HAUSA NOVEL

BAKIN CIKIN KISHIYATA Complete Hausa Novel

Da wani mugun kallo MAMI fiddausi ta bita a zuciyarta tana fad’in

“Munafika taita wani simi_simi da dankwafar da kai irin na uwarta,” tsaki tayi sannan taci gaba dacin abincinta

Mik’ewa yayi shima faruoq d’in yana fad’in “bari inje in watsa ruwa in d’an huta don na gaji sosai,”

Tab’e Baki mamin tayi sannan ta rakashi da harara don ta fara zargin wani Abu da bazataso ya kasanceba har abada tsakaninshi da zahran dontasan ba wani k’oshi da yayi shida yace yanajin yunwa Amman baifi tsokali 4 yayiba ya tashi don kawai yaga zahran ta tashi,
Ajiyar zuciya tajavmai k’arfi tana gyad’a kai tare dayin kwafa…………………!

Mrs Bilyamin kaita
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️
BAK’IN CIKIN KISHIYATA
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️

Story and written
By
Fatima umar kas
(Mummyn mihal)

*بسم الله الرحمن الرحيم*

®????
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *…*????✍????
[ “`Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women“`]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

*_Z• W• F•????_*
Page 65_70

Faruoq ne kawai ya lura da ita shi abinma dariya ya bashi Amman sai ya danne abarshi suka nufi ciki shida iyayen nashi,
A parlour suka zauna dukkansu anan yake musu k’orafin rashin zuwansu tarbarshi, uncle Aminu ne yace,

“Wallahi wani meeting ne ya taso mana Na gaggawa kuma dole ana buk’atarmu agurin shiyasa, Amman inbanda haka me zai hana ni zuwa tarbar babana aisai da dadlili,”

Alhaji Abubakarne yace. “Kaidai Aminu zanga sanda zaka daina shageab’a yaronnan,kalli yadda yazo ya tasamu gaba yana tuhumarmu kaikuma ka wani biyemai har wani uzuri kake bashi,

Ka tashi kaje anjima inmun kimtsa ka samemu a d’akina muna da magana dakai,”

Ya fad’a yana duban faruq sannan ya tashi yai cikine d’akinshi, shima Alhaji aminu mikewa yayi sannan ya dafa kafadar faruoq da cewa,

” bari inshiga ciki babana ka samemu anjima a parlour n dadyn naka,

Da toh ya amsa sannan ya shige d’akinshi shima bayan fitar uncle Aminu,

Bayan sunje sallahr isha,i sun dawo kai tsaye suka wuce parlourn Alhaji Abubakar d’in, bayan zaman sune Alhaji Aminu ya gyara zama sannan ya kalli faruoq yace,

“To babana zaman nan dai nakane, da farko dai muna godewa Allah da ya baka ikon kammala jaratunka lafiya ka dawo garemu lfy, Abu Na gaba kuma shine Aure a yanzu aurene ya dace dakai don haka munason sanin yarinyar daka tsayar amatsayin wacce zakuyi rayuwa tare,”
Dan sararawa yayi da maganar yana jiran yaji abinda faruoq d’in zaice

Shi kuwa faruoq wani irin sanyin dad’ine ke ratsashi najin damarshice yanzu ya fad’i abinda ke ranshi don haka ya gyara zama sannan yace,

“Eh uncle Akwai yarinyar danakeso harmun daidaita da ita,”

Murmushi uncle d’in nashi yayi sannan yace “to hakan yayi kyau yanzu saika sanar damu inda yarinyar take sai muje ayi komai don bamason abin ya d’au lokacin,”

Sosa kanshi yayi sannan ya daure yace “Ammm! Ummmm! Daman anan gidan take kuma tin inacan muka daidaita da ita,”

Shiru yai ya k’asa k’arasawa saida uncle d’in yace uhmm muna jinka wacece anan d’in?

Kasa d’ago kanshi yayi da kyar ya fuzgo maganar yace “uhmm wannance Zahra ta wajenka,”

Yana fad’a ya tashi da sauri ya fice daga d’akin don wani irin nauyin uncle din yaji ayau duk yadda ya tsara zai tunkaresu da maganar sai gashi su sukayimai Amman amsawa Na Neman gagararshi don ba karamin dauriya yayiba wajen cewa Zahra yakeso, Amman wani b’arin Na zuciyarshi dad’i yakeji,

Su kuwa bayan fitarshi kallon juna sukai suna farin cikin yanda abinya kasance kamar yadda suka tsara,

Alhaji aminu ne yace” yaya kaga ikon Allah ko? Ashema sun Dade sunason juna harmuke shirin had’asu aure, tosaimu godewa Allah da hakan ya kasance bari ina zuwa,”

Tashi yayi ya fita ba jimawa ya dawo ,kud’i ya dire a gaban ya yan nashi yana fad’in, ” ga wannan yaya ina nemawa d’ana Auren ‘yarka ga wannan amatsayin sadaki,”

Shima cike da farin ciki ya d’au kudin yana fad’in “ah da wuri haka? To Abu yayi kyau indai zahrace anbaku yanzu saura d’aura aure kawai ya rage,

Yanzu gobe ya dace mu had’a family meeting mu sanarda iyayen nasu mata wannan abin farin cikin,”
“Hakan yayi Allah ya kaimu,”

Uncle d’in ya fad’a sannan yamai sallama ya fita ya nufi bangarensu,
Bayan ya koma ya danarda momy husna akwai meeting gobe, Allah ya kaimu tace, yace ta danarda Fatima
Shima Alhaji Abubakar ya ssnarda MAMI Fiddausi zaman da za ayi da safe yace ta sanarda yaran, tasojin akan abinda zaca zauna Amman yace ta bari dai goben ta ji,

Washe gari

Dukkan Ahlin gidan sun hallara a babban parlour n gidan kowa so yake yaji akan abinda za a yi magana,
Alhaji Abubakarne ya bud’e taro da addua sannan ya d’ora da yi musu bayanin dalilin zaman akan faruoq da Zahra yace daman sunyi niyyar had’a auren sai kuma gashi da suka tuntub’i faruoq din yace daman sunason juna don haka yanzu sadakin Fatima yana hannunshi saura tsayar da ranar d’aurin aure,”

Parlor n gaba d’aya ya kaure da hayaniya kowa ka kalli fuskarshi cike take da farin ciki Na kadancewar hakan mudamman momy husna inbanda murmushin jin dad’i ba abinda takeyi don sosai tai murna ta faruwar hakan,

Wata gigitacciyar tsaea mai cike da hargowa da MAMI fiddausi ta dakane ya sanya kowa Shiva taitayinshi gaba d’aya suka zuba mata ido ganin babu alamar Annuri a fuskarta saima rikici da tashin hankali da suke hangowa a fuskar tata, cikin tsananin b’acin rai da basu tab’a ganinta dashiba ta fara magana jikinta har rawa yakeyi……………….!

????????????????????????????????????????
Ina mik’o gaisuwa da jinjinar girma gareku fan’s na wannan littafin????????

Inayinku kamar yadda kuke yina????????????

Masuyimin sharhi akan littafin inajin dad’in sharhinku musamman????????

Aisha Ibrahim
Ummu thurab
Ummu maryam
Ummu unaisat
Babynah
Maman prince
Maman Nana
Maimuna sweaty
…………………..

Da dai sauran da ban ambatoba da fatan zaku cigaba da zubo sharhi ni kuma incigaba dayi muku typing akai akai.????????❤️
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️
BAK’IN CIKIN KISHIYATA
????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️????????‍♀️
????????‍♀️

Story and written
By
Fatima umar kas
(Mummyn mihal)

*بسم الله الرحمن الرحيم*

®????
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *…*????✍????
[ “`Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women“`]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

*_Z• W• F•????_*
Page 70_75

“Ya isheku! Nace ya isheku haka! wannan maganar mai kama da k’anzon kurege ko shirin wasan kwaikwayo ita kuka d’auka gaske harkuke murna akanta? Yanzu menene abin farin ciki akan wannan ha d’in? To duk wani mai murna yai gaggawar maida murnarshi ciki don ko bayan raina ba zan tab’a son wannan had’inba, don baza ayiwa yarona auren doleba daga dawowarshi jiya jiya Amman har za a mak’alamai aure? Kuma a rasa da wacce za a had’ashi sai wannan k’arma shashshiyar yarinyar data kwaso bak’in hali irin na uwarta? Tana zaune ta rasa mai aurenta shine za a lik’a mai daga dawowarshi to ainice nai wahalar nakudar faruq ba watace ko wani sukayimin wahalashib………………!”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button