HAUSA NOVEL

BAKIN CIKIN KISHIYATA Complete Hausa Novel

Comment and share pls
????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️

BAK’IN CIKIN KISHIYATA

????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️

STORY AND WRITTEN
By
FATIMA UMAR KAS
(Mummyn mihal)

Page 99

Juyawa yayi a sanyaye da niyyar fita karaf suka had’a ido da kaninshi Abdul, k’arasowa Abdul din yayi sannan ya dafa kafadar ya yan nashi yace,

“Dan Allah yaya ka dena sa damuwa a ranka kaga ba lafiyace da kaiba, ninasan maman Fuad na sonka kuma zata yafe maka kuma nasan baza ta iya rabuwa dakaiba,don da ace zata iya rabuwa dakai da baza ta zauna tasha wahala agidanka ba da tini ta Dade da barinka don haka ka kwantar da hankalinka komai zai wuce………….”

Hakadai ya dinga rarrashinshi da kalamai masu dadi har faruk din yadanji sanyi aranshi sannan suka koma wajen zaman makokin,

***Acan kuwa likitocin gajiya sukayi da jiran tsammanin ganin yan uwansu jamcy don haka suka CE suyi kwatancen inda suke aje afadawa yan uwansu, mahaifiyar tata CE ta bada kwatancen gidanta tace aje asiyar da kayan gidan ayi musu magani, saidai mummunan labarin da yazo kunnensu shine gidan ya kone kurmuss ba a samu ko tsinke agidanba,

Tashin hankali da ba a sa masa rana nanfa hankalin hajiya salamatun ya kara tashi jin cewa komai nata ya k’one bata tsira da komaiba duk kadarorinta na gidan, gashi itama jamcy anje gidanta antarar da wasu aciki, hankalinsu bai kara tashiba said a likitocin suka kira mai kura aka kwashe su jamcy aciki aka fitar dasu daga asibitin don likitocin sunce bazasu ci gaba da kwantar dasu a gadonsu ba, don sun lalata d’akin ko shiguwa bayayi don inbanda wari da zarni ba abinda dakin keyi don yanzu kafafuwan nasu sun rub’e har tsutsotsi suke fitarwa ga fuskar jamcy data zama kamar ta kutare itama kurajen ruwa suke zubarwa, kashi da fitsari duk anan sukeyi kasancewar bamai jinyarsu, anan Bakin titin aka juyesu tabbas duk Wanda yaga yanda suka lalace suka kanjame saiya tausaya musu a lokacin,sosai HAJIYA salamatun ke kuka tana jawa jamcyn Allah ya isa tana fadin.

“Duk ke kikajamin wannan bala’in ina zaman zama na kikazo kika azalzaleni kikasa na manta nabar gas a kunne yanzu gashinan ban tsira da komaiba ubanwa ya hana ki tafi ke kadai saikinzo kin tafi dani?, nikam haihuwarki batayimin rana ba……..”

Itama jamcyn cikin kuka ta katse mahaifiyar tata.

” wallahi ni kika cuta ni ya dac e nai miki Allah ya isa nikam banyi sa ar uwaba,ke kika cuceni kika dorani a hangar zuwa wajen boka nitun farko sanshi nakeyi tsakani da Allah Amman kikazo kika zugani akan na mallakeshi muci dukiya, gashinan yanzu ba mijin ba dukiyar ga wahalar da na jawowa kaina, gashi wadanda na zalinta basu yafemin ba, kaicona ni Jamila nacuci kaina na zalinci kaina mahaifiyata ta kaini ta baro,.”

Sosai suke kukan nadama kowanne yana ganin d’ayane ya cuceshi,(Allah ya kyauta shiyasa akace inzaka Gina Ramin mugunta ginashi daidai tsayinka)

****BAYAN ARBA,IN 40**
Washe garin sadakar arbain din hajiya mijin Jidda yazo tafiya da matarshi don sun Dade dayin arbain kawaidai mutuwar Nance ta dakatar da komawar tata shikuwa adaddafe ya iya kara wadannan kwanakin don sosai yai kewar matarshi da jaririyarsu duk da kullum yana zuwa Amman inyazo kamar kar ya tafi yakeji,don haka da wuri ya iso gidan sakamakon Kiran da daddyn yamai na yazo ya tafi da matarshi, Asafiyarne kuma daddyn ya had’a dukkan iyalen gidan a part dinshi

bayan kowa ya hallarane daddyn yai gyaran murya sannan ya fara magana.

“Nasan dukkanku bakusan dalilin dayasa akayi zaman nanba,to babban dalilindai akan faruk da fatimane, nasan kunsan dalilin da yasa suka kasance agiida tsawon lokaci, hakanta faru sakamakon kaddarar da ta fada musu musamman shi faruk duk da dai shima da laifinshi amman dai ubangiji ya Riga ya rubuta faruwar hakan saidai muyi fatan ya kiyaye gaba, ada na yanke wani hukunci Amman tun bayan rasuwar HAJIYA na janyeshi sakamakon wasiyyarta da nakeson cikawa don haka yanzu kai faruq ga matar kanan Ankara dawo maka da ita a karo na biyu sai ka kiyaye, saidai kun sami canjin gida Uncle dinka ya sai muku wani gidan anan kusa damu saboda baza mu kara yarda kuyi nesa damuba anmayar da kayanta cikin wannan gidan anzuba komai aciki,wancen kuma na kyautar dashi ga BABA LIMAN ya jima da komawama shida iyalenshi don haka kaje kayi harkokinka anjima su momynku zasu raka ita fatiman sabon gidan naku, Allah ya Kore duk wata fitina daga cikin auren, kaima Bilyamin kad’au matarka Ku wuce gida Allah ya raya,
Akwai mai magana acikinku,?

KUNA IYA SIYAN DATA NA MTN CIKIN FARASHI MAI RAHUSA A NIGERIA
1GB = 250 NAIRA
2GB = 480 NAIRA
3GB = 700 NAIRA
4GB = 950 NAIRA
5GB = 1200 NAIRA
10GB = 2400 NAIRA
15GB = 3500 NAIRA

IDAN KUNA BUKATA KUYI MANA MAGANA TA WANNAN NAMBAR 08140419490, TA WATHASSAP KO KU KIRA MU
Ya fad’a yana kallon kowa yanda fuskokin su suka cika da farin ciki, mamy fiddausi ce tace…………………..!
????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀
????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀
????????‍♀????????‍♀????????‍
????????????‍♀
????????‍♀

BAK’IN CIKIN KISHIYATA

????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️

STORY AND WRITTEN
By
FATIMA UMAR KAS
(Mummyn mihal)

Last page
Page ????
????????????????????????

Cikin tsananin farin ciki mamy fiddausi ke fad’in.

” Alhamdulillahi godiya ta tabbata ga Allah hak’ik’a nayi matuk’ar farin ciki da gyaran auren nan da akayi, ubangiji ya Kore duk wata fitina daga cikin auren,”

Kusada Momy husna ta koma ta rike hannunta tace.

“‘Yar uwata ina mai godiya agareki kuma ina kara Neman afuwarki da kiyafemin duk abubuwan da nayi mini abaya.”

Itama Momy husna cike dajin dad’i tace.
“Ba komai yayata Nina yace miki nidaman ban rike ki da komaiba,”

Nagode sosai Yar uwa ta, sai kuma ta maida kallonta kan Fatima tana fad’in,
“Zonan d’iyata ‘Yar albarka zo inji duminki a kusa dani,”
Tasowa fatiman tayi cike da kunya ta zauna kusa da mamyn,itama yafiyarta ta kara nema, nan tace.

“Mamy ni bakiyin komaiba ubangiji ya yace mana gaba daya,” faruk ne shima cikin matuk’ar jin dad’i ya taso ya dawo gaban daddyn ya sunkuyar dakanshi sannan yace. “Hakika daddy da Abba babu abinda zan iya saka muku dashi face addua nagode nagode Allah ubangiji ya jikan HAJIYA ya gafartamata yasa ta huta, ” da amin suka amsa, sannan mijin Aunty Jidda shima godiyar yayi sannan yayi musu sallama ya fita yana jiran jiddan ta fito su wuce, itama kasancewar a shirye take sallama tayi musu ta fito suka tafi, shima daddyn da Abba Aminu tare suka fice suka wuce office tare da faruk din suka fito yai musu rakiya,itama Momy husna da Fatima part d’insu suka wuce don k’ara kintsawa,

Hakance ta kasance da daddare su momyn suka raka Fatima gidan ta ta koma a karo na biyu, bayan sun tafi ta fito ta zazzaga gidan ko da inda zata gyara ganin ba dattin komai ya sanya tazo ta shiga wanka ta yiwa yaranta, shiryasu tayi cikin shiga mai kyau sannan itama ta zauna ta tsara kwalliyar da ta Dade batayi irintaba, ta sanya wata dakakkiyar shaddarta tayi musu anko da yaranta, masha Allah ZAHRA fa ta fito a amaryarta sak kamar bata ajiyesu fuad ba, sosai tayi kyau itada yaranta, zama sukai jiran shi a parlour, aikuwa ba jimawa sukaji alamar shigowar mota da sauri ta tashi ta kama hannunsu suka fice don tarbarshi, suna fitowa shima ya fito daga motar, aikuwa da gudu yaran sukayi gunshi shima bud’e musu hannu yayi suka fad’a jikinshi sunamai oyoyo cike da farin ciki ya riko hannunsu suka nufo gun Fatima da ta ke tsaye tana ta sakin murmushi, itama b’ude mata hannunshi yayi ba musu tazo, hadasu yayi ya rungume kyam ajikinshi kamar za a kwace mai su, ahaka suka nufi ciki,a parlor suka zauna dukkansu, “mijina me zaka fara wanka ko abinci zaka faraci,?” Cewar Fatima kallonta yayi cike da annashuwa yace, “Ranki ya dad’e ko me kika ga ya dace infarayi shi zanyi ai girmankine,”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button