HAUSA NOVEL

BAKIN CIKIN KISHIYATA Complete Hausa Novel

Murmushi ta sakar mai sannan tace bari inhad’a maka ruwan wanka kafijin fad’in jikinka,” tashitai taje ta had’amai ruwan wankan kafin ya fito ta had’a musu abinci, anan kan carpet suka zauna dukkansu tare sukaci abincin suda yaran,bayan sun gama zuwatai tayiwa yaran shinfid’a ta canja musu kaya zuwa na bacci ta kwantar dasu, fitowa tayi gurin mijinta sukaci gaba da fira,

“Har yanzu dai ba zan gaji da Neman afuwarki akan abubuwan da nayi miki abayaba abisa rashin sani,ina k’ara rokonki da ki yafem.,……..”
Da sauri ta katseshi ta hanyar rufemai baki da hannunta,

“Ka dena Neman yafiyata na Riga na yafema kuma daman ko a baya bantaba k’ullatarkaba saboda nasan ba laifinka bane shiyasa ban tabajin araina na tafi na barkaba na zauna ina yimaka addua ba dare ba rana nayi hakuri da duk abinda na gani, don haka saidai ince Allah ya kara mana zaman lfy da kyaunar juna,”

“Allah sarki mata ta Yar aljanna nagode Allah yayi miki albarka,inason jin raayinki akan na Samar miki aiki?
Sannan yau na samarwa yaranmu makaranta anan kusa damu kema inkina raayin yin aikin saina Samar miki,”

Murmushi tayi sannan tace.”nikam banida raayin yin aiki na fison na zauna na kula da mijina da yarana.”

Shima yaji dad’in
maganar ta ta nandai suka raba dare suna firar soyayya, sai can tukunna suka nufi d’aki suka kwanta,

Tin daga nanfa wad’annan maauratan suka fara rayuwar mai tsafta mai cike da soyayya da kaunar juna gami da tattalin juna,

Matar Dr Ahmed ta haihu tare sukaje barka inda faruk din ya nemi yafiyar su akan abinda fatiman tace yayi musu, suma sunce ba komai ya wuce,

Abin farin cikin da ya kara samunsu shine bayyanar cikin Momy husna, itakanta batasan da cikinba said a ya fara motsi, tana zuwa asibiti akace cikine na 5 months sosai sukai farin ciki da cikin kamar shine na fari,

ahakadai taci gaba da renon cikin,
Alokacinne kuma akasha bikin Abdul da ‘Yar gidan aunty Fatima wani zumunci ya kara kulluwa, Momy husna ta sauka inda ta haifi ‘yan uku nanfa mamy fiddausi ta dage sai anbata d’aya ta rike, sun mata alkawarin bata in anyaye yaran, Aunty Jidda ma ta kara haifar namiji akasa sunan daddy,

itama Fatima wani cikinne da ita yanzu,

Ayaune suka shirya zuwa gidan marayu da asibitoci dankai tallafi, gidan marayun suka fara zuwa sannan suka wuce asibitin, Bayan sun shiga sun bada tallafi ga marasa lfy sun fito har sun k’usa fiita daga ciki Fatima taji ankira sunanta, waigawa tayi nantai tozali da wasu almajirai k’udaje sai binsu sukeyi, itadai kamar tasan fuskar Amman ta kasa ganewa,

” Fatima nasan bazaki ganeniba daman Jamilace kishiyarki ada wannan kuma mahaifiyatace, kinga yadda rayuwar ta maidamu sakamakon son zuciyarmu Allah ya rufa mana asiri mun tonawa kanmu,hakika na cutar daku Amman kunga yanda Allah yayi dani ke kuma Dana musgunawa kinga yadda ubangiji ya d’aukakaki, Dan Allah ki yafemin kisa mijinki ya yafemin,”
Hawayene ya zubowa Fatima tabbas d’an Adam ba abakin komai yakeba tabbas ta tausayamusu, cewa tai ta yafemusu sannan ta fito da kud’i mai yawa ta basu tace sasai abinci,shima yad’anji tausayinsu yace ya yafe musu, sannan suka fita suka tafi,

Bayan komawarsu gida jikinta duk yai sanyi inta tuna yadda su jamcy suka koma, faruk ya lura tun dawowarsu batada walwala don haka saida sukazo kwanciya ya dinga rarrashinta da nuna mata ko me ya samu su Jamila su suka jawa kansu kartama sa damuwa aranta kodan abinda yake cikinta, hankalinta ya kwanta da kalmomin mijin nata daga nan suka kwanta,

** Hakadai rayuwar wannan familyn ta cigaba da tafiya cikin farin ciki da kwanciyar hankali inda Fatima taci gaba da renon cikinta sai fatan ubangiji ya sauke ta lfy da dukkan sauran masu ciki.

TAMMAT BIHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH

Godiya ta tabbata
ga Allah da yabani ikon kammala wannan littafin, ina rokon abinda na fada daidai ubangiji yabani ladanshi inda nai kuskure ya yafemin Yakuma sa sak’on danakeson isarwa ya isa ya amfani Al,umma ????????????????????????

Godiya da jinjina gareku masoyana masoyan rubutuna, naji dad’in yadda kuka kasance dani tun daga farko har karshen littafin kuka dinga karfafamin gwiwa da comment mai sharhi harna kammala, ina muku sonso fisabillillahi musamman,????????

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button