nan ya shiga Amman kai ko ajikinka? bayan kuma kasan kalamankane suka jefashi a wannan halin? Yanzu ko tausayinshi bazakajiba saikace ba d’ankaba?”

Cike da rashin damuwa ya d’ago ya kalleta sannan yace,

“Wannan kuma ke ta shafa donni na Riga na gama magana, ba suma ba ko mutuwa zaiyi indai zai farfad’o sai ya bani takardar ‘yata don ta gama Aurenshi”

Cigaba yayi da cin abincinshi da sauri ta tashi ta fita don taga alamar daddyn ba taimaka mata zaiyiba, ba jimawa suka shigo itada Abdul da Jidda da mai gadi, Abdul d’inne shida mai gadi suka ciccibi faruk din sukai waje, bud’e motar mamy tayi suka Sanya faruk din sannan Abdul ya shiga mazaunin direba ya tada motar suka fice kai tsaye asibiti suka nufa suna zuwa aka karbeshi, likitocine suka rufu akanshi don ceto rayuwarshi, sun dau lokaci mai tsayi akanshi sannan ya dawo hayyacinshi Allurar bacci suka yimai don ya sami Hutu suka jonamai drip sannan suka fito da sauri mamyn ta zo ta sha gaban d’aya daga cikin likitocin da tags shine babbansu, a rikice take tambayarshi ya jikin faruk din, cewa yai su biyoshi office dinshi, dukkansu suka d’unguma d’akin, zama Dr yayi sannan itama ta zauna tana fuskantarshi su kuma su Abdul din tsayawa sukai, gyaran murya Dr yayi sannan ya fara magana ” Gaskiya hajiya rayuwar d’anki na cikin had’ari matuk’ar bazaku magancemai matsalarshiba, abinkicen da mukayi mungano yana cikin matsananciyar damuwa da ta Sanya jininshi yai mugun hawa, ayanzu haka ma zuciyarshi ta kusan bugawa sakamakon wata magana da yaji ita ta sanya zuciyarshi harbawa da karfi, Amman dai yanzu munyi nasarar shawo kan matsalar sai dai dolene Ku bashi abinda yakeso Indai kunason yai lfy,”

“Shikenan Dr mungode insha Allah zamuyi kokarin ganin ya sami abinda yakeso,”
Cewar Abdul ita kuwa mamy inbanda sharar kwallah babu abinda takeyi don tasan itace silar faruwar komai,

Abdul dinne yace su koma gida shi zai zauna agurin faruk din Amman mamyn tace baza ta iya tafiya tabarshi ba, saidai su su tafi shida Jidda, ganin ta dagene yasa suka tafi suka barta agurin faruk din,

A can kuwa tin dare akayowa daddyn waya akan jikin hajiya ya matsa ciwon kafarta ne ya tashi,hankali tashe suka tafi shida Abba Aminun Aunty Fatima ma an mata waya tazo sun Tarar da mahaifiyar tasu najin jiki, asibiti akayi da ita, saidai tun ahanya takeyi musu wasiyya da su rike zumunci su k’ara had’a kansu, kuma tace suyi k’okari su gyara auren yaransu don ko bayan ranta tana Alfahari da aurensu faruq din, ahakadai suka is a asibitin saidai wajen Asuba hajiya Jidda tace ga garinku nan, Allahu akbar daman dukkan mai rai mamacine,saidai muyi fatan in tamu tazo Ubangiji yasa mu cika da imani,
HAJIYA jiddah kam antafi mutuwar da tayi matukar girgiza yaranta don sai sukaji mutuwar mahaifinsu ta dawo musu sabuwa, Aunty Fatima sosai take kuka na rashin mahaifiyar tata, suko su daddy daurewa kawai suke Amman mutuwar ta dakesu, da safe aka basu gawar suka dawo gida amasallaci akabada sanarwar janaizarta don haka ana gama hadata aka mikata gidanta na gaskiya, hakika ta sami kyakykyawar shaida daga Bakin mutane kowa fadar kyawawan halinta yakeyi musamman makwaftanta don lfy take zaune da kowa,mamy husna da Fatima suma sosai sukai kukan rasuwar tata, ahakadai akayi sadakar 3 Amman har lokacin faruk na asibiti, saida yayi kwana 7 a asibiti sannan aka sallamesu don jikin nashi da sauk’i saidai ba warwarewa yayiba,daga asibitin gidan mutuwar suka nufa kasancewar ranar ne sadakar 7 shima faruk sosai yaji mutuwar kakartasu saidai subita da addua, saida ya gama yin gaisuwa a waje sannan ya nufo cikin gidan don yayi gaisuwar,alokacinne kuma Fatima ta rako wasu bak’i zasu tafi, karaf suka had’a ido da shi aikuwa da sauri ta juya da nufin komawa cikin gidan saidai sunanta da taji ya kirawo cikin raunananniyar murya shiya hanata tafiya,k’arasowa yayi ya sha gabanta sannan ya zuba mata ido,itama tad’an rame Amman ba kamarshiba,magana yafarayi a hankali,

“ZAHRA me yasa zaki gujeni a lokacin da nafi kowa bukatarki? Me yasa kika haramtamin ganinki da kuma jin muryarki har tsawon wannan lokacin? Shin kinsan halin da kika jefa zuciyata ta silar k’auracemin da kikayi? Yanzu kin amince su daddy su raba aurenmu bayan kinsan muna son junanmu,? Haba mata ta ki tausayawa mijinki ki cetoshi daga halinda zai shiga sanadiyyar rabashi da abinda yakeso,”

Da sauri ta katseshi idonta na zubarda hawaye,

” a a Abban fuad baka sona don da kana sona bazaka yimin abinda kayimin agidankaba, ka sani na kunshi Bakin ciki agidanka ga Bakin cikinka ga BAK’IN CIKIN KISHIYATA,

Da bakinka Kace baka sona baka kaunata ka tsaneni kuma adole ma kake zaune dani SBD kana tsoron daddy da Tini ka rabu dani, ka mareni ka cemin jaka kacemin dabba sannan ka hanamu abinci ni zakasa nayi girkin Amman sai Wanda kuka rage kake ba yaranka suci,Kace inna mutu ma bai shafekaba,Amman yanzu kazo kanacemin Wai bazaka iya rayuwa babuni ba taya zan yarda dakai, ni yanzu saidai ince Allah ya hada kowa da rabonshi,tana kaiwa nan ta rab’a ta gefenshi tai cikin gida don wani kukanne ya ke shirin kwace mata data tuno irin wahalar da tasha agidanshi………………..!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button