HAUSA NOVEL

BAKIN CIKIN KISHIYATA Complete Hausa Novel

Yana gama tura mata ya ajiye wayar don yasan inya biye mata yanzu zata karyamai zuciya da magiya harya hak’ura
yana ajiye wayar bacci ya d’aukeshi a gurin,

Da daddare
Bayan ya dawo daga sallah r magriba ya kirata akan yanason ganinta yanzu yana jiranta a harabar gidan
tana shirin cemai baza ta iyaba d’if ya kashe wayar, ganin ya kashene ya satayin jigum tana Neman mafita,

Wani kiranne ya k’ara shigowa, “inajirankifa,”
Haka kawai yace ya kashe wayar ganin batada mafitane yasa ta zira zumbulelen hijab d’in datai sallah ta fita, d’akin mahaifiyarta ta shiga ” Momy yaya faruoq yana kirana,”
Ta fad’a tana sunkuyar dakai,
Ba tare data kawo ko mai arantaba tace “To kije mana watak’il sak’o zai baki,” ficewa tai ta nufi harabar gidan ,

Tana fitowa ta hangoshi a zaune kan farar kujerar kusada wasu flaws da suka zagaye gidan k’arasa tai tare dayin sallama,
Amsawa yai sannan yace “Bissimillah”
Yana nuna mata kujerar dake fuskantarshi, satar kallonshi tayi sannan ta gyara kujerar ta maidata yanda tashi take sannan ta zauna, gaidashi tayi ya amsa sannan ya d’ora da fad’in,

“Wai wannan kunyar tawa da akeji yaushe aka farata? To ni dai gaskiya bana sonta don zata cutar dani kawai ki ware muci gaba kamar da ki saki jikinki dani Mu dinga fira kamar yan
da mukeyi a way
a,”
Itadai murmushi kawai takeyi tana wasa da zoben hannunta don ita wata irin kunyarshi takeji da nauyinshi, bakintama nauyi yake mata intai niyyar yimai magana,

A hankali yake d’an janta da fira harta fara sakewa tana amsamai, kamar daga sama sukaji tsayuwar motoci

D’agowa sukayi don basuji shigowar motocin ba sai tsayuwarsu, ido Zahra ta zaro Dan ganin su abban tane suka dawo daman abinda take gudu kenan su dawo su gansu tare,
kafin ta ankare harsun fito daga ciki sun nufi ciki,

Ajiyar zuciya ta sauke ganin basu lura dasu ba saidai kafin ta farga saiji tayi faruoq Na fad’in

“Daddy and uncle you are welcome back,”
Kusan atare suka juyo inda sukaji muryar faruk suka gani shida fatima,

tasowa yai yana cigaba da musu barka da dawowa,
Suma cike da farin ciki suke amsawa Na ganin d’an nasu musamman Alhaji Aminu da yakejin faruk d’in kamar d’anshi Na cikinshi,

Kafin k’iftawar ido Zahra ta kwasa da gudu tabi ta k’ofar baya tai cikin gida…….,……………!

Pls comments and share
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️
BAK’IN CIKIN KISHIYATA
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️

Story and written
By
Fatima umar kas
(Mummyn mihal)

*بسم الله الرحمن الرحيم*

®????
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *…*????✍????
[ “`Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women“`]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

*_Z• W• F•????_*
Page 55_60

_______Abangaren Zahra ma cike take da d’okin dawowar ya yan nata domin tayi matuk’ar kewarshi, dukda bata tab’a bari wani ya ganotaba kasancewar tanada zurfin ciki ko wayama a b’oye takeyi dashi ba ta iyayi agaban iyayenta kasancewarta mai tsananin kunya,

Hakance ta kasance ranar da faruoq zai diro k’asar tin safe suke aiki itada Aunty Jidda don basu bari yan aiki sukayiba sunce wannan na musamman ne don itama Jidda sosai takeji da yayannata,

Aikuwa kafin 10:00 sun kammala duk abinda suka shirya yi na tarbar yayan nasu nandanan kwa gida ya gauraye da k’anshin girkin, zamewa Zahra tayi tanufi d’akinta tabar Jidda da shirya kayan akan danning table, tana shiga d’akin ta fad’a bathroom ta sillo wanka bayan ta fito tasa towel ta tsane jikinta sannan ta zauna akan mirrow, mai ta shafa sannan ta shafe jikinta da wasu kalar turaruka masu k’amshi simple make up tayi don ita ba ta b’ata lokacinta wajen kwalliya itadai akwai son k’amshi donduk sanda zaka ganta to cikin k’amshi take,

Sif ta bud’e ta zaro wani had’edden less d’,inta black Wanda akawa ado da duwatsu red Riga da zani akayi mata zanin ya tsuke daga sama kasa kuma ya bude hakanne yabawa sharp dinta damar fitowa rigarma das ta zauna ajikinta kamar ajikinta aka d’inka kayan, kasancewarta fara sai kayan suka haskata, dukda ba kwalliya tayi ba Amman tayi kyau don ita daman mai kyauce gashinta ta tufke da wani Jan ribom tana shirin d’aura d’ankwali momynta ta shigo d’akin tana fad’in

“Zahra Wai me kikeyi a d’akinne tin dazu? Kowafa ya fito ke kawai ake jira kuma kinsan jirginsu 11:00 zai sauka,”

“Na gama Momy ganinan fitowa”
Ta fad’a da muryarta mai sanyi don batada hayaniya ko kad’an,

Fasa d’aura d’ankwalin tayi ta d’auko wani mayafinta red ta yafa a saman kanta
Kasancewar mayafin baida santsi shiyasa ya zauna akannanta ba tare daya zameba,takalmi ta zira shima red sannan ta d’au pos mahad’in takalmin ta fice daga d’akin,

A parking space ta Tarar dasu duk sun fito Dan zuwa taro faruoq d’in,
Momy husna da mamy fiddausi sai Aunty Jidda sai Zahra da Abdul sai kuma sauran k’annensu mota biyu sukayi sannan suka fits daga gidan suka nufi air port ,

basufi minti biyu da zuwaba jirgin ya iso,

Fasinjan cikine suka fara fitowa su kuwa inbanda rarraba ido ba abinda sukeyi sai ka rasa Wanda yafi zumud’in dawowar faruoq d’in,

Can na hango wani santalelen saurayi fari tas dashi yana saukowa daga jirgin kusan shine na k’arshen fitowa sanye yake da English wear’s da sukai matuk’ar amsar jikinshi a hankali yake saukowa daga matattakalar jirgin hannunshi sanye cikin aljihun wandonshi,

Wani dad’ine ya ratsa Zahra na ganin habibin nata,
gaba d’aya ya canja kamar ba shiba, duk da suna vidio call Amman ganinshi azahiri yafi ganin da takemai a waya,

Tun kafin ya gama saukowa suka nufeshi shima da sauri ya k’araso gunsu yana sakin murmushi, rungumesu ya dingayi d’aya bayan d’aya cike da d’okinsu don yayi kewar ahlin nashi sosai,
rarraba ido ya farayi ganin baigantaba bayan tace da ita za azo tarararshi yana shirin tambayar ina take?
Karaf suka had’a ido ta jingina da jikin motar da sukazo,

Da sauri ta sunkuyar da kanta k’asa tana murmushi don taji kunyar yadda ya kamata tana kallonshi, shi kuwa ka sa d’auke idonshi yayi daga kanta don ba k’aramin kyau tayi masaba ga girman da yaga tayi Ashe ganin da yake mata a waya ganin tsoro yake mata,

Mami Firdausi ce ta lura da hankalinshi baya Kansu yanacan wani guri daban a hankali ta maida idonta inda taga yana kallo,

Ido ta zaro k’irjinta na bugawa da sauri da sauri ganin hankalin d’an nata gaba d’aya yana kan Zahra ita kuma ta sunkuyar da kanta tana murmushi,

Faruoq d’in ta girgiza da k’arfi ganin tamai magana Amman baisan ma tana yiba, da sauri ya dawo da hankalin shi kanta yana sauke ajiyar zuciya mai k’arfi, harara ta bankamai Don ba k’aramin haushi ya bataba sannan tace

“Ka wuce mu tafi gida inka gama kallon nata”

Sosa kanshi yayi sannan ya juya yabi bayan ta don duk sun shige mota,
ya so ace mota d’aya suka hau da Zahra saidai ina ita Tini ta shiga motarsu momynta,
shiga d’ayar yayi ya zauna kusa da Abdul dazaiyi driving d’insu sai mamy da yaran abaya don ita Aunty Jidda motarsu Fatima ta hau itacema takejan motar,

Isarsu gida suka baje akan danning table suna kwasar girki sunaci suna zuba santi musamman ma faruoq, ita kuwa Zahra tunda suka zauna ta kasa kai 1 spoon bakinta don duk a takure take na kallon da faruoq din ke mata tin zamansu a gurin donshi yake fuskantarta shiyasa duk d’agowar da zatayi dai sun had’a ido, mik’ewa tayi tabar wajen tanufi sashinsu,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button